Asiri ya tonu!
Makarantar Sojin Amurka na kwas din kyamar Musulunci
Wannan kwas da aka dakatar da koyar da shi a Joint Forces Staff College Virginia, daya daga cikin manyan makarantun sojin kasar, na koyar da sojin cewa babu wani sassaucin ra’ayi a addinin Musulunci, saboda haka su dauka addinin makiyinsu ne. Jami’in da ke koyar da wannan kwas din, Laftanar-Kanar Matthew Dooley, an dakatar da shi daga koyarwa, amma kuma yana rike da aikinsa a Kwalejin da ke birnin Norfolk.
Ci Gaban Jawabin
Tweet
A ranar Litinin 8 ga Mayu, 2012 ne aka haifi wani jariri rike da dan karamin Kur’ani a hannunsa a wani coci mai suna White garment Church da ke Mushin, jihar Lagos a kudu maso yammacin Nijeriya.
Ci Gaban Labarin
Tweet
“To, ya za a yi ka san darajar Sayyida Zahra (SA) in ba ka san bala’o’in da aka fuskanto mata da shi ba da yadda ta daure? Ita ce mai cewa an zubo min da bala’i wanda yake da yinnai aka sa ma wadannan bala’o’in da sun zama darare.” - Sayyid Zakzaky
Ci Gaban Labarin
Tweet
Janar Buhari
Tsohon Shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari (murabus) ya ce, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ce babbar ’yar Boko-Haram. Ya fadi hakan ne a Kaduna, lokacin da yake jawabi ga wata tawagar wakilan jam’iyyarsa ta CPC daga jihar Neja, lokacin da suka ziyarce shi.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Ya kusa kawo tarzoma
Kisan gilla da aka yi wa wani matashi da ake kira Abdullahi Nura (Fahad Baba) a Unguwar Kaura cikin birnin Zariya, ya kusa jawo wata mummunar tarzoma a garin.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Da sanyin safiyar ranar Juma’ar da ta gabata ne ’yan uwa na Da’irar Kano da kewaye suka shiga cikin wani yanayi na jimami da alhini na kisan wani fitaccen dan uwa, Alhaji Muhammad Ali da ke zaune a unguwar Gadon Kaya cikin birnin Kano.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Tambihi
DARASIN FIKHU 2Tare da Muhammad Suleiman 08029493717
Kamar yadda aka ambata a darasin da ya gabata cewa, wannan darasi na Fikhu insha Allah, za a dinga gabatar da shi a bisa Usulubi na Fikhul-Mukarana ne, wato mukarana tsakanin wadannan Mazhabobi guda hudu na Ahlus-sunnah; Hannafiyya, Malikiyyah, Shafi’iyya, Hanbaliyya. A daya gefen kuma da Ja’afariyya, amma za a karfafa a Fikhun Ja’afariyya ne.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Hannun ka Mai Sanda
Sun daura damarar yaki da Musulunci
Ko mutum ya yarda ko kada ya yarda, azzaluman duniya ba su da manyan abokan gaba fiye da Musulmi da Musulunci.
Ci Gaban Labarin
Tweet
