Daga Aliyu Saleh da Muhammad Isa Ahmad
Jama'a sun fusata matuka da matakin da kungiyar kwadago, NLC, ta kasa ta dauka na mika wuya ga tayin Naira 97 ga litar mai da gwamnatin Goodluck Jonathan ta bayar, inda ta bukaci kowa ya koma bakin aikinsa duk da kuwa a baya suna korarin cewa ba za su koma bakin aiki ba, matsawar an kara kudi a kan Naira 65.
Jama'a da dama a Kano, Kaduna da Legas sun bijire wa umurnin uwar kungiyar kwadago ta kasa da ta bukaci mutane su ci gaba da zama don yajin aiki a ranar Litinin, amma kar su fito zanga-zangar adawa da cire tallafin mai da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.
Jama'ar da suka fito a wadannan garuruwan sun yi Allah wadai da amincewa da karin da gwamnati ta yi wa litar mai daga Naira 65 zuwa 97 da kuma amincewa da haka da kungiyar kwadago ta yi. Sun yi zargin cewa an ba su kudi ne shi ya sa suka bayyana amincewarsu tare da umurtar mutane su koma bakin aikinsu.
A Kano da Wakilinmu ya ga mutane sun fito daga kowane sashi da bangare na cikin birnin, ciki har da tsofaffi da mata suna bayyana kin amincewarsu da wannan abin da suka bayyana da cin amanar al'umma.
Duk da jami'an tsaron da aka jibge a wuraren da masu zanga-zangar suka ratsa, amma wannan bai hana kungiyoyin NLC, ASUU, SUG, tare da wasu kungiyoyi fitowa dauke da kwalayen da aka yi masu rubuce-rubucen bayyana adawarsu ba. Cikin wadanda suka shiga zanga-zangar ta Kano har da wasu Malaman Jami'a da masu fafutika irin su Dakta Mahmud, Dakta A. M. Bichi, Dakta S.A. Dukawa.
A Legas ma duk an jibge jami'an tsaro a dandalin Gani Fawahemi, amma wannan bai hana mutane fitowa kan titi don bayyana adawarsu da wannan karin da aka yi wa albarkatun mai ba. Da yawansu sun yi zargin cewa akwai hadin baki tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago, wanda suke ganin kamar ta sarayar da hakkinsu ne.
A baya dai gwamnatin Jonathan ta cije a kan cewa ba za ta rage ko taro ba a kan Naira 141 da ta sanar tun farko, yayin da ita kungiyar kwadago ta tsaya kai da fata a kan cewa ba za ta yarda a kara ko anini a kan Naira 65 ba. Sai dai kuma bayan tattaunawa da bangarorin biyu suka yi sun cimma matsaya a kan sabon farashin na Naira 97, wanda wasu suke cewa ba ta sake zani ba.
