Jami’an leken asiri na Mossad ne suka kashe masanin nukiliyar Iran
Cewar jaridar Sunday Times
Wata jaridar London da ake kira SUNDAY TIMES ta bayyana cewa jami’an Hukumar leken asiri na Haramtacciyar Isra’ila, MOSSAD ce ke da alhakin kisan dauki dai-dai da aka yi wa wani masanin fasahar nukiliyar Iran a makon jiya.
Sunday Times ta ruwaito a ranar Litinin na makon nan cewa kisan da aka yi wa Mostafa Ahmadi Roshan ya yi kama da irin kisan da akan yi a ‘fima-fiman ayyukan leken asiri’, wanda aka shirya shi na tsawon watanni, wanda cike yake da ayyukan tara bayanan sirri.
Jaridar mai fitowa kullum ta ambato wata majiyar sirri ta Isra’ila da ke ikirarin cewa kisan wani mataki ne na ishara, amma ba makwafin kai wa Iran din harin soji ba, wanda manufar hakan shi ne mai da sake gina tashoshin nukiliyar Iran din mawuyacin abu madamar aka kai musu hari.
Kamar yadda rahoton ya nuna, wasu ejen-ejen na Mossad suna lura da wasu muhimman wurare a Tehran, wadanda suke ganin suna da muhimmanci a kisan Roshan.
“Ba a yarda da kuskure komai kankantarsa. Alal hakika kasa aiwatar da shirin ba kawai zai yi sanadin wuyan ejen-ejen din ba ne, har ma yana iya zama wani abin tonon silili na kasa da kasa,” a cewar majiyar sirrin ta Isra’ila.
Rahoton na Sunday Times ya ce, an rika lura da Ahmadi Roshan ne ta wani dakin leke-leke daga wani gida da ke kusa, yayin da shi kuma ke shirin tafiya bakin aiki.
Kuma ko da mai bai wa Ahmadi Roshan tsaro yake tuko shi za su masarrafar nukiliyar Iran da ke Natanz, inda yake aiki a matsayin Mataimakin Manajan kasuwanci, sai aka ga wani dan mashin da ke rufe da kansa ya matso motar a cikin jerin motoci da ke kan titi, ya manna wa motar wani bom wanda aka shirya shi musamman don ya fashe kan fasinjan da ke cikinta.
Da faruwar abin, Amurka ta yi gaggawa ta ce ba hannunta a ciki ta hannun Sakataren tsaronta Leon Panetta.
Ofishin Birtaniya ma ya ce kasarsa “ba ta da hannu ko kadan” a cikin kai harin.
A fili yake cewa a watan Nuwamban 2011, wasu masu neman takarar shugabancin Amurka sun rika yin kiran a aiwatar da kisan dauki dai-dai kan masanan nukiliyar Iran da ma kai wa Iran din harin soji da kuma yi wa ayyukanta na nukiliyan zagon kasa.
Da alamu kuma wadannan kiraye-kiraye ba na kawai ba ne don kuwa ya zuwa yanzu an kashe masanan nukiliyar Iran da dama.
Masu sharhi kuma na zargin Hukumar hana yaduwar makamashin nukiliyar Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, da mika sunayen masanan nukiliyar Iran ga jami’an leken asirin Amurka da Isra’ila don kuwa shi wanda aka kashen, sunansa na cikin jerin sunayen masanan da ke hannun Hukumar IAEA.
Iran ta danganta kisan gillar da ake yi wa masananta kan harkokin nukiliya da bayanan da ta bai wa Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) kan shirinta.
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ramin Mehman Parast ne ya bayyana hakan, inda ya ce dukkanin masanan da aka yi wa kisan gilla suna daga cikin wadanda Iran ta bayar da sunayensu ga Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wanda kuma an yi hakan ne bisa yarjejeniya tsakanin Iran da kuma Hukumar, kamar yadda ka’idoji na kasa da kasa suka shata, amma abin mamaki ne yadda ake bin wadannan masana daya bayan daya ana yi musu kisan gilla. Ya ce hakan ya sanya Iran yin shakku kan amincin Hukumar kula da makashin nukiliya ta duniya.
Mista Ramin Mehman Parast, wanda ke zantawa da gidan talabijin din AL-ALAM dangane da kisan gillar da aka yi wa masani kan harkokin nukiliyar Iran, Dakta Mustafa Ahmadi Roshan, ya ce ko shakka babu haramtacciyar kasar Isra'ila da Amurka suna da hannu kai tsaye wajen aiwatar da wannan kisan gilla. Ya ce, hakan babu abin da zai kara wa masana Iran face azama kan abin da suka sanya a gaba domin ci gaban kasarsu da al'ummarsu.
A nasa bangaren, masani kan harkokin siyasa a kasar Amurka, John Parker, ya fadi a wata zantawa da ta hada shi da gidan talabijin PRESSTV cewa, yin kisan gilla kan masana harkokin nukiliya kasar Iran, na daga cikin abubuwan da Hukumar leken asiri ta Amurka CIA, da kuma kungiyar liken asiri ta HKI suka mayar da hankali kansu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kaddamar da irin wannan hari na ta'addanci kan masana Iraniyawa ba, da nufin kawo cikas ga shirin na makamashin nukiliya da take gudanarwa domin amfanin farar hula. A kwanakin baya ne aka kame wasu da suke da hannu a irin wadannan ayyuka, kuma sun tabbatar da cewa Amurka da HKI ne suka sanya su.
A nasa bangaren Jagoran juyin-juya-halin Musulunci na Iran, shi ma ya bayyana cewa; Hukumar CIA da kungiyar Mossad suna da hannu a kisan gillar da ake yi wa Roshan.
A sakon ta'aziyyar da ya aike ga iyalan Mustafa Ahmadi Roshan, Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa; “Kisan gilla irin ta ragwaye da Hukumar leken asirin kasar Amurka ta CIA da kungiyar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila ta Mossad ke yi kan masana ilimin kimiyyar kasar Iran dalili ne da ke tabbatar da cewa; manyan kasashe masu girman kai a duniya sun zo karshe a fito-na-fiton da suke yi da kasar Iran”.
Har ila yau Jagoran ya jaddada cewa; “Mutanen da suka aiwatar da kisan gilla kan Mustafa Ahmadi Roshan za su fuskanci hukunci kan mummunan aikin da suka gudanar”.
Shi kuwa Limamin Juma'a na birnin Tehran, cewa ya yi kisan da makiya ke yi wa Malaman kimiyya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa.
A lokacin da yake gabatar da hudubar Sallar Juma'a a masallacin Jami'ar Tehran, Ayatullahi Muhammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa Malamin kimiyyar nukiliya na kasar Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro-da-kai a fannoni na bincike da kuma kimiyya.
Har ila yau Limamin ya ce, wasu daga cikin dalilan matsa kaimi da kasashen Yamma, musamman ma Amurka ke yi a kan Iran, sun hada da yadda al'ummomin kasashen wannan yanki suka juya mata baya, saboda haka suke zargin Iran da hannu a shirya irin wannan bore da ke gudana. To, sai dai Ayatullah Imami-Kashani ya ce shirun da kasashen duniya suka yi dangane da wannan ta'addanci da ake aikatawa a kan Iran, wata alama ce da ke nuni da irin goyon bayan da masu wannan shiru ke bai wa ayyukan ta'addanci a duniya.
A mayar da martanin farko da ta yi kan wannan lamari, gwamnatin kasar Amurka ta nisantar da kanta daga wannan ta'asa, amma a nata bangaren Isra'ila ba ta kore ko tabbatar da cewa tana da hannu a cikin wannan aika-aika ba, amma a ta bakin Kakakin rundunar sojinta Birgediya-Janar Mowaf Mordkhei, ya bayyana cewa ko ma da wane ne ya kashe masanin nukiliyar Iran, hakan aiki ne na daukar fansa.
A cikin wannan makon ne babban Hafsan-Hafsoshin sojin Isra'ila, Bani Ganitez, ya fadi a gaban Majalisar Keneset cewa, shekara ta 2012 za ta zo wa Iran da abubuwa na ban mamaki dangane da shirinta na nukiliya da ba ta saba gani ba.
Yayin da shi kuwa masanin harkokin tsaro na kasar Amurka, Mark Peters Patrick, ya yi amannar cewa, yadda aka shirya kashe masanin nukiliyar, da kuma yadda aka aiwatar da kisan, wata manuniya ce kan yadda wasu kungiyoyin leken asiri na kasashen ketare suke da hannu kai tsaye a cikin lamarin.
A cikin shekara ta 2011 da ta gabata, wasu daga cikin 'yan Majalisar Dattijan kasar Amurka, sun bukaci gwamnatin kasar da ta dauki wasu matakai na yin kisan gilla kan masana harkokin nukiliya na kasar Iran, da nufin gurgunta shirin nata ta wata hanya ta daban, domin kuwa a ganinsu, matakan barazana ko kakaba takunkumi kan Iran bai tasiri wajen dakatar da shirin nata ba.
Wadannan da ma wasu daga cikin dalilan na daban na daga cikin abubuwan da Iran ta dogara da su wajen nuna yatsan tuhuma kan kungiyar leken asiri ta Isra'ila, Mossad, tare da hadin gwiwa da Hukumar leken asiri ta kasar Amurka CIA, dangane da kisan gillar da aka yi wa masanin harkokin nukiliyan na kasar Iran din a ranar Larabar da ta gabata.
