Sojan Amurka sun shirya wa rugujewar Nijeriya
In ji wata mujalla a Amurka
Akwai kwararan alamu da ke nuna cewa Amerika tana shirye-shirye tarbar yiwuwar wargajewar kasar nan daga abubuwan da suke faruwa tun a ’yan shekarun nan.
Wadannan alamu sun fito ne a wani bayani da wata mujalla da ake kira NEWSRESCUE a Amerika ta wallafa a shafinta na intanet www.newsrescue.com , inda aka yi bayanin wata makala da Daraktan AllAfrica Global Media, Mista Daniel Volman, ya gabatar a taron kara wa juna sani da AFRICOM ta shirya a Fort McNair na Amurka.
In za a iya tunawa a 2005, Amerika ta yi hasashen cewa Nijeriya za ta gushe daga zama hadaddiyar kasa a 2015 in aka yi la’akari da irin barazanar da rigingimun addini da na kabilanci ke yi wa kasar na tsawon shekaru.
Haka nan kuma a Mayun 2008, sojin Amerika sun yi wata rawar daji da suka kira Unified Quest 2008, don gwada yadda za su mai da martani da sojojinsu in yakI ya barke a wasu sassan Afrika, ciki har da ambatar Nijeriya.
Har kuma aka duba yiwuwar Amerika ta iya tura sojoji 20,000 in Nijeriya ta wargaje zuwa sassa daban-daban, don su kwace yankin Kudu da ke da albarkatun man fetur, a yayin da kuma Arewa za a mai da ta wani yanki da ke da karkata ga kasashen Laraba ko wani sansani na wadanda Amerika ke kira ’yan ta’adda.
Abubuwan da yanzu suke faruwa a siyasar kasar na rigingimun da suka biyo bayan zabe, ayyukan tsegerun Neja-Delta da kuma ayyukan wadanda ake kira Boko-Haram, suna kara tabbatar da wannan hasashe.
Da ma dai Amerika an shaide ta da kasancewa a bayan wargajewar wasu kasashen duniya kamar su Biyatnam, da Koriya. Kuma ko da suka rabe, sai Amerika ta jibge sojojinta a kan iyakokin bangarorin da take marawa baya. Haka nan kuma a kasafin kudin 2010, Amerika ta ware wasu makudan kudi don ayyukan wata Hukumar soji da ta kafa mai suna AFRICOM a takaice, wadda aka shirya za ta ba da taimakon tsaro ga wasu gwamnatocin kasashen Afrika, ciki har da Nijeriya.
Don fuskantar wannan kule, Shugaban National Action Coalition for Democratic Forces, Dk. Tunji Braithwaite ya yi tir da shirin da gwamnatin Tarayya take yi na gayyato Amerika ta taimaka mata don kawo karshen ayyukan wadanda ake kira Boko-Haram.
Yayin da yake magana a ranar Talatar da ta gabata a Lagos, ya bayyana shirin da cewa ya yi kama da ‘kyautar Girkawa’, wadda bai kamata Nijeriya ta amsa ba. Sa’ilin da yake tsakiyar manyan membobin kungiyar, Braithwaite ya yi zargin cewa Amerika dai na son man fetur din Nijeriya ne, yana mai kara wa da cewa matsalar Boko-Haram matsala ce da za a iya magance ta ta cikin gida.
