Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Tashin bama-bamai a Kano

An ga wasu cikin kayan jamian tsaro suna kisa

Daga Muhammad Isa Ahmad

Alummar Kano, cibiyar kasuwanci da ke arewacin Nijeriya daga yammacin ranar Jumaa 27 ga Safar 1433 (20/1/2012) an kwana cikin zullumi da firgici sakamakon karar fashewar wasu abubuwa da ake ji tare da ganin turnukewar bakin hayaki da ake iya hangowa daga nesa, da kuma wuta da ke tashi tana kona wasu sassa na wuraren da wannan abin fashewa ya tashi.

Alummar Kano sai cewa suke abin da ake gani a fim ko ake jin labaran sa a wasu wurare, yau ga shi an kawo mana shi garinmu. Menene ya faru? Da misalin karfe 5:00ny ranar Jumaa ne aka ji kara daga hedikwatar yan sanda, zone 1 da ke hanyar zuwa BUK old site, da an wuce kofar Naisa kafin a je kofar Gadon Kaya, kuma yake kusa da NNDC kwatas.

Bayan wannan karan da aka ji a wannan guri, awa biyu bayan wannan an dinga jin wadansu kararrakin fashewar abubuwa da ke da kara sosai, kuma ana iya jin girgiza daga akalla kilomita daya daga wajen wannan fashewar tare da jin aman karar bindigogi na musayar harbe-harbe a gurare daban-daban na cikin kwaryar Kano.

An samu tabbacin inda wannan hatsari ya auku ranar Jumaa da ya hada da hedikwatar yan sanda zone 1, Immigration office, ofishin yan sanda da ke Farm Centre, Yar Akwa Police Station da ke Unguwa Uku, New Road da ke Sabon Gari, Police hedikwata da ke Bompai da kuma ofishin jamian tsaron farin kaya wato SSS da ke Sardauna Crescent na Nasarawa GRA.

Alummar da ke kusa da inda wannan hatsari ya auku sun firgita sosai, inda suka fara guje-guje domin tsirar da rai, kuma nan da nan hanyoyi suka cika da ababen hawa da ke nufan isa gidajensu don ceton rai. Guraren da wannan hargitsi bai auku ba kuwa, jamaa sun ci gaba da tafiyar da alamuransu, sai dai su ji me ke faruwa ne a kafafen yada labarai.

Shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa da misalin 5:00ny wani a cikin mota yana u-turn ya kwaso motarsa a guje da karfin tsiya duk da jamian yan sanda sun yi kokarin hana shi, amma ya kutsa ya shiga ya tayar da bom din da ke cikin motar, ya tarwatsa motarsa, wanda ya sabbaba lallata sassan gini biyu da ke daura da inda motar ta tawatse, tare da lalata wasu motocin da ke wajen.

Wannan ta da bom din ya sabbaba kisan yan sanda biyu nan take tare da raunata mutane da dama. Wakilinmu ya ji wani na fadin cewa yana gida ya ji benen da yake ciki a unguwar Sabon Titi (kimanin kilomita uku daga wajen) ya girgiza, wanda daga baya ya ji ana cewa bom ne ya tashi a hedikwatar yan sanda na hanyar BUK.

A sauran sassan da wannan matsalar ta auku, shedu sun ambata harbe-harbe tare da tayar da abin fashewa, wanda wasu da ba a san ko su waye ba suka sabbaba, wanda ya sanya rasa rayuka da dama tare da jikkata mutane da dama ko barnata dukiya.

A hedikwatar yan sanda da ke Bompai ne kisa da raunata alumman da ba su ji ba su gani ba ya fi kazanta, inda wasu shedu da aka zanta da su ta kafafen yada labarai ke ambata cewa wasu da ba a san ko su waye ba cikin kayan jamian tsaro suka dinga antaya harbe-harbe ga duk wanda yake wajen ko ya zo gitta da ya sabbaba mutuwa da jikkatar mutane masu yawa.

Adadin da Hukuma ta bayar a ranar Litinin 23/1/2012 na wadanda ake da tabbaci kuma rahoto ya zo masu sun rasa rayuka sun kai mutum 184, wanda ya kunshi jamian yan sanda 29, jamian Immigration 2, jamian SSS 3, da akalla fararen hula 150, yayin da wasu ke ambata cewa lallai adadin wadanda suka rasu za su haura mutum 300, wannan banda wadanda suka raunata.

Shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan ya ziyarci garin Kano ranar Lahadi, inda aka zaga da shi asibitoci da kuma wasu wuraren da ya faru. Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso suna cikin wadanda suka nuna alhinusu da abin da ya faru.

Gwamnatin Jihar ta sanya dokar hana fita na awa 24 ranar Jumaa domin kare rayuka da samar da yanayin da zai samar da kwanciyar hankali, wanda aka sassauta zuwa 6:00ns zuwa 7:00nd a ranar Asabar da ta gabata, tare da daukar takalifin kula da ba da magunguna ga wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Lokacin da aka sassauta dokar ta-bacin zuwa 6:00ns-7:00nd, an ga alumma na ta kai-kawo tare da bude cibiyoyin kasuwanci, amma ana dar-dar, tare da samar da matakan tsaro da sojoji ke lura da su a gurare daban-daban a cikin garin.

An ga wasu motoci fiye da bakwai wadanda ke kunshe na nakiyoyi a ranar Lahadi a Eastern by-pass da ya hada daga Yan Lemo, Hotoro da titin Yan Kaba, wanda hakan ya kara sanya alummar gari cikin firgici da dar-dar. Sake kai wani harin da aka yi a Sheka a ranar Talata, tare da kone ofishin yan sanda da ke wajen, gami da musayar wutar da aka yi ya kara jefa mutane cikin firgici.

Muhawarar da ta game garin Kano bayan harin; menene ya sabbaba wannan harbe-harben da ta da abin fashewa a ofisosin jamian tsaro? Shin sanya alumma a cikin firgici da kashe rayuka zai zama yana da faida? Wane matakai ne alumma da gwamnati ya kamata su dauka domin magance irin wadannan matsalolin?

Kafafen watsa labarai sun bayyana cewa kungiyar Ahlul Sunna Lid Daawati Wal Jihadi da aka fi sani da Boko-Haram ta bakin Kakakinta Abu Kaka, ta dauki alhakin kai wadannan hare-haren sakamakon abin da ya bayyana da cewa kame mutanensu da aka yi a garin na Kano.

Wakilinmu ya ji tattaunawa daga daidaikun mutane da kuma masu majalisi daban-daban, inda suke sanya ayar tambaya ga makasudin abin da ya auku. Wasu cewa suke kokarin bata sunan Musulunci da Musulmi ne da kafircin duniya ke yi, don a nuna shi a matsayin addinin taaddanci da tashin hankali. Yayin da wasu suke cewa ko dai harin daukar fansa ne da kungiyar CAN ta sha alwashin yi? Yayin da wasu suka ce ana dai neman tabbatar da hasashen da aka yi ne na wargajewar kasar nan nan 2015. Wasu kuma suka ce an yi haka ne don a kawar da hankalin mutane daga batun cire tallafin mai da gwamnatin ta yi.

Wannan harin da aka kai ya hana gamayyar kungiyoyin kwadago gudanar da zanga-zangar da suka shirya gudanarwa ranar Asabar din da ta gabata, don nuna bijirewa daga janye yajin aiki da NLC ta yi, har sai an mai da farashi zuwa Naira 65 ga lita.

Malam Turi ya kai ziyarar jaje

Da yammacin ranar Litinin ne, Malam Muhammad Mahmoud Turi, Wakilin Sayyid Ibraheem Zakzaky a Kano ya kai ziyarar jaje ga wadanda suka ji raunuka, rasa rayuka, ko dukiya a sakamakon tashin hankali na fashewar bama-bamai da kuma harbe-harbe a garin Kano ranar Jumaa 20 ga Janairu 2012.

Daga cikin wuraren da Malamin ya ziyarta kuma ya tarar da mazauna wurin shi ne cibiyar sai da wayoyi da ke Farm Centre daf da ofishin Immigration na Kano, wanda yana daya daga cikin wuraran da bama-bamai da harbe-harbe ya auku.

Alh. Ishaq Abdullahi, shi ne Shugaban masu sai da wayoyin na Farm Centre, shi ya tarbi tawagar Malam Turi, yana mai nuna masa taadin da ya wakana sakamakon firgici da harbe-harbe da ya wakana a ranar har wasu masu sayaya da kuma yan kasuwar suka rasa ransu, kuma barayi suka yi amfani da ranar wajen sace-sace, inda suka rasa dimbin dukiya.

Malamin ya isar da jajen Sayyid Ibraheem Zakzaky da almajiransa tare da adduar Allah ya mai da mafi alherin abubuwan da aka rasa.

Malamin ya so zuwa sauran sassa da wannan taasa ya auku domin jajantawa, amma yanayin guraren bai ba da damar yiwuwar hakan ba.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan