Wasu Kiristoci sun shiga hannu
Bisa zargin watsa sakonnin Jihad
Daga Abdullahi Usman
Jamian tsaro farin kaya, wadanda aka fi sani da SSS, sun gabatar da wasu yan siyasa a gaban kotun Majistare da ke Yola bisa zargin watsa sakonni ta wayar salula don neman ta da ricikin addini a jihar ta Adamawa.
Mutanen biyu dai sun hada da Mista Edward Ogundani da kuma Mista Charles Tomlava, suna watsa wadannan sakonni ne da sunan cewa alummar musulmin jihar na shirin yin Jihadi kan wadanda ba musulmi ba a duk fadin jihar.
Ogundani dai shi ne mai magana da yawun dan takarar Gwamnan jihar na jamiyyar CAN, kuma shi ne hukumar ta zarga da cewa yana daya daga cikin yan wannan kungiya da ke yada wannan sako. Sannan kuma sauran mutane hudun da aka yi imanin cewa sune ke yada wadannan sakonni, ana nan ana ci gaba da bincikarsu.
Jihar Adamawa dai ta fuskanci matsalar rashin tabbas a yan kwanakin da suka gabata, inda har ta kai ga an sanya dokar hana fita a fadin jihar.
Wadannan mutane dai hukumar na zargin su ne da yada wannan sako don ci gaba da tayar da hankalin jamaa a daidai lokacin da zaben Gwamna da za a yi a jihar ke kara matsowa, wanda za a yi a farkon watan Fabrairu nan mai zuwa.
Jamii mai gabatar da kara, ya shaida wa kotun cewa wadannan mutane lokacin da suke watsa wannan sako sun yi ikirarin cewa wani ne da har yanzu ba a san ko wanene ba, mai suna Shaikh A.Y. Muhammad ya rubuta. Ya ce wannan abu da suka yi tayar da hankalin alummar jihar.
Don haka mai sharia Susan Ellam ta umurci da a tsare wadanda ake tuhumar a gidan yari, sannan ta dage wannan sharia zuwa 2 ga watan Fabrairun mai zuwa.
Kwanan nan dai hukumar ta SSS ta fitar da sunayen wasu yan siyasa a jihar, da ta ce suna cikin bakin littafinta. Ta ce yin hakan ya zama wajibi a gare ta saboda jamiyyun wadannan yan siyasa su gargade su.
Duk da cewa jamian SSS din sun ki bai wa manema labarai wannan littafi, Daraktan hukumar, Mista Alfred Olusegun Ajayi, ya ce yin hakan ya zama wajibi saboda bakin halin wasu daga cikin yan siyasar jihar.
Ya ci gaba da cewa wasu yan siyasar da jamiyyunsu suna yin siyasarsu bisa tsafta da bin doka da oda, amma wasu ba abin da suka sa a gaba sai bakin hali.
