Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Sakon Shaikh Jingir ga Jonathan


Ka fito da ’yan Boko-Haram da ke cikin gwamnatinka

Daga M. Umar Saye a Bauchi

Kungiyar Izalatul Bid’ah Wa ‘iklamatis Sunnah ta kasa, ta bukaci Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana sunayen ’yan Boko-Haram din da suke tare da shi a cikin gwamnatinsa suke zama teburi guda suke cin abinci suke shan shayi tare.

Shugaban Majalisar Malamai na kasa, Shaikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya yi wannan kira cikin jawabinsa a wajen wa’azi da kaddamar da gidauniyar ilimi da sayen motocin aiki da suka gudana ranakun Asaba da Lahadi a garin Bauci.

Shaikh Jingir, ya bayyana cewa Shugaban ya bar Musulmi cikin wani yanayi na kokwanto da tsarguwa da sukan lamurra da dama, don haka ya ce, amma idan ya fito fili ya bayyana wadannan mutane a cikin soji ko Majalisa ko ’yan sanda da sauransu sai a samu natsuwa, saboda a kullum Musulmi suna da bukatar ganin ya fito fili ya bayyana wadannan mutane da suke hidimar Boko-Haram a cikin gwamnatinsa, kuma ya fito fili ya ce sukan zauna teburi guda suna ci da sha tare da su.

Shi ma cikin jawabinsa, Shugaban kungiyar Izala na kasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci Sarakuna su yi namijin kokari wajen fita su fada wa shugabanni kura-kuransu idan sun kauce hanya, tare kuma da jan hankalin mutane wajen ganin sun ci gaba da addu’o’in fatan alheri ga kasar nan, tare da rokon Allah ya tona asirin dukkan wadanda ke da hannu cikin kashen- kashen mutane da ake aiwatarwa a kasar nan don a samu ingantaccen tsaro.

Shaikh Lau ya bukaci dukkan Musulmi su tashi tsaye wajen yin addu’o’i a masallatai tare da kunuti don Allah ya kawo karshen wannan fitina da ke aukuwa a kasar nan, musamman Jihohin Arewa.

Yayin gidauniyar an tara Naira miliyan 83 da 618. Gwamnonin Bauchi da Zamfara da Yobe sune suka bayar da gudummawa mafi tsoka ta Naira milyan 10-10, sai Jihohin Nassarawa da Taraba da Gombe masu Naira milyan biyar-biyar.

A wani labarin kuma, an samu tashin bama-bamai uku da suka auku a daren wannan Lahadin a wasu sassa na garin Bauci, an sake samun kai mummunan hari a kan jami’an tsaro da suke aiki a shingen duba abubuwan hawa da ke mararrabar Liman Katagum, inda aka kashe soja daya, da kuma cikin garin Tafawa Balewa da aka kashe DPO da wani soja mai mukamin las-kofur, da kuma mutane 8 farar hula, cikin wata fafatawa da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi, Ikechukwu Ayo Aduba, shi ne ya bayyana wa manema labarai tare da hadin gwiwar sojoji da jami’an tsaron ciki, wato SSS a harabar rundunar ’yan sanda ta Bauchi. Inda ya kara da cewa a karon farko cikin dare wayewar Lahdi wasu fashewa uku sun auku a unguwar kofar Dumi da kuma titin Sultan Abubakar da ke Fadamar Mada, inda aka rusa garun wasu majami’u biyu, amma ba rasuwa ko rauni kuma ba wanda aka kama.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan