Bin tafarkin Shehu Danfodiyo ne zai warware matsalolin kasar nan
-Sayyid Zakzaky a Abuja
Daga Aliyu Saleh, MSU Abuja da rahoto daga www.harkarmusulunci.org A ranar Asabar 27 ga watan Safar, (21/1/2011) ne yan uwa na Resource Forum da ke Abuja suka shirya tare da gabatar da wani gagarumin taron tunawa da haihuwar Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo (RA) karo na hudu a babban dakin taro na masallacin kasa da ke Abuja.
A lokacin taron na bana, kamar na bara, Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky ne ya gabatar da jawabi ga daruruwan jamaar da suka yi dafifi maza da mata, inda bayan ya lissafo wasu daga cikin matsalolin da suka yi wa kasar nan dabaibayi, sai ya tabbatar da cewa komawa kan tafarkin Shehun Usman Danfodiyo ne kawai maganin matsalolin.
Shi dai taron, an fara shi da misalin karfe 10:30ns, inda mawakan Harkar Musulunci suka rika gabatar da wakokin yabon Manzon Allah (S) da kuma wanda suka yi wa Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo (RA).
Bayan isowar Sayyid Zakzaky sai ya fara gabatar da jawabinsa. Tun da farko ya fara ne da neman uzurin mahalarta saboda kuncin zauren taron da jinkirin da aka samu na isowar sa daga Zariya, wanda yanayin da gwamnatin kasar nan mai tsananin farin cikin tsiya ta jefa jamaa ya jawo; Saboda yanayin tsare mutane da ake yi da kuma yanayin yadda hanya take, ya kamata a ce awa biyu ta ishe mu, amma sai da muka yi kusan awa hudu.
Sayyid Zakzaky ya ce; Za mu iya cewa wannan taro namu na murna ne, na murnar haihuwar Shehu Danfodiyo (RA). Bisa yadda aka fada a tarihi an ce an haife shi a karshen Safar ne, amma ba a fadi takamaimen rana a Safar din ba, amma dai a karshen Safar din ne aka haife shi.
Sannan sai ya shiga magana kan munasabar ta tunawa da ranar haihuwar Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo (RA), inda ya kawo gajeren bayani kan wanene Shehu? Ina aka haife shi? Da kuma ranar da aka haife shi. Inda ya bayyana cewa shi Mujaddadi Shehu Usman an haife shi ne a karshen watan Safar a wani gari da ake kira Marata, wanda yake a cikin jamhuriyar Nijer a yanzu, daga nan kuma suka koma Dagel. Kuma a nan ya yi yarintarsa, har zuwa lokacin da ya fara ba da karatu, bayan ya je wajen wasu Malamai ya yi karatu a wurare daban-daban da suka hada da Tumbuktu, da Malamai da dama ciki har da Malam Jibrila da ke garin Agadas da Malam Hamid da ke Zariya.
Sannan ne sai Malam ya shiga bayani kan yanayin da Shehu ya tarar a lokacinsa, yanayin kasar Hausa a wancan lokacin, yanayin yadda Sarakuna suka kasance, da irin fadin ikon su, yadda alumma suke kallon Sarki da yadda ikon Sarki ya salladu a kansu.
Haka nan kuma Malam ya yi bayani game da yadda miyagun Malamai suka kasance suna taimaka wa sarauta don cimma manufofinsu, da kuma yadda suka rika yin amfani da addini wajen bai wa wadannan manufofin nasu kariya.
Bayan daukar kimanin shekaru 100 kafuwar wannan daula ta Musulunci a wannan nahiya da ta hada daukacin arewacin kasar nan ta yau da jamhuriyar Nijar, Kamaru, Chadi da Mali da ma wasu yankuna na Afrika, sai ga Turawan Faransa da na Ingishi sun iso inda suka yaki Daular suka karkasa ta a tsakaninsu.
Turawan Faransa sun zo da salo na hadiye al'umma su zama tamkar irin su (Assimilation), yayin da shi kuwa Baturen Ingila ya zo da salon mulki mai wasida (Indirect Rule). Daga nan ne sai Malam ya kwatanta wancan lokacin na Shehu da kuma wannan lokaci da muke ciki, ya bayyana irin fuskokin da suka yi kama, sannan ya fitar da darussan da ya kamata mu dauka daga rayuwar Mujaddadi.
Malam ya bayyana cewa, mu a wannan kasa ba wani bako abu ne muke kiran al'umma zuwa gare shi ba face wannan addinin da Mujaddadi Shehu Usman (RA) ya jaddada, wanda kuma Turawan mulkin-mallaka suka zo suka kawar shi ne muke son mu sake dawo da shi a wannan lokacin namu.
Sayyid Zakzaky ya bayyana cewa Shehu ya tashi ya ga ana Musulunci, sai dai Musuluncin yana cike ne da wasu aladu da tsaface-tsaface, tare da mallake kasa da mazaunanta, inda Sarakuna sukan kwace komai na kasa da sunan kasa tasu ce, yayin da ko da mafarauci ne ya je farauta, to duk abin da ya farauto na Sarki ne, sai ya biya haraji, ko da gona ko fili ne mutum zai yi, sai ya biya Sarki, wani lokacin ma sukan kwace mata da yayan mutum saboda suna ganin komai da ke doron kasa mallakar Sarki ne.
Ya ce a wannan halin ne Shehu ya sami al'ummarsa duk da Malamai sun rufe idonsu daga wannan yanayi da sunan Musulunci ne suna mara wa Sarakuna baya saboda dan abin da suke samu, amma zuwan Shehu ya barranta da halayayyar Sarakunan tare da nusasshe da alumma cewa wannan hali da Sarakuna ke yi na mulkin danniya da kwace tare da dabi'ar tsaface-tsaface ba Musulunci ba ne.
Sarakuna suna zalunci, sun mayar da ikon da ke hannunsu a matsayin makami na tursasa alumma, da dora masu abin da Allah bai dora masu ba, kamar dora masu harajoji a kan abin da suka fi karfin mutane, da kuma yin haraji a kan abin da ba a san ana yi masa haraji ba, gami da kwacen da suke yi da danniyya, wanda har ta kai mutum daya na mallakar mata 1,000. Wannan ne ya sanya talakawa, musamman Fulani suka yi saurin amsa daawar Shehu. Daga nan kuma sai Sarakunan suka fusata da haka, har zuwa lokacin da Allah ya dora Shehu da almajiransa a kansu.
Sayyid Zakzaky ya kuma bayyana cewa a duk tsawon lokacin da Shehu ya yi rayuwarsa, ya yi ta ne a kan neman ilimi da koyar da shi da kuma kira a dowa wa Musulunci tsantsa. Wanda hakan ya sa ya samar da juyi a cikin rayuwar mutane gaba daya. Addini a wancan lokacin tamkar addinin Sarakai ne, su Sarakai suna bukatar addini domin makami ne wanda ya ba su sulda a kan alumma. Sai ya zama addini bai zama abin tsoro ga Sarakai ba, tunda ya zama makaminsu saboda mutane sun dauki Sarki a matsayin shi ne inuwar Allah a bayan kasa. A lokacin an dauki Sarki kusan shi ne komai a kasar Hausa.
A wani bangare na bayaninsa, Sayyid Zakzaky ya ce Shehu ya samu kule daga wadanda ke adawa da shi, musamman a kan yadda ya dauki mata a matsayin wadanda ake yin gwagwarmaya tare da su, da kuma ilmantar da su, tunda a gun masu adawa da shi, su ba su san ana addini da mata ba.
Da Sayyid ya juyo ga kasar nan da yadda alamura suke ya ce, al'ummar yau ta kasance tana aikata barna fiye da lokacin alummar da Shehu ya zo ya same su. Ya ce a lokacin Shehu ya zo ya sami ana tsafi da bori da maita, amma a wannan lokaci al'ummar da muke ciki ana yin tsafi da maita din har an zarce ana yanka mutum a ci namansa a yi tsafi, yayin da Malamai da ya kamata su fadi gaskiya, sai suka buge da biye wa shugabanni duk abin da suka ce shi ke nan ya zauna kuma shi ne daidai.
Daga karshe ya yi adduar Allah ya tona asirin wadanda suke neman bakanta addinin Musulunci, suke hankoron nuna shi a matsayin addinin kashe-kashe da tashe-tashen hankula.
Bayan kammala jawabin ne sai Sayyid ya shiga wajen Sakataren masallacin kasa na Abuja, Alhaji Ibrahim Jega, wanda kuma ya karrama shi, ya bayyana jin dadinsa da zuwan Sayyid, sannan ya nemi ya sa hannu cikin littafin baki na masallacin.
Alhaji Ibrahim Jega ya ji dadin wannan ziyara ta Malam, sannan ya bayyana cewa wannan dakin taro nasu bai taba ganin yawan jama'a kamar na wannan lokacin ba.
Sayyid Zakzaky ya yi dan tsaiko a garin na Abuja, inda ya yi Sallolin Azahar da La'asar sannan ya kama hanyarsa ta komawa Zariya.
