Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Yadda aka gudanar da juyayin wafatin Manzon Allah (S) a Zariya

Daga www.harkarmusulunci.net da Musa Muhammad Awwal

A ranar Lahadin 28 ga watan Safar 1433, wanda kuma ya zo daidai da 22 ga watan Janairu aka gudanar da taron juyayin tunawa da rasuwar Fiyayyen halitta, Manzon Allah, Annabi Muhammadu (S) a Husaniyya Bakiyyatullah, Zariya, wanda kuma Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sayyid Ibraheem Zakzaky ya gabatar da jawabi.

A jawabin da ya gabatar, Sayyid Ibraheem Zakzaky ya fara ne kamar yadda aka saba da taya daukacin al'ummar musulmi juyayin wannan rana ta rasa Fiyayyen halitta, Manzon Allah (S). Wanda kuma ya ce wafatin Manzon Allah babbar musifa ce ga al’umma.

Daga nan sai ya kawo bayanin irin abubuwan da suka faru, musamman a karshen rayuwar Manzon Allah (S) da irin abubuwan da suka faru na musibu, musamman ma bayan kwanciyarsa rashin lafiyar da a cikinta ne ya koma zuwa ga rahamar Ubangijinsa.

Daga cikin abubuwan da Sayyid ya tabo sun hada da Raziyyatu Yaumul Khamis, watau musibar ranar Alhamis, kamar yadda Abdullahi Ibn Abbas ya kira ta, wadda kuma dukkanin littafan hadisai suka ruwaito da siga daban-daban.

A lokacin da Manzon Allah (S) ya nemi a ba shi takarda da alkalami saboda ya rubuta abin da in al'umma suka rike a bayan sa ba za su taba bacewa ba, amma sai wani daga cikin Sahabbai ya ce kar a ba shi, su littafin Allah ya ishe su.

Daga nan ne sai Sayyid ya fara kawo ayoyi daban-daban na Alkur'ani wadanda duk suke nuni a kan bin Manzon Allah (S) cikin dukkanin abubuwan da ya yi umurni da su, ciki kuwa har da wannan abin na musibar ranar Alhamis.

Daga cikin ayoyin da Sayyid ya kawo don kafa hujja, akwai inda Allah (T) ke cewa ‘ma yandiku anil hawa in huwa illa wahyun yuha’. Watau shi Manzon Allah (S) ba ya furuci a kan son zuciya, duk abin da ya fadi wahayi ne.

Haka kuma a cikin Alkur'anin, Allah (T) na cewa ‘Ma aatakumur Rasulu fa khuzuhu wa ma nahakum anhu fantahu’. Watau abin da Manzon Allah (S) ya zo maku da shi ku rike shi, kuma abin da ya hane ku a kansa, ku bar shi. Da dai sauran ayoyi daban-daban wadanda suke a sarari suna nuna cewa ana yi wa Manzon Allah (S) mudlakin biyayya ne a cikin dukkanin abin da ya zo da shi.

Bayan duk wadannan abubuwa ne, kamar yadda Sayyid Zakzaky ya nuna, sai al'umma suka rabu kashi biyu. Sayyid ya ce kuma har zuwa wannan ranar tamu ta yau, haka mutane suke, wasu suka ce zance shi ne abin da Manzon Allah (S) ya fada, wasu kuma suka ce magana ita ce wadda wane ya fada.

A nan ne sai Sayyid Zakzaky ya jawo hankalin al'umma a kan cewa ya kamata kowa ya dubi kansa ya gani, a wanne cikin wadannan gungun guda biyu yake? Yana tare da wadanda suka ce ‘Alkaulu ma kala Rasulullah’ ne, ko kuwa yana tare da wadanda suka ce ‘Alkaulu ma kala Fulan’ ne? Watau ma'ana yana tare da wadanda suka ce magana ita ce wadda Manzon Allah (S) ya fada ne, ko kuwa yana tare da wadanda suka ce magana ita ce wadda Wane ya fada? Sayyid ya jaddada cewa, mu dai muna cewa magana ita ce wadda Manzon Allah (S) ya fada ne.

To, bayan jawabin na Sayyid ne kuma, sai aka gabatar da sallolin Magriba da Isha kamar yadda aka saba, sannan aka gabatar da abincin dare ga mahalarta, sannan Ma'atam.

Daga baya sai Sayyid ya sake zama inda ya karanto ziyarar Manzon Allah (S) da ziyarar Ashura, sannan aka yi addu'a aka sallami jama'a.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan