Wa ke aiko da bindigogi Nijeriya?
Zuwa ga masu karatu.
A bisa zahirin gaskiya ban so na dami masu karatuna da wannan rikitaccen rubutun ba, sai dai kawai domin dalilai biyu ne na ga ya kamata na kawo maku su.
Na farko dai saboda abubuwan da ke ta faruwa ba tare da kakkautawa ba a cikin wannan kasar da kuma halin da ta fada na rashin tsaro. Don haka ne na ga cewa wannan nauyi ne da ya hau kan ’yan jarida da su fahimtar da al’umma matukar iyawarsu, yin hakan zai sanya ko dai ita kasar ta fadaka ta tsira, ko kuma ta ruguje saboda munafunci da kuma halin ko-in-kula.
Na biyu, wannan sako dai yana zuwa ne daga wata majiya da za mu iya cewa ko ma me ya faru a kasar bai shafe ta ba, wato daga wanda shi ba dan kasar ba ne. Ya zo da magana daidai sani da kuma fahimtarsa ba tare da nuna tsoro ko son kai ba, wannan hukunci da ya yanke ko da ya sha bamban da fahimtarmu, yana da dukkanin hujjojin da za mu iya cewa lallai biri ya yi kama da mutum.
Don haka masu karatu, a sha karatu lafiya!
Naku Dakta Aliyu U. Tilde
WA KE AIKO DA BINDIGOGI NIJERIYA NE?
Daga Osae Brown
A lokacin da ya kasance ’yan Nijeriya suna can kan kwalta suna ta ihu da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da janye tallafin man fetur, can kuma a kasar Ingila wani mutum ne mazaunin kasar ta Ingila aka gurfanar da shi a gaban Kuliya ana tuhumar sa a kan dalilansa da kuma wa ya sanya shi jigilar bindigogi har dubu tamanin, gami da albarusai kimanin miliyan talatin da biyu ya zuwa kasar ta Nijeriya? Makaman dai sun kunshi manyan bindigogin nan ne samfurin AK47 guda dubu arba’in, sai kuma kananan bindigogi masu saurin barna guda dubu talatin, da kuma sauran kananan bindigogi guda dubu goma samfurin 9mm.
A bisa rahoton BBC dai mutumin, wanda aka bayar da sunansa da Gary Hyde, ya yiwo jigilar wadannan tarin makamai ne ta ruwa, ba tare da samun amincewa daga hukumomin da suka kamata ba a can kasar ta Birtaniya.
Gary Hyde dai ba shi kadai ne ba a cikin wannan mummunar kwangilar ta kawo makaman Nijeriya. Suna tare ne da abokin harkallarsa, wato Karl Kleber, wani dan kasar Jamus kuma mazaunin Jamus din kamar dai yadda aka shaidawa kotu a can.
Kamar dai yadda aka ci gaba da shaida wa kotun a cikin wannan rahoto na BBC, wadannan mutane biyun suna a matsayin dillalai ne a tsakanin wadansu kamfanoni guda biyu na kasar Poland da kuma ’yan Nijeriya masu sayen kayan da kuma wasu kamfanonin kasar China. Rahoton ya ce tuni har wadannan dillalai biyu sun karbi awalajarsu (kamasho) na wannan ciniki, wanda jimlar abin da suka karba da sunan kamashon shi ne dalar Amurka har milyan guda da dubu dari uku ($1.3m) ko kuma fam din Ingila dubu dari takwas da arba’in daidai (£840,000) ko a Nairar Nijeriya shi ne miliyan dari uku da hamsin da daya (N351,000,00).
Wannan labari dai ya bar tambayoyi masu yawa ba tare da amsa ba. Shin su wanene ’yan Nijeriyan da suka yo odar wadannan makaman? Shin ma dai da gaske ne Nijeriyan ne za a kai wadannan dimbin makaman?
Wani kuma abin mamakin shi ne, tun daga lokacin da waccan kafar yada labarai ta Birtaniya ta bayar da wannan labarin, har ya zuwa lokacin wannan rubutun ita gwamnatin Nijeriyan babu wata sanarwa da ta fitar dangane da lamarin. To, ko dai gwamnatin Nijeriyan ne ta yiwo odar wadannan makaman? Idan kuma ba gwamnatin Nijeriyan ne ta yiwo odarsu ba, to akwai wani yunkuri da ita gwamnatin Nijeriyan ta yi na gano su wanene suke kokarin shigo da wadannan tulin makamai a cikin wannan kasar nata? Albarusai miliyan talatin da biyu fa sun isa su halaka ’yan Nijeriya miliyan talatin da biyu, idan muka kaddara cewa kowane albarushi guda zai sauka ne a jikin kowane dan Nijeriya guda! Wannan sai mutum ya ga kamar da karin gishiri amma dai gaskiyar lamarin shi ne, tilas ne hankalin duk wani dan kasar ya tashi a sa’ilin da ya kasance akwai tulin makamai masu yawa haka can waje a hannu wani da ba gwamanati ba a cikin kasar.
Idan muka yi la’akari da muhimmancin babban dillalin wannan badakalar shigar da makamai kasar ta Nijeriya, wato Gary Hyde, wanda ya yi kaurin suna a duniyar nan wajen cinikin makamai ta bayan gida, an ce shi babban jarinsa shi ne hatsabibiyar bindigar nan mai hadari ta AK-47. Mutumin da kamar yadda ta bayyana a cikin shahararriyar mujallar nan ta Observer ta watan Fabrairu shekarar 2011, cewa shi wannan kasurgumin dillalin makaman a yanzun haka yana fuskantar shari’a ne a kotu a can kasar Amurka a kan fasakwaurin makamai ya zuwa kasar ta Amurka. A wannan mujallar dai ta kasar Birtaniya an misalta Gary Hyde a matsayin “babban algungumin Birtaniya mai haddasa yaki da fadace-fadace.”
A cikin mujallar ta Observer an bayar da labarin cewa gwamnatin kasar Amurkan ta kama Gary Hyde ne tana kuma tuhumar sa da shigar mata da bindigogin AK-47 kirar China ta hanyar fasakwauri har guda dubu shida, wacce kowace dayansu a lokaci guda tana iya daukar harsasai har guda saba’in da biyar.
Har ila yau dai mujallar ta Observer ta gutsuro wani yanki na bincike da rahoton sirri na Wiki Leaks, wanda aka samo tushensa daga ofishin jakadancin Amurka. Rahoton ya yi nuni da cewa a shekarar 2008, babban kamfanin nan mai kerawa da safarar bindigogi, wanda Gary Hyde darakta ne a cikinsa, ya yi kokarin shigar da bindigogin AK-47 har guda 130,000 cikin kasar Libiya ta ruwa. A wannan rahoton na Wiki leaks an nuna Gary Hyde ya zama shi ne dillali a tsakanin sa da wani babban kamfanin kera makamai da har ya zuwa yanzun ba a iya gane ko wanene ba na kasar Ukraine da kuma wasu jami’an gwamnatin Libyan. “Babban abin da ya dami masu sanya ido a wannan cinikin shi ne yawan makaman da ake kokarin shigar da su kasar ta Libya a wancan lokacin, domin a wancan lokacin kwata-kwata kasar ta Libya tana da sojojin da ke yaki a kasa guda 70,000 ne kawai, wadanda yawansu ma bai kai na yadda za su iya amfani da wadannan makaman ba. Masu sanya idon suka ce gwamnatin kasar Birtaniya ta ki sanya hannu ne a kan wannan lasisin cinikin saboda tsoron da take yi na cewa, za a kai makaman kasar Libya ne kawai, amma daga bisani za a canza masu jiha, musamman ma kila za a karkata su ne zuwa ga bangarorin ’yan tawayen da ke samun goyon bayan gwamnatin Sudan ko kuma masu samun goyon bayan Ndjamena a yakin da ake yi can Chadi ko na Sudan.
Kleber, wato Bajamushe, abokin burmin Gary Hyde’s, shi ma ya yi kwaurin suna da hankalin hukumomi ba ya kwantawa da shi a kan harkar fasakwauri da kuma dillancin makamai ta bayan gida. Shi ma a cikin wannan rahoton na mujallar Observer, an nuna a shekarar 2008 hukumar ’yan sanda ta kasar Jamus, da hukumar jami’an tsaro na asiri kasar BKA, sun shiga binciken hadin gwiwa a kan Kleber, don gano irin rawar da ya taka a wani haramtaccen cinikin sayar da makamai samfurin ‘machine gun’ wadanda aka bi da su ta Crocia zuwa cikin kasar Iraki. Wannan kuwa duk ya samo asali ne bisa zargin da ake wa ubangidansa Hyde na cewa kamfanonin da ke da alaka da Hyde din sun sayar da dubun-dubatan bindigogi ga Ziad Cattan, tsohon mai tattalin makaman soji na kasar ta Iraki, wanda ke karkashin Ma’aikatar tsaron Irakin, ba ta hanyar da ta dace ba. Daga bisani dai Cattan ya arce daga Irakin bayan da aka bayar da sammacin kamo shi bisa zargin yin sama-da-fadi ta hanyar karkatar da miliyoyin Daloli.
To, duk dai mahallul Shahid din dai daga wadannan rahotanni shi ne, gawurta da kuma kwarewar wadannan mutane biyu da ake tuhuma da yunkurin shigar da makamai kasar ta Nijeriya. Shin kafin ma wannan ta fasu guda nawa ne kila suka sami nasarar shigar da su cikin kasar ta Nijeriya ba tare da sanin hukumomin kasar ba? Wannan dai shi ne babban abin damuwa ga duk dan kasar da ma mazauna a cikinta.
Kai hankali ma zai kara tashi ne bisa la’akari da cewa a daidai lokacin da aka gurfanar da Hyde a can Birtaniya, can kuma a Ghana sai ga wata babbar motar daukan kaya an kama ta shake da makamai, ita ma ta dumfari kasar ta Nijeriya. Makaman da suka kumshi manyan bindigogi da kuma harsasai. Duk wadannan kame-kamen dai sun zo ne a daidai lokacin da lamarin hare-haren ’yan kungiyar boko haram yake kara kazamta a arewacin kasar ta Nijeriya, ta yadda ake samun tashin bama-bamai kusan a kullum garin Allah ya waye, kuma mutanen da kan bad da kamannu sukan shiga gari su yi ta harbi na kan mai uwa-da-wabi da muggan makamai. Hare-haren ’yan kungiyar Boko Haram, da kuma rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa a Jos, lamurran suna da ban tsoro, musamman ma idan sauran wadanda ake afka ma su ma suka soma tunanin daukar fansa. Shin wadannan tulin makaman da ake ta shigar da su kasar ta Nijeriya za a iya cewa sauran kabilun ne da ake auka ma suke ta tattalin kare kansu ko kuma su ma su kaddamar da nasu harin?
Wannan dai wani mummunan yanayi ne da kasar ta Nijeriya ta tsinci kanta a ciki a duk tsawon tarihinta, kuma duk wani mai yi wa kasar fatan alheri, tilas ne ya tashi tsaye wajen ganin an samo hanyar kwantar da wadannan rigingimun. Kamar yadda na fada ne a wancan rubutun nawa na baya cewa hanyar da kasar Rwanda ta sami kanta a ciki, yana da matukar hadari da ban tsoro a cw kasar ta Nijeriya ita ma ta hau wannan hanyar. Don haka ya zama tilas gwamnatin kasar ta Nijeriya ta gaggauta daukan matakin ganin cewa kasar ba ta sullube ta hau wannan hanyar ba a cikin hamzari.
Wanan kuma shi ne daidai lokacin da ya kamata a ce sauran kasashen duniya sun mike tsaye domin su ga sun agaza wa Nijeriyan. Bisa zahirin gaskiya a fili yake cewa jami’an binciken sirri na kasar, kwarewarsu ba ta kai ga yadda za su iya shawo kan fitintunun da ke kunno kai ba. Don haka tilas ne sauran kasashen duniya su taimaka wa kasar a daidai wannan lokacin. Bai kamata kasashen duniya su zura ido sai irin ta Rwanda ya faru a kasar ba, sannan a ce za su kawo mata dauki. Musamman kasar Chaina, ya kamata ta gargadi ’yan kasuwanta, da cewa wannan ba shi ne lokacin da ya dace su zuzuta wutar rikici a kasar ba, saboda kawai suna son su sami kudi. Kasar ta Nijeriya dai ita ce babbar kasuwa ga kasar ta Chaina a duk fadin Afrika. Matukar Nijeriyan dai ta fada cikin rikici, to kuwa kasar ta Chaina za ta fi kowa cutuwa ta fuskacin kasuwanci.
An ciro wannan makala ce daga http://osae-brown-insights.blogspot.com/2012/01/who-is-sending-guns-to-nigeria.html
Wanda ya fassara mana Umar Abubakar Samaru
