Wasu mata kiristoci sun kai wa Sayyid Zakzaky ziyarar godiya
Wani gungun Kiristoci mata da ke zaune a rukunin gidaje na ‘Danraka Estate’ da ke daura da ABU Congo Campus, Zariya, sun kai wa Sayyid Ibraheem Zakzaky ziyara. Sun ce sun zo ne saboda su nuna godiyarsu game da irin karamci da yake nuna masu kowane lokaci, “musamman ma lokacin rikicin day a faru, inda yake turo mutanensa su kare mu daga masu kawo mana hari”, in ji su.
Suka ci gaba da cewa duk wanda ya damu da halin da kake ciki, ai ya zama wajibi ka nuna godiyarka gare shi. “Wannan shi ne dalilin da ya sa muka zo mu ce wa Malam mun gode”.
Dama dai wadannan mata sun ce sun zo ne su nemi lokacin da za su kawo wannan ziyara, saboda sun san cewa Sayyid Zakzaky mutum ne mai harkoki da yawa, amma suna zuwa sai suka sami dama suka isar da sakon godiyar tasu a madadin sauran ’yan uwansu.
Da yake mai da jawabi, Sayyid Zakzaky ya nuna damuwa ne a kan yadda da mahukuntan da jama’ar gari, duk babu gwani. Su jami’an tsaro suna harbe mutane babu wani laifi, haka kawai don sun yi zanga-zanga. Ya ce haka bai kamata ba. Su kuma mutane bai kamata su dauki doka a hannunsu ba. Sai ya ba da misali da yadda aka yi wa masu zanga-zanga kan karin man fetur, sai aka bade masu wuta. “Tunda zama ya hada mu, to dole ne mu zauna tare”, in ji Sayyid Zakzaky.
Su dai wadannan gungun mata sun bayyana wa Wakilinmu jin dadinsu da wannan zaiyara, kuma sun bayyana cewa da a ce duk sauran shugabannin Musulmin kasar nan kamar Malam Zakzaky ne, da babu sauran rikici a Nijeriya.
A wani labarin makamancin wannan kuma, Hukumar tattara jini da adanawa ta kasar nan NBTS ta yi tattaki zuwa Zariya, inda ta kawo wa Sayyid Zakzaky ziyara ta godiya da kuma yabawa a kan yadda yake ba da goyon baya wajen tattara jinin da take bukata a kowace shekara don taimaka wa mabukata da shi.
Wakilan Hukumar, wadanda suka bukaci ganawa da Sayyid Zakzaky, kuma aka ba su ranar Talatar makon jiya , sun sami damar ganawa da shi ne a Husainiyya Bakiyyatullah da ke Zariya.
Shugaban bangaren kula da lafiya na Harkar Musulunci, ISMA, Dakta Mustafa Umar Sa’eed ne ya jagoranci Wakilan na Hukumar ta tattara jinin.
A lokacin ganawar, daya daga cikin Wakilan mai suna Malama Maryam ta mika takardar godiya da kuma yabawa ga Sayyid Zakzaky.
Tun kafin wannan dai, Sayyid Zakzaky ya bayyana muhimmancin taimakon jama'a wanda ya nuna cewa koyarwa ne daga cikin koyarwar addinin Musulunci.
Haka nan kuma ya kawo tarihin yadda asali ba da jini ya samo asali, musamman ma a cikin watan Muharram, inda Malamai na makarantar Ahlul Bait suka ga cewa maimakon zubar da jini da wasu suke yi saboda juyayin kashe Imam Hussaini (AS), ya kamata ne su rinka ba da wannan jinin ta hanyar da za a iya taimaka wa wasu su rayu.
Wannan ya sa jama'a suka rinka ba da jinin su ana tattarawa ana taimaka wa mabukata, a kasashe daban-daban na musulmi.
Saboda haka sai Sayyid Zakzaky ya bayyana cewa wakilan suna iya zuwa su ci gaba da tattara jinin a lokutan tarurrukan ‘yan uwa da ake gabatarwa a lokuta daban-daban, musamman ma a nan gaba kadan akwai taron makon hadin kai, da kuma na Mauludi da za a gabatar.
A wani bangare na tattaunawar da wajilinmu ya yi da shugabar wannan tawaga, Malama Maryam ta bayyana cewa duk da irin yawan jinin da suke tattarawa, yanzun haka ya kare gaba daya, saboda masu bukata sun nunnuka masu bayarwa yawa.
In dai za a iya tunawa, a lokacin zaman juyayin Ashura da ya gabata ne ma’aikatan wannan hukuma suka kai kayan aikin su a wuraren da ake zaman makokin juyayin Ashura, kuma ’yan uwa da dama suka bayar da gudumawar jini albakacin Imam Husaini (AS). An sami wannan a garuruwan Kaduna, Zariya, Kano, Katsina da sauran garuruwa da dama.
