Ambaliyar ruwa ya shafi miliyan 20 a Pakistan da daruruwan Dubbai a Nijeriya da Nijar


Daga Wakilinmu

Fiye da mutane miliyan 20 ne suka shiga wani mawuyacin hali sakamakon ambaliyar ruwan da ta auka wa kasar Pakistan, inda mutane masu tarin yawa suka rasa mahallinsu, wani adadi mai yawa suka rasa madafa.

Miliyoyin jama’a sun shiga wani mawuyacin hali, wasu sun ce ba su taba ganin bala’i makamancin wannan a kasar da take fama da matsalar fadace-fadacen kabilanci da na bangaranci ba.

Wani abu da ya fi tayar da hankalin jama’a a daidai wannan lokacin shi ne barazarar yiwuwar aukuwar sabuwar ambaliyar ruwa a Pakistan, makonni uku bayan aukuwar ambaliyar ruwa mafi muni a tarihin kasar.

Sabon gargadin da aka sanar ya tilasta wa dubunnan mutane da ke lardin Sindh wanda ke arewa maso yammacin kasar tserewa daga gidajensu.

Wannan sabon labarin ya kara dagula halin tsaka mai wuyar da Pakistan ke ciki a yayin da take fuskantar ambaliyar ruwa mafi muni a tarihinta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan shida na tsananin bukatar agajin gaggawa, amma sai dai da dama har yanzu ba su sami wani taimako ba.

Mahukunta a Pakistan sun bayyana cewa, an yi masu sabbin alkawuran agajin da ya zarta Dala miliyan 300, domin fuskantar bala’in ambaliyar ruwan da ta lalata kusan rabin kasar.

An yi sabbin alkawuran ne, ba yadda kwamitin kai agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, kudaden da ya samu ba su wuce kimanin kashi daya bisa uku na abin da yake bukata ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu miliyoyin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a Pakistan din, ba su sami wani taimako ba. Wasu jama’ar sun yi zargin ana yaudarsu game da tallafin da ake yi masu alkawarin za a ba su.

Jakadan Pakistan a ofishin Majalisar da ke Geneva, Zamir Akram, ya ce wani yankin kasar da girmansa zai kai Ingila, yanzu haka ruwa ya mamaye shi, kuma za a kwashe shekaru kafin a iya sake gina shi.

Ambaliyar ruwan ta mamaye yankuna da dama a kudancin Punjab. A arewa maso yammacin kasar dubunnan jama’a suna matukar bukatar ruwa da abinci.

Jami’ai sun ce yawancin rijiyoyi sun gurbace, don haka akwai barazanar yaduwar cututtukan da ake samu ta ruwan sha.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya tura da jakada na musamman Pakistan din domin taimakawa wajen neman agaji daga kasashen duniya.

Sassa daban-daban na tsakiya da kuma kudancin Pakistan na fama da wannan masifa ta ambaliyar ruwa wacce ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa ambaliyar ruwan ta shafi kimanin mutane sama da miliyan hudu.

Ambaliyar ta tilasta wa miliyoyin mutane barin gidaje, kuma babban abin da ya fi damunsu shi ne rahin abinci. Yara da dama ne ke bukatar agajin gaggawa sakamakon matsalar.

Wadansu masu kai agajin gaggawa na kai agajin, sai dai dubban jama’a sun ce ba su samu wani agajin a zo a gani ba.

Wannan ambaliyar ruwan da aka yi ma ta shafi wasu daruruwan dubban mutane a kasashen Nijar da Nijeriya, inda a wasu daga cikin garuruwan aka yi hasarar rayuka da kuma dukiyoyi. Tuni har jama’a na ta kai dauki ga wadanda abubuwan ya shafa.


Shafin Farko