Hari a Bagadaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane 60

Daga Musa Muhammad Awwal

Akalla mutane 60 suka rasa rayukansu wasu sama da 100 kuma suka jikkata sakamakon tarwatsewar bam a wurin daukar sabbin sojoji a birnin Bagadaza na kasar Iraki da safiyar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa da karfe 7:30 na safe ne wani mutum wanda ya yi damara da jigidar bam ya tarwatsa kansa a wurin daukar sojojin mai cinkoso wanda yake unguwar Baab al-Muatham a tsakiyar birnin Bagadaza. Akasarin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata sojojin Iraki ne.

Kakakin jami’an tsaro, Manjo Janar Kassim Ata ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akwai alamu da suke nuna cewa ’yan kungiyar Alka’ida ne suka yi wannan aika-aika. Harin dai shi ne mafi muni a wannan shekara.

Firaminsta Nur al-Maliki ya ba da umarnin a gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano wadanda suke da hannu a wannan ta’asa.

An kai wannan hari ne yayin da Amurka ke dab da kammala janye sojojinta na bakin daga, duk da yake wasu sojojin dubu 50 za su ci gaba da zama a Irakin, domin taimakawa dakarun Irakin.

Harin zai kara rura wutar muhawara a kan ko a shirye dakarun tsaro na Iraki suke su ci gaba da aikin tabbatar da tsaro daga inda Amurkawan suka tsaya.

Jami’an Amurka na cewa duk da irin wadannan hare-hare da ke kai wa, ba za su sauya shawararsu ta janye sojojin da ke bakin daga ba, domin kuwa a cewarsu har yanzu tashe-tashen hankulan da ake fama da su ba su kai na lokacin da ake ganiyar ta da kayar baya ba.


Shafin Farko