An kama wani zai kai makamai Jos

Daga Wakilinmu

Hukumomi a kasar Nijeriya sun cafke makamai da ake zargin ana dauke da su ne zuwa wuraren da suka yi kaurin suna wajen rikice-rikicen addini da kabilanci, kamar yadda wani jami’in tsaro ya bayyana.

Jami’an tsaro a garin Maiguduri da ke arewa maso gabashin kasar nan da kuma na Filato sun kama mutane shida dauke da bindigogi guda 27 samfurin Kalashnikov wadanda suka boye a cikin mota yayin da suke kan hanyarsu zuwa birnin Jos.

A wani gefe kuma jami’an tsaro sun tsare wata mota dauke da wasu bindigogi 25 su ma samfurin Kalashnikov, kuma masu dauke da su suke tafe ne zuwa jihar Taraba wanda wuri ne da ya yi fama da tashe-tashen hankulan kabilanci da addini. Kawo yanzu dai hukumomi ba su tantance ko daga ina aka dauko wadannan makamai ba.

A watan da ya gabata mutane 8 suka rasa rayukansu wasu 40 kuma suka sami raunuka sakamakon rikicin da ya barke a tsakanin Musulmi da Kirista a garin Wukari na jihar ta Taraba.

Kazalika kuma an samu wasu kudade sama da Naira miliyan hudu. Wadanda aka kama Amos Akila, Daniel Chayi Gyang, Mbono Musa da Yakubu Sule duk sun amince da abin da zargin da aikatawa a lokacin da aka gabatar da su a gaban manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Maiduguri.


Shafin Farko