Su wa ke neman tayar da hankali a Masallacin layin kosai?

Daga Wakilinmu

Masallacin Layin Kosai, wanda aka fi sani da masallacin Tureta, masallaci ne da ’yan uwa Musulmi almajiran Malam Zakzaky suka kwashe fiye da shekara 20 suna gudanar da karatuttukansu ba tare da wata tsangwama ba.

Amma daga bisani sai wasu da suka ayyana kansu a matsayin wai ’yan kwamitin masallacin suna neman su tayar da rikici a masallacin ta hanyar neman sanya karfi don a tayar da ’yan uwan daga wannan masallaci.

Wakilinmu ya labarta mana cewa wadannan mutane wadanda suka hada da Muhammadu Mai Dabino, Alhaji Bala da Alhaji Lawal suna neman fakewa ne da wani wuri da ke jikin masallacin, wanda ’yan uwa ke karantar da yara a ciki tun shekaru da dama.

Majiyar tamu ta ci gaba da shaida mana cewa wannan wuri ya fara janyo hankalin su wadannan mutane ne sakamakon wani gida na jikin wannan wuri da ’yan uwan suka saya don gina babbar makaranta.

Ganin haka ne sai wadannan mutane wadanda suka sanya kansu a matsayin ’yan kwamiti suka ce su ma sai an ba su dama su karantar da wasu marayu. Suna neman cewa sai an ware masu wasu awonni a rana su ma su koyar.

Ganin cewa ’yan uwan ba su amince da wannan tsari bane, sai suka kai kara wajen Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Alhaji Muhammad Sani Aminu, don sanya baki a wannan lamari tare da neman tilasta wa ’yan uwan su ba su wani lokaci a rana.

Shugaban Karamar Hukumar ya kira zama na musamman tsakanin bangaren ’yan uwa da su ’yan kwamitin don tattaunawa. A zaman da aka yi na farko wanda aka a yi a ofishin Shugaban Karamau Hukumar tare da jami’an tsaro na SSS, an saurari duk bangarorin biyu, wanda kuma daga bisani sai shi Shugaban Karamar Hukumar ya nemi ’yan uwa Musulmi almajiran Malam Zakzaky da su duba su ga yiwuwar ware wani lokacin don su ma wadancan su sami damar koyar da marayun.

Daga nan sai ya nemi da a dage wannan zama, a je a duba yiwuwar wannan abu don a sami yadda za a zauna lafiya ba tare da an yi wata rigima ba.

An sanya ranar Talatar da ta gabata don ci gaba da wannan zama, amma zaman bai yiwu ba saboda su bangarorin biyu sun je amma Shugaban Karamar Hukumar ba ya nan.

Sai dai su ’yan uwa Musulmi almajiran Malam Zakzaky suna zargin ana so a yi amfani da wannan wuri ne kawai, amma masallacin ake nema a kore su daga gabatar da karatuttuka da suka dade suna gabatarwa.



Shafin Farko