Gwamnatin Bauci ta ware Naira miliyan 49 don ciyar da masu Azumi

Daga M. Umar Saye

A kokarin da take yi na taimaka wa masu karamin karfi a masallatai da unguwanni, gwamnatin jihar Bauci za ta kashe Naira milyan 49 domin ciyar da masu Azumi a masallatai da ke ciki da wajen garin Bauci kamar yadda ta saba a shekarun da suka gabata.

Shugaban Kwamitin ciyar da masu Azumin a bana, Mai ba Gwamna shawara kan harkar ilmi da inganta tarbiyyar al’umma, Dakta Salisu Shehu, shi ne ya bayyana haka cikin wani taron manema labarai da ya kira a ofishinsa, don bayyana irin shirin da suka yi a bana don ciyar da masu Azumin.

Ya ce za a aiwatar da wannan aikin alheri a masallatan da ke cikin garin Bauci da kewaye, kuma kwamitin nasa shi ne aka dorawa hakkin sanya ido wajen ganin aikin ya gudana a yankunan Kananan Hukumomi 20 na jihar Bauchi kamar yadda aka shirya.

Ya ce a cikin garin Bauci an shirya za a ciyar da a kalla masallatai 80 daga wannan kudi, haka kuma an ayyana irin nau’o’in abinci da ya kamata a ba kowane mai Azumi wanda ya kunshi, shinkafa da miya, ko da taliya da nama, ko shinkafa da wake, ko faten doya tare kuma da nama da dabino da zobo da lemo, ko ruwa da kunun zaki, ko kuma koko da kosai da dai duk irin abin da aka ga mutane suna bukata yadda aka kiyasta za a kashe Naira 250 a kan kowane mutum.

Haka kuma kowane masallaci akwai irin adadin mutane da za a ciyar, ya kuma danganta da yawan jama’ar da suke halartar masallacin, adadin da ya kama daga mutane 100 zuwa mutane 250. Amma kananan masallatai da ba su da yawa ana iya samun mutane 50 shi ne mafi karancin wadanda za a ciyar, a cikin jiha ko a yankunan Kananan Hukumomi.

Dakta Salisu Shehu ya yaba game da kokarin da Gwamna Malam Isa Yuguda ya ke yi kan wannan aiki wanda a baya ba a gudanar da irin sa ba, don haka ya yi fatan mutane su rika sanya shugabanni cikin addu’o’insu don Allah ya kara musu karfin imanin tsarkake ayyukansu da kuma jin kayin wadanda suke yi wa shugabancin tare da taimakawa a kan duk wata hanyar ciyar da rayuwarsu gaba.

Wakilinmu ya halarci irin wadannan masallatai a lokacin da ake rabon abincin inda ya gane wa idonsa yadda mutane suke jin dadin wannan aiki na gwamnatin jihar kamar yadda wani magidanci, Alhaji Ibrahim Isa ya bayyana cewa hakika wannan aiki yana da kyau matuka kuma kowa yana jin dadinsa.

Ya ce da farko suna ganin kamar lamarin abin wasa ne za a shafawa mutane maiko a baki ne a barsu cikin kwadayi, amma sai ya ga irin abincin da ake bayarwa kowa zai iya ci, don bambancinsa da na gidan mutum ba yawa, mai karamin karfi kuwa za a iya bayyana cewa wani ba ya samun irin wannan abincin a gidansa.

Ibrahim Isa ya kara da cewa a karon farko mutane suna kokawa, amma sai ya zamanto har ana cin abincin ana bari saboda yawansa. Don haka ya bayyana cewa musamman kamar masallacin Gwallaga da Masallacin Dutsen Tanshi da na Ustaz Zubairu Madaki akwai tsari mai kyau wajen raba abincin. Don haka ya bukaci a kara yawan irin abin da ake ba wasu masallatan da mutane da yawa suke halarta, musamman kamar masallacin kofar Sarki akwai masu karamin karfi da yawa, ya kamata a kara musu yawan abincin da ake dafawa.

Maryam Abubakar ta kalubalanci masu hannu da shuni su rika shiga cikin irin wannan aiki ba kawai su bar wa gwamnati ita kadai ba, ta ce ya kamata kowane mai rufin asiri ya rika fito da abinci akalla ko na mutum guda ne ya kawo masallaci don masu karamin karfi su samu kashe yunwa da kishiruwarsu, saboda wannan lokaci ne da kowa ya dace ya amfana daga irin ladan da ake samu ba a zuba ido wa gwamnati kadai ba.

Wakilinmu ya samu zantawa da Ustaz Albashir Tahir, wani Malami mai wa’azin musulunci kan wannan aiki na ciyar da masu Azumi da gwamnatin jihar ke gudanarwa. Ya bayyana cewa aiki ne mai kyau, kuma ya kamata kowace jiha da Kananan Hukumomi su yi koyi da irin wannan aiki don neman yardar Allah.

Don haka ya ce idan aka yi la’akari da irin makudan kudaden da gwamnatoci ke kashewa a wasu hidimomin wasanni ko wasu ayyuka marasa amfani ga talakawa, wannan shi ne abin da wasu mutanen za su iya cin moriya daga hukuma kai tsaye. Kuma wannan aiki shi ne zai taimaki shugabanni su kara martaba a idon talakawa kuma ya kasance ta hanyar addu’ar wasu bayin Allah su samu gamawa da duniya lafiya da kuma mulkin lafiya.

Albashir Tahir, ya jawo hankalin mawadata kan su dauki wannan aiki na ciyar da masu Azumi don samun rabauta ranar gobe kiyama. Ya ce bai dace ba mutum ya kasance shi da iyalansa sun yi buda baki da sahur da abinci na gani na fada amma makwabtansa da ’yan uwansa sun rasa abin da za su ci. Saboda haka ya bukaci jama’a su taimaka wajen neman yardar Allah ta hanyar samun ladan ciyar da masu Azumi a wannan watan, ba a bar gwamnati ita kadai ke rawar gani a wannan fanni ba.

Bai gushe ba sai da ya kawo misali; game da yadda iyalai ke yin gidauniya kasashen Larabai da Turai don daukar nauyin sahu-sahu a masallatai wajen ciyar da su abincin buda baki, kowa ya sani kuma yana gani musamman a kasar Saudiyya.


Shafin Farko