|
|
Juma'a 10 Ramadan, 1431 Bugu na 939 ISSN 1595-4474 |
A kafa dokar hana almajiranci
Wani Malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), Shaikh Muhammad Sadik Al-kafawy, ya yi kira ga hukumomi, musamman na arewacin kasar nan da suke gudanar da Shari’ar Musulunci a jihojinsu da su kafa dokar hana almajiranci. Shaikh Al-kafawy, wanda ya furta haka a wajen taron hadin gwiwa da gidan rediyo da talabijin na kasa da ke Kaduna suka shirya ranar Lahadin nan da ta gabata, ya ce hakki ne a kan Gwamnonin wadannan jihohin su tabbatar ba a bar yara suna gararamba a gari da sunan neman ilimin Alkur’ani ba. Ya ce, kodayake neman ilimin Alkur’ani wajibi ne, amma halin da wasu yaran da aka turo birane da kauyuka suke shiga wajen neman ilimin yana kaskantar da addinin Musulunci da kuma jefa rayuwar wadannan yaran cikin hatsari. Shaikh Muhammad Sadik Al-kafawy, wanda shi ne Daraktan Cibiyar bincike ta addinin Musuluci da ke ABU, ya nanata cewa, yanzu akwai hanyoyi da daman gaske da zai zama yaro ya samu ingantacen ilimin addinin Musulunci ba tare da an tura shi wani gari ya yi bara ba. “Yanzu hanyoyin samun ilimi sun inganta, ba wani ilimi da za a bukata da ba za a samu a kowane gari a cikin fadin kasar nan ba”, in ji shi. Ya kawo Ayoyi da Hadisai masu tarin yawa da suke nuni da wajibcin da ke kan iyaye wajen kula da ilimi da tarbiyyar ’ya’yansu. Ya ce ba wata ka’ida a wannan lokacin da za ta halatta wannan dabi’ar da wasu al’ummar Musulmi suke yi na tura ’ya’yansu wasu garuruwan don neman ilimi alhali ba su mallaki hankalinsu ba. “A bari yaro idan ya girma ya mallaki hankalinsa sai ya je duk garin da yake so don neman ilimi”, in ji shi. Shaikh Muhammad Al-kafawy, ya nuna damuwarsa a kan yadda taimakon juna ya yi karanci a cikin al’ummar Musulmi a daidai wannan lokacin duk da kuwa irin dimbin Ayoyi da Hadisan da suke nuni da alfanun da ke cikin wannan aiki na alheri. Ya ce, Manzon Allah (S) ya ce Jibrilu bai gushe ba yana yi masa wasicci a kan kula da hakkin makwabci har sai da ya yi tsammanin za su gaji juna. Shi ma da yake takaitaccen jawabi a madadin Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa’adu Abubakar, wanda bai samu damar halartar taron ba, Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya yaba da namijin kokarin da masu shirya wannan taron suke yi a kowace shekara. Ya ce irin wannan taron zai kara inganta tarbiyya a tsakanin al’ummar Musulmi da kuma kara masu kishin kasa. Don haka sai ya yi kira ga iyaye da su tabbatar sun tarbiyyantar da ’ya’yansu a kan tafarkin addinin Musulunci da kuma koyar da su karatun Alkur’ani. Ya koka a kan yadda wasu iyayen suke watsi da ’ya’yansu a kan titi da sunan koyon karatun Alkur’ani. Ya yi fatan shirin da gwamnatin jihar Kaduna take yi wajen hada karatun Alkur’ani da kuma na boko da kuma koya masu sana’a zai ci gaba, ta yadda idan mutum ya kammala makarantar zai zama ya iya birkila, ko kafintanci, maimakon ya zama yana gararamba a kan titi. Shi dai wannan taron wanda a bana aka ba shi taken ‘’yancin yara da kuma almajiranci a Musulunci’, shi ne karo na biyar. Na farko an tattauna ne a kan ‘shika-shikan Musulunci biyar’, na biyu kuma an yi magana a kan ‘muhimmancin shugabanci a Musulunci’, na uku ‘hadin kan Musulmi’, na hudu kuma aka yi magana a kan ‘aure da rabuwa a Musulunci’.
|
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |