|
|
Juma'a 10 Ramadan, 1431 Bugu na 939 ISSN 1595-4474 |
|
|
|
Malama Fatima Muhammad tana cikin ’yan uwa mata da ke gudun hijira a garin Kaduna bayan da Alu Magakarda Wamakko ya auka wa ’yan uwa na Sakkwato. Ta shaida mana cewa; “lokacin da aka yi wannan waki’ar ina gidan Mahaifana da ke Gidan Igwai. Lokacin na je haihuwar fari ne. Saboda haka abubuwan da aka yi akasarin su ban sani ba, domin an jima ana waki’a cikin gari kafin ta zo Unguwarmu.
“Amma zan iya tunawa wata rana da safe shi Maigidana ya zo nan gidanmu. Na fito waje muna magana da shi sai aka kira shi a waya, ya ce in dan jira shi yana zuwa. Ashe a lokacin an gaya masa cewa ga wasu nan sun biyo shi gidan surukansa su kashe. A lokacin na yi ta jira har dare babu duriyarsa. A ranar ban yi barci ba, domin ban san halin da yake ciki ba, idan ma ka kira shi a waya ba ta aiki. Ashe da barin gidanmu ya nufi jamhuriyar Nijar ne tare da wasu abokanansa, suka kwana biyu a can kafin a nan gidanmu a ji labari.
“Ina nan gida sai ga sako an aiko wa mahaifiyata wai ta je gidan Maigidana ta kwaso kayana domin an ce za a je gidan a kona shi. Sai mahaifiyata ta kada baki ta ce dama an bar kayayyakin, domin yanzu ba ta kaya take ba, idan dai har mijinta ya tsira a bar kayan a can a kona gidan da su a ciki. Nan aka matsa cewa tunda an kwashe na abokiyar zamana, ai babu laifi a kwashe nawa. Haka aka yi a kwashe kayan.
“Bayan wani lokaci sai Maigidan nawa ya kira ni cewa yanzu yana Kaduna, kuma idan na kammala wankan jego zan iya samun sa a Kaduna. Sannan ya bukaci in ci gaba da yin addu’o’in da na saba gudanarwa.
“To dama iyayena ba sun fahimci Harka bane, kuma lokacin da Maigidana ke zirga-zirga nan unguwar jama’a sun gane cewa dan Shi’a ne. Don haka sai aka fara gunaguni, ana ’yan surutai iri-iri a gidanmu cewa wai ’yan Shi’a suna auren mutu’a, suna zagin Sahabbai da dai surutan da ko hankali bai dauka. A wannan lokaci suna yi ne domin in tanka musu, ko kuma mahaifiyata ta ce wani abu, amma muka yi kamar ba mu san suna yi ba. A lokacin ban mantawa mahaifiyata har kira na ta yi tana cewa duk abubuwan da ake fada game da ’yan uwa na san ba gaskiya bane, kada in damu kaina, in kyale su. Kuma ta ce in tabbatar na zauna da Maigidana lafiya, kuma haka aka yi. Daga nan sai na kamo hanya na baro Sakkwato.
“Wannan shi ne dan abin da zan iya tunawa game da wannan matsala. Sai dai zan roki duk wadanda suka karanta wannan labarin su taimaka mana da addu’ar Allah ya kara ba mu karfin jure wannan waki’a. Sannan shi kuma Alu Allah ya yi yadda ya ga dama da shi. Duk na Annabi ya ce, amin”.
Daga Abdullahi Dambam
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) reshen Karamar Hukumar Dambam da ke jihar Bauci kuma mai cibiya a Jos ta shirya tsaf domin tunkarar gasar karatun Alkur’ani na jiha da za a yi na bana a garin Jama’are.
Wannan gasa an gabatar da ita ne a ranar Juma’ar da ta gabata a babban Masallacin kungiyar ta Izala da ke tsohuwar kasuwar garin, inda masu fafatawar da suka fito daga fadin Karamar Hukumar suka rinka baje basira, kwazo da kuma kaifin hadda da suke da shi mazansu da matansu.
Da yake jawabi bayan kammala gasar, Shugaban Majalisar Malamai ta Karamar Hukumar Dambam, Malam Nuhu Abdulmumin, ya fara ne da bayyana dalilin assasa wannan gasa da cewa don sa kaimi ga masu son haddace Alkur’ani. “Duk wanda yake dauke da haddar Fatiha a kansa, in yana tafiya, to kasa ma ta san shi mutum ne na musamman yake tafiya a kanta. To, ina kuma ga in ka haddace izifi guda daga Sabbi zuwa Nasi surori 30”.
Sai dai Malamin ya nuna alihinsa kan yadda Hukuma ta yi wa wannan bangare rikon sakainar kashi, ta kuma fifita ilimin boko. Wannan kuma shi ne ya sa iyaye ba sa damuwa da tura yaransu makarantun karatun Alkur’ani, don sun san ba hanya ce ta yin Kansila ba. Don haka sai ya yi kira ga Hukuma da ta kakkafa irin wadannan makarantun a inda suka dace.
Wannan gasa an gudanar da ita ne a fannoni biyar na Alkur’ani, watau Izifi 1,2,3,5, da kuma 10, inda aka mika kyautuka ga wadanda suka suka zo na daya da na biyu a kowane fanni.
Wani karon batta da ake so a yi a fanni na biyu wanda ya zo na daya Abdul Raseed Ahmad daga Jalam da kyar ya sha a gaban wata yarinya Zainab da maki daya tak. Wanda ya zama gwarzon shekara shi ne Ahmad Sunusi daga Jalam da ya fafata a Izifi 10, ya zo na daya da maki 46.
Bayan kammala musabakar, Wakilinmu ya zanta da Shugaban Alkalan gasar, kuma babban Limamin na Izala, Malam Musa Muhammad yaro, inda ya yaba da kokarin yaran, ya kuma ba da tabbacin samun nasara a gasar jiha da za a yi nan gaba kada a garin Jama’are.
Daga Buhari Daure Daura, jihar Katsina (buharidaure@ymail.com)
Masu iya magana na cewa “mutuwa tonon asiri.” Tabbas ba sai mutum ya yi amfani da tabarau ba za a gane cewa Arewa ta sauya a ruhi da gangar jiki, yankin da ya kawo ci gaba da dauki a yayin da kasar nan ke yakin neman ’yancin kai tare da tallafawa ’ya’yanta har da ’yan kasa da wasu kasashe.
A yau Gwamnoni da dattijai sun gaza zama tsintsiya madaurinki daya, kullum sai jayayya ko rikici za ka ji tsakanin dattijan Arewa. A bisa haka matasan suka rasa kama kai balle a amsa sunan manyan gobe. Zai yi wuya ka ji wani dan Arewa ya kera wani abu, ko ya yi wata bajinta. Kai har yau a Arewa wasu na ganin amfani da ’yanci kamar rashin kunya ne, kuma har yanzu camfi da barace-barace sun zama jiki, balle kananan sana’o’i kamar yankan farce, gadi da tukin acaba. Duk da cewa muna kewaye da attajirai, amma me suka yi wa ’yan layinsu, Kananan Hukumominsu, balle Jihar ko matasan Arewa?
Ganin halin da Arewa ke ciki shi ya sa yankin ya gaza warware matsalolin da suka shafi matasa na zaman banza da rashin aikin yi. A yau idan mutum ya shiga wani birni a Arewa zai iske matasa a zube, ba abin da suke yi sai gararamba daga wannan inuwar zuwa wancan inuwar har dare ya yi, ba karatu, ba kasuwanci. Kai ko an yi karatun ba a aiki da shi, kaico Arewa! Ga uwa-uba matsalar shugabanci, kowa gani yake shi ma Sarkin kansa ne. A bisa haka mun gaza fito da mutum daya a matsayin wanda zai zama Shugaban kasa daga nan Arewa, duk da akwai wanda ake gani ya fi cancanta! Hakan ya sa ake shirya taro a daga, zafi ma ya hana shan shayin! Ko an zauna sai a tashi baram-baram. Lallai gyaran sai Allah.
Kullum sai a rika cewa gwamma jiya da yau, to wai haka za mu ci gaba da zama? Idan manya da dattijan da suke raye a yau ba su yi abin kirki ba, ba za a tofa masu albarka kamar yadda ake wa manyan da suka gabata ba. Matasa ba za su ce Allah ya jikan wane ba, sai gara da babu wane. Kuma a ci gaba da fadar sharrin da ya aikata a rayuwarsa, kuma ko da ya bar dukiya, ba za ta tsirar da ’ya’yansa ba, in banda ma asirinsa ya tonu!
Kowa na da irin gudummuwar da zai iya badawa idan ana son a dawo da martaba da mutuncin Arewa a Nijeriya da idon duniya, sai kowa ya yi abin da ya wajaba a kansa, ta yadda za mu tallafi juna. Kuma kowa ya bi a hankali da wannan duniyar, don wuri ne na bakunta, duk wanda muke gani, wata rana sai labarin abin da ya aikata a adabin da ba ya karya, kuma akwai makoma, inda za a gamu da babban Sarki.
Idan muka kalli Kudu da ’yan Kudu za mu ga cewa sun nuna cewa ci gaba ta kowane fage shi ne burinsu, walau ta kasuwanci, tattali da siyasa, shi ya sa ko a kwanan nan suka ce mutum daya suka amincewa da ya zama shugabansu, inda Gwamnonin yankin suka yi magana da murya daya. Kukan kurciya dai jawabi ne.
Zamani ya sauya a yanzu, kuma a kusan ko’ina a duniya matasa ake dagawa don su yi wakilci a kowane fage, kama daga kasuwa, mukamai a gwamnatance da sarautun gargajiya, kai ko makarantu ka je za ka ji ana alfahari da yara masu kananan shekaru wadanda hazakarsu ta fito fili, ko Malamai masu tashe ko wasu jarumai da suka zama taurari a wani fage don bajinta ko wata baiwa da ke tafe tun ana kuruciya. A yanzu sai mu yi hakuri da kaddarar da ta same mu, mu dage ta yadda za mu yi gini a kan ci gaban wadanda suka gabata, mu tallafa wa juna ko da da kyakkyawan fata ne da sanin cewa idan aka daure aka dage wata rana sai labari.
A ganina mafita ita ce tun a yanzu a fara daukar nauyin matasa ta fuskar neman ilimi da ba su shawarari nagari, ta yadda za a bar karkatar da su a kan son rai. A kan haka wasu za su taso a zahiri da sanin ya kamata. Kuma su kansu matasan su ba na kasa da su shawarar da taimakon da suka ga za su iya ta yadda za a yi aikin gayya kowa ya cudi dan uwansa.
In ji Malam Yusuf Ali Bici
Daga Alhusain Dakace
Daukacin al’ummar Musulmi a ko’ina suke ya kamata su san cewa watan Azumin Ramadan yana da muhimmacin gaske ga rayuwarsu.
Wannan kalami ya fito ne daga bakin wani bawan Allah da ke zaune a cikin garin Kano, mai suna Malam Yusuf Ali a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya.
Malam Yusuf, ya kara da cewa ya kamata al’ummar Musulmin su san da sanin cewa daukacin kwanakin gaba daya rahama ce gami da albarka ke sauka a cikinta dare da rana, saboda haka babu wanda zai samu rabo da daukaka, sai wanda ya kiyaye da barin duk wasu abubuwa wanda Allah ya ce a nisance su don gudun kada Azuminsa ya baci a yayin da mai Azumi ke Azumi.
Don haka Yusuf Ali ya shawarci Musulmi da cewa su shagaltu da aikata abubuwan da za su sa su kai su ga kusanci da Allah Madaukakin Sarki kamar karatun Alkur’ani mai girma da salloli da kuma neman gafarar Allah, tare da addu’o’i da kuma yi wa Manzon rahama salati.
Har ila yau ya yi amfani da wannan dama da kira ga mawadata da cewa su rubanya kyautatawar da suke yi wa mabukata a cikin wata mai albarka, kamar ciyarwa da kuma bayar da kyaututtuka, duk kuma wanda ya aikata wannan a cikin wannan watan Allah kan rubanya masa lada, sannan kuma duk wanda ya saukaka shi ma Allah zai saukaka masa.
Malamin ya yi amfani da wannan dama da jawo hankulan ’yan kasuwa da cewa kamata ya yi su saukaka farashin kayayyakin da aka fi yin amfani da su a watan albarka ta Ramadan maimakon tsawwala farashi ko kuma karin farashi, inda ya bayar da misali da wasu kasashe da suke yin rangwame a harkokin kasuwancinsu ta yadda mai karamin karfi zai iya mallaka; mafi yawanci sun fi aikata haka ne a watan na Ramadan.
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |