|
|
Juma'a 10 Ramadan, 1431 Bugu na 939 ISSN 1595-4474 |
|
|
|
Batun iya rubutu da karatu ga Manzon Allah, Annabi Muhammad (S) yana daya daga cikin abubuwan da ake tafka muhawara a kansa tsakanin masu cewa bai iya rubutu da karatu ba, da kuma masu cewa ya iya rubutu da karatu, har ma ya aikata su a aikace a rayuwarsa. Wannan muhawara ba ta takaita tsakanin Shi’a da Sunna ba, a’a, Sunna ya-su ya-su ma akwai sabani a junansu, kamar yadda a Shi’a ma akwai sabanin fahimta a kan wannan batu.
Wani abu dai da duniyar Musulmi gaba daya ta yi ittifaki a kai shi ne cewa ba wani abu da ya tabbatar da cewa Manzon Allah (S) ya iya rubutu ko karatu kafin a aiko shi da Annabci, ana muhawarar iya karatu da rubutunsa ne bayan fara saukar wahayi zuwa gare shi, domin tarihi ya fayyace sunaye da adadin mutanen da suka iya karatu da rubutu a zamanin jahiliyya, wanda sanin hakan ba abu ne mai wahala ba saboda yanayin waccan al’umma ta zamanin jahiliyya.
A zahiri dai, cibiyar muhawara tsakanin masu cewa Manzon Allah (S) ya iya karatu da rubutu da masu cewa bai iya ba, ita ce hakikanin fassara da ma’anar kalmar “Ummiy” da Alkur’ani ya zo da ita. Masu cewa ya iya rubutu suna cewa kalmar ‘Ummiy’ da ake amfani da ita a kan Manzon Allah (S) tana nufin dan birni ne, kamar yadda ya zo a fadin Allah Ta’ala cewa “Domin ka yi gargadi ga Uwar Alkaryu (Makka), da wanda ke gefenta” (An’am, 92), suka ce kalmar “Umma” a nan ita ce “Ummiy” in an koma tushensu.
Abin sani dai shi ne, masu cewa Manzon Allah (S) bai iya karatu da rubutu ba suna ikirarin cewa rashin iya karatu da rubutu ga Manzon Allah (S) ba nakasu bane, hasali ma karama da mu’ujiza ce gare shi! “Idan Likita yana ta rubutawa marasa lafiya magunguna suna sha, amma shi ba ya shan magungunan saboda koshin lafiya, shi kenan sai abin ya zama nakasa a gare shi, (a ce in dai ba ya shan magani a matsayinsa na mai rubutawa mutane magunguna, to shi nakasasshe ne)?” (Nabiyil Ummiy, 57).
A nazarin masu wannan fahimta: “Tunda Allah Ta’ala ne ke ilmantar da Manzonsa duk abin da ya so, to ai Manzon Allah (S) ba ya bukatar iya karanta wani abu na wani dan Adam, domin ba zai amfane shi da komai ba, kuma ba dole ne ya iya rubutu ba domin duk wata bukatarsa ta rubutu tana biya ta hanyar sakatarorinsa masu yawan gaske, don haka Manzon Allah (S) mawadaci ne ga wadannan abubuwa (wato karatu da rubutu).” (Nabiyil Ummiy, 50).
Amma manyan Malaman Shi’a da dama dai sun tafi a kan cewa Manzon Allah (S) ya iya rubutu da karatu domin wasu ayoyi sun yi nuni ga hakan, misali:- Allah Ta’ala Yana cewa: “Shi ne wanda Ya aiko a cikin mabiya al’adu (marasa iya rubutu da karatu) Manzo daga cikinsu, yana karanta musu ayoyinsa, kuma yana tsarkake su, yana sanar da su littafi da hikima.” (Juma’a, 2). Ga kuma ayar da Allah Ta’ala ke cewa: “Hakika Allah Ya yi baiwa ga Muminai a lokacin da Ya tashi Manzo a cikinsu (zuwa) gare su, yana karanta musu ayoyinsa a kansu, yana tsarkake su, yana sanar da su littafi da hikima, alhali sun kasance kafin hakan a cikin bata mabayyaniya.” (Aali Imran, 164). Sannan ga ayar da Allah Ta’ala ke cewa: “Manzo ne daga Allah, yana karanta wasu takardu masu tsarki, a cikinsu akwai littatafai masu kima da daraja.” (Bayyina, 2-3).
Wadannan sune sashe na ayoyin da masu ikirarin iya rubutu da karatu ga Manzon Allah (S) suke kafa hujjoji da su don tabbatar da ikirarinsu. Abin da suke cewa shi ne wadannan ayoyin sun tabbatar da cewa Manzon Allah (S) ya iya rubutu da karatu, domin Alkur’ani ya ce: “Yana karanta musu ayoyinsa”, a wani wuri kuma ya ce “Yana sanar da su littafi da hikima.” Wasu Malamai sun fassara hikima a matsayin rubutu. Sannan ga inda Allah Ta’ala ke cewa: “Yana karanta takardu masu tsarki, a cikinsu akwai littattafai masu kima da daraja.” Suka ce wadannan ayoyin sun tabbatar da cewa Manzon Allah (S) ya iya karatu da rubutu.
Akidar Shi’a bisa rinjaye ita ce: “Manzon Allah (S) ya iya karatu da rubutu kwarai da gaske! Tabbataccen abu ne cewa Manzon Allah (S) shi ya karantar da daruruwan Sahabbansa karatun addini tun daga Darul Islam, (gidan Arkam Bin Abiy-Arkam) har zuwa birnin Madina. Ya sabawa hankali a ce ga Malami amma bai iya karatu ba. Idan an ce Manzon Allah (S) bai iya karatu ba, sai mu ce, to ta yaya Manzon Allah (S) ke karantar da Sahabbansa?
Game da iya rubutu ma ba yadda za a iya gamsar da tunani cewa Manzon Allah (S) bai iya rubutu ba, domin rashin yin abu ba yana nufin rashin iya shi bane. Shi ya sa ’yan Shi’a suke cewa kamata ya yi a ce Manzon Allah (S) ba ya yin rubutu, ba wai Manzon Allah (S) bai iya rubutu ba! Rashin yin rubutu daban, rashin iya rubutu daban! Ko ba a lura ba?
Cikin hujjojinsu na iya rubutun Manzon Allah (S) akwai batun Musuluntar Umar Bin Khaddabi, kissar Musuluntarsa ta nuna cewa, ya zo gidan kanwarsa Fatimah Bint Khaddab ne, sai ya same ta da Allo tana karatun Alkur’ani, sai ya ce ta ba shi Allon, ita kuma ta hana, ta ce masa shi najasa ne bai da tsarki, don haka ba zai yiwu ya taba rubutun Alkur’ani ba. Da ya kalli Allon sai ya ga Bismillah da suratu Hadeed a jiki. Tambayarmu a nan ita ce, wa ke koyawa Sahabbai rubuta ayoyin na Alkur’ani? Shin wanda bai iya rubutu ba zai iya koyawa wani? Sannan ya za a yi ya iya gane abin da ya ce a rubuta, daidai aka rubuta ko ba daidai ba in har bai iya rubutu ba?
Har ila yau, akwai wani Hadisi da ke tabbatar da cewa Manzon Allah (S) ya yi rubutu da hannunsa. An karbo daga Anas Bin Malik ya ce: “Manzon Allah (S) ya yi wani rubutu sai ya ce “Wannan (misalin burin) dan Adam ne da ajalinsa” (Bukhari, 2. Riyadus Salihin, 128).
A wani Hadisi na Ibn Mas’ud, ya kawo misalin yadda Manzon Allah (S) ya taba yin rubutu (duba Riyadus Salihin shafi na 128 ka gani), cikin abin da ya kawo wanda Manzon Allah (S) ya rubuta akwai “Al’Ajal” da kuma “Al’amal”, sai kuma “Al’A’aradh.” To, ta yaya mutumin da ya rubuta wannan da hannunsa za a ce bai iya rubutu ba?
Da aka tambayi Imam Sadik (AS) cewa: “Wasu na cewa wai Manzon Allah (S) bai iya karatu da rubutu ba”, sai ya ce “Karye suke yi…… ta yaya zai koyar da wasu abin da shi bai iya ba? Na rantse da Allah, Manzon Allah (S) yana karatu, kuma ya iya rubutu”. (Hakkul Yakin, 136).
A takaice, tabbataccen abu ne cewa Manzon Allah (S) ya iya karatu da rubutu, ya koyar da Sahabbansa karatu, kuma tarihi ya ambaci yadda ya yi rubutu kamar yadda muka ambato kadan daga ciki.
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |