Bulaliya
Gaskiyar lamari (12)
Tare da Bala Muhammad MakosaKHALIFAN ANNABI (SAWA) NA UKU, IMAM HUSAINI (AS) SHAHIDIN KARBALA: Ahlul Baiti, itaciyar gidan Annabta, sun tabbatar da cewa wannan littafi na Imam Ali (Sahifa), ya koma ga hannun Imam Husaini bayan shahadar Imam Hasan (AS). Kamar yadda aka ruwaito a cikin littafin Basa’ir al-Darajat, na Muhammad Ibn Hasan Al-saffar, mujalladi na 9, shafi na 148; a lokacin da Imam Husaini yake gab da zai fuskanci tsinannu makiya Allah a Karbala, sai ya kira babbar ’yarsa, Fatima ya ba ta wani babban littafi.”
A wata ruwayar kuma duk a cikin wannan littafin da aka bayyana sunansa a sama, an ruwaito cewa; a lokacin da Imam Ali (AS) ya fuskanci Iraki domin fafatawa, ya bai wa Ummu Salma, (RA), matar Manzon Allah (S) wannan littafi mai cike da dimbin ilimin gidan Annabta; daga bisani ta damka shi a hannun Imam Hasan, shi kuma ya bai wa Imam Husaini, daga nan ya koma hannun Imam Ali Ibn Husaini (AS); haka aka ci gaba da gadar da shi ga ’ya’yan itaciyar gidan Annabta.
Bari in dan yi baya kadan: “A cikin littafin “Manakib Ali Ibn Abi Talib”, na Ibn Shahrasub mujalladi na 2, shafi na 37, an ruwaito cewa, kafin Manzon Allah (S) ya yi wafati, ya bai wa matarsa Ummu Salma (RA), wani littafi mai cike da dimbin ilimomi, kuma ya gaya mata cewa; “Kada ki bai wa Wasiyyina wannan littafin, sai lokacin da da kansa ya zo ya nemi ki ba shi. A lokacin da al’umma suka yi wa Imam Ali mubayi’a, sai ya je ya same ta ya amshi wannan littafin.”
A dai cikin wancan littafi na Basa’ir al-Darajat, an karbo daga Imam Ali Ibn Husaini wanda ya ce; “Muhammad Ibn Hanafiyya, da ga Imam Ali, ya je ya sami Imam Husaini yana mai tambayar sa kan irin gadon da mahaifinsu ya bar masu. Daga nan Imam Husain ya ce: ‘Mahaifinka ya bar Dirhami 700 ne kacal’. Daga nan Ibn Hannafiyya ya ce: ‘To sanar da ni gadon ilimin da ya bar mana’. Daga nan Imam Husaini ya dauko masa wani littafi wanda fadinsa da tsawonsa bai fi tsawon yatsa ba, wanda ke cike makil da ilimomi kai tsaye daga gidan Annabta”.
A takaice, wannan littafi wanda Manzon Allah (S) ya bai wa Ummu Salama (RA) a matsayin amana, domin ta ajiye wa Imam Ali, ya bambanta da wanda Manzon Allah ya zaunar da Imam Ali ya yi masa “shifta”, ya rika rubutawa. Na farkon, shi ne littafin da ke cike da yadda Shugaba zai tafiyar da jagorancin jama’a, daya littafin kuwa, yana cike ne da hukunce-hukuncen addini, tarihin al’ummomin da suka gabata da sauransu.
Wani karin bayani a nan shi ne, Zuri’ar Gidan Annabta, suna matukar girmama uwar Muminai matar Manzon Allah (S) Ummu Salma (RA), wadda ta fi dukkanin sauran matayen rikon amanar Manzon Allah da Ahlul Baiti; wadda ta yi iyakar bakin kokarinta wajen taimaka masu, da kuma adana sahihan bayanai na addini, da ba su kariya.
Sanin irin tuggun da aka rika shirya wa Ahlul Baiti tun bayan wafatin Kakansu Muhammad (S), da yadda wadanda suka rike mulki bayan wafatin Manzon Allah suka yi ta kokarin bice hasken Allah da kuma sahihin koyarwar Manzon Allah da sunnarsa tsantsa, da kuma yadda suka yi ta kirkiro sunnar son rayukansu da sunan Ijtihadi; an ruwaito a cikin littafin Kitab Sulaym Ibn Qays, a shafi na 165 cewa, wata rana Imam Husaini ya yi wata huduba a Mina yana mai cewa “Kuna gani, kuma ku shaida ne kan irin yadda wadannan azzaluman suke yi mana (tun bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), da kuma gallazawar da suke yi wa mabiyanmu. A domin haka ne yanzu zan gaya muku wata magana; kuma idan kun tabbatar da cewa gaskiya na gaya muku, to ina so ku yi abin da na fada a aikace. Ku saurari duk abin da nake fada, kuma ku rubuta; idan kun koma lardunanku cikin kabilunku, ku kira wadanda kuka aminta da su, ku sanar da su, domin ina gudun cewa, za su batar da sakon addini tsantsa (daga Manzon Allah). To, bari na yi burki a nan, kan bayanin yadda Khalifa, kuma Wasiyyin Manzon Allah (SAWA) Imam Husaini (AS), ya gadar da tsantsar gangariyar addini daga Kakansa, ba domin ya kare ba, sai domin rairayowa ne kawai nake yi.
KHALIFAN MANZON ALLAH NA HUDU, IMAM ALI IBN HUSAIN AL-SAJJAD:
Bayan wafatin mahaifinsa Imam Husain, shi ma Imam Ali Ibn Hussain, khalifan Manzon Allah na biyar, kuma wasiyinsa, tsatso-kuma reshe daga jikin itaciyar gidan Annabta, ya dora daga inda mahaifinsa ya tsaya, na gadar da tsantsar addini daga kakansa Muhammad (SAWA); ya rubuta littafai da yawan gaske; littafansa da suka fi shahara sune “Risalat Al-Huquq da Sahifa Al-Sajjadiyyah, wadda ake yiwa take da “kundin addini”.
A cikin littafin Al-Fihrist na Shaik Al-Tusiy, shafi na 68, lamba na 138, an ruwaito cewa Abu Hamzah Al-Thamaliy ya ce: “A lokacin da nake karanta wani littafi wanda Imam Ali Ibn Husain ya rubuta, na ci karo da wani bayani kan yadda ake tsantseni, wato zuhudu ko gudun duniya, sai na kwafe wurin, na nuna wa Imam Ali Ibn Husain, kuma ya tabbatar da cewa daidai na rubuta.”
An kuma ruwaito a cikin littafan Man-la-Yahduruhul-Faqih, na Shaik Al Saduq, mujalladi 4, shafi na 204, da littafin Ma’ani Al-Akhbar cewa, a duk lokacin da aka tambayi Imam Ali Ibn Husaini wani bayani kan addini, yakan duba littafin Imam Ali ne wanda ya gada domin ya ba da amsa.
Ku dubi dai yadda Imam Muhammad Baqir (za mu zo cikakken bayani a kansa) da kuma Zayd Ibn Ali, kuma daga wanda muke bayani a kansa, wato Imam Ali Ibn Husaini, suka rika tattara bayanai da ilimomin addinin Kakansu Muhammad (SAWA). A kan haka nan, har ma Shaikh Ahmad Muhammad Shakir, wanda ya duba littafin nan mai suna “Mafatih Kunuz Al-Sunnah, ya tabbatar da cewa littafin da Zayd Ibn Ali ya rubuta, mai suna Al-Majmu, lallai shi ne din ya rubuta shi, domin yana cikin littafan da malaman farko a can baya suka rika amfani da shi. Haka nan kuma, a cikin littafin Tahmidun Li-Tarikh Al Falsafah al-Islamiyyah, an ruwaito Asad Hydar yana cewa: “Zayd Ibn Ali, ya rubuta littafi wanda yake cike da hukunce-hukuncen addini da aka samu kai tsaye daga cikin gidan Annabta, wanda aka samo shi a cikin tsofaffin littafan da suke ajiye a dakin adana littafan tarihi na Girkawa, a bangaren littafan tarihi na jama’ar kudancin yankin Larabawa. Wannan littafi yana daga cikin mafiya dadewa a cikin littafai wadanda suke tattare da hukunce-hukunce na addini; kuma wannan littafi an ba shi suna “Musnad Al Imam Zayd Ibn Ali”.
Dadin dadawa kuma, tattara bayanan da aka yi kan al’amuran addini daga karni na farko, wanda Abu Hamzah AlThamaliy da sauran mabiya gidan Annabta suka hada guri daya; wato Risalat Al-Huquq da Sahifa AlKamilah Al-Sajjadiyya suna nan har yanzu ana amfani da su, domin neman tsira a duniya da lahira. To fa, ina fata kuna tare da ni daki-daki, domin jin yadda Khulafa’ur Rashidin din gaske, kuma rassa daga itaciyar gidan Annabta, wasiyyan Manzon Allah (SAWA) suka rika gadar mana da sahihin addini tun daga kan Kakansu zuwa ’ya’ya da jikoki. Bari mu dakata a nan, kan Khalifa na hudu, mu shiga batun Khalifa na biyar Imam Muhammad Ibn Ali Al-Baqir.
KHALIFAN MANZON ALLAH (SAWA) NA BIYAR, IMAM MUHAMMAD IBN ALI, AL-BAQIR:
Bayan wafatin Imam Ali Ibn Husaini, daga nan sai Imam Muhammad Ibn Ali dansa, ya zama Khalifan Manzon Allah na biyar. Kada ku manta da cewa a baya na kawo bayanin inda a lokacin da Manzon Allah (SAWA) yake bayyana Khalifofi- Wasiyyansa, ya bayyana Imam Muhammad Ibn Ali a matsayin wanda Allah ya kira da suna “Baqir” a cikin Attaura, har ma ya gaya wa sahabinsa Jabir (RA) cewa idan ya riski zamaninsa ya ce yana gaishe shi. To, a kan shi yanzu za mu dan taba magana.
An bayyana cewa, lokacin rayuwar Khalifa na biyar Imam Muhammad Ibn Ali Al-Baqir, da na dansa Imam Ja’afar Sadiq, sune mafiya lokutan masu karsashi wajen yada koyarwar gidan Annabta; ilmomi daga Manzon Allah kai tsaye ta hannun zuri’ar gidansa wadanda Allah ya tsarkake. Domin a daidai wadannan lokutan ne Allah ya kawo karshen Daular Banu Umayya, sannan Daular Abbasid suka soma jan ragama, wanda ya shagaltar da su. A don haka ne zuri’ar gidan Annabta suka dukufa wajen yada addinin Kakansu Muhammad (SAWA) gangariya.
Wani muhimmin abu wanda ya faru a lokacin khalifancin Imam Baqir da dansa Imam Ja’afar Sadik shi ne, sun yada ilimin addini na kimiyyar Musulunci wanda suka gada daga Kakanninsu, da ya samo asali daga Manzon Allah (SAWA), da ilimin hukunce-hukunce na addini. A lokutan ne aka sami masana ilimin gidan Annabta da yawan gaske masu fikira, wadanda suka ci gaba da yada wannan addini. Haka nan kuma, wadannan Imamai tsarkaka, zuri’ar gidan Annabta, sun yi tsayin daka wajen ragargazar irin abubuwan da wadansu sarakuna suka yi da sunan addini, mai suna Ijtihadi, tun bayan wafatin Manzon Allah, (SAWA) har zuwa kan su Mu’awiyya da sauransu. Imaman, sun rika gabatar da littafin Sahifa na Imam Ali, wanda Manzon Allah (SAWA) ya rika yi masa shifta yana rubutawa da hannunsa, mai dauke da dukkan hukunce-hukunce na addini.
A kan haka, an ruwaito cewa, wata rana Imam Muhammad Baqir ya gaya wa sahabinsa mai suna Zurarah cewa: “Ya Zurarah, ka yi hankali da wadannan mutane wadanda suke bayanin addini a bisa son rayukansu da tunaninsu. Domin sun himmatu wajen yada addinin da aka kirkira, suna kokarin batar da addini na gaskiya (daga Manzon Allah). Suna ta kirkirar hadisan karya da fatawowi na bogi wadanda suka dace da bin son rayukansu. A kan irinsu ne Allah (T) yake fadi a cikin Alkur’ani yake cewa “Allah ne ya umurce ku da yin haka, shin kuna kirkirar karya a kan Allah? (10:54).” (Shaik Al Mufid: Al Amaliy, 12:51).
A cikin littafin Al-Rijal, a shafi na 360, lamba 966, an ruwaito cewa Adhafir Al Sayrafiy ya ce “ya yi rakiya ga Al-Hakam Ibn Utaybah zuwa ga Imam Muhammad Al-Baqir. Da suka isa gare shi, sai Hakam ya yi ta yi wa Imam Baqir tambayoyi. Kodayake Imam Baqir ya girmama shi sosai, amma ya nuna masa rashin jin dadinsa kan yadda Hakam ke so ya yi jayayya da shi kan wadansu amsoshi wadanda ya ba shi. Nan da nan Imam Bakir ya umurci dansa ya dauko masa littafin Imam Ali Sahifa, wanda ya gada daga Kakanninsa, har zuwa kan Manzon Allah (SAWA). Da aka kawo masa, ya bude littafin, yana nuna wa Hakam wannan hukunci da ya yi masa musu a kai; littafin mai dauke da rubutun Imam Ali, wanda Manzon Allah ya yi masa shifta yana rubutawa.
Daga nan Imam Baqir ya kalli Hakam yana mai ce masa: “A duk inda kuka je kai da abokin tafiyarka, ba za ku taba samun cikakken ilimi gangariya kai tsaye daga Manzon Allah ba, sai daga gare mu; mune wadanda Mala’ika Jibril ke kaiwa da komowa a gidanmu yana saukar da wahayi”.
Shin jama’a, tambayata a nan ita ce da akwai wadansu da suka isa su fadi haka idan ba zuri’ar gidan Annabta ba, rassa daga itaciyar Annabta? To, idan amsarku ita ce eh, a ina ya kamata mutum ya nemi addini sahihi?
Za mu ci gaba insha Allah.
Nasir Fudiyya ne a Baki’a, inda kabarin Imam Hasan yake, yana karanta ziyara, da kuma inda yake kokarin shiga cikin Baki’a din. Duk wannan zai fito a cikin faifan ‘documentry’ din da aka sa wa suna GASKIYAR LAMARI
