Bulaliya
Gaskiyar lamari (13)
Tare da Bala Muhammad MakosaYADDA KHALIFOFIN ANNABI (S), SUKA GADAR MANA DA ADDINI TSANTSA
A ci gaba da bayyana mana yadda Khalifofin Manzon Allah (S) kuma wasiyyansa suka gadar mana da addini tsantsa daga Manzon Allah (S), a cikin littafin Alkafi, mujalladi na 7, shafi na 112. An karbo daga Muhammad Ibn Muslim, wanda ya ce; “Imam Muhammad Bakir, ya bude mini littafin Sahifa; abin da na soma gani shi ne, an rubuta kamar haka: “Idan masu gadon mamaci sun kansance ’ya’yan ’yan uwansa ne, ko kuma kakansa, to za a raba masu abin gadon dai-dai. Ni kuma sai na ce; “Iyayena su zama fansa a gare ka ya Jikan Manzon Allah (S), amma a yanzu masu hukunci ba haka nan suke aiwatarwa ba idan za su yi rabon gado”. Imam Muhammad Bakir ya amsa min yana mai cewa; “Hakika, wannan littafin (Sahifa), rubutun Imam Ali ne (AS), kuma Manzon Allah (S), ya rika gaya masa yana rubutawa”.
A wani tsantsan ilimi kuma kai tsaye daga gidan Annabta, an ruwaito a cikin littafin Ma’ani Al-Akhbar, na Shaikh Al Saduk, shafi na 219 zuwa 220, an ruwaito cewa, Ibn Uyaynah Al-Basriy, ya ce ya kasance yana wurin a lokacin da aka kawo wa Alkali Abi Layla wata matsala domin warware wa. Abin da ya faru shi ne: “Wani mutum ne a lokacin yana raye, sai ya bai wa wasu danginsa wani gida domin su kasance a cikinsa, ba tare da ya ayyana masu tsawon lokacin da za su kasance a cikin gidan ba. Bayan da mutumin ya mutu, masu gadonsa da kuma wannan mutumi wanda gidan ke hannunsa suka gurfana a gaban Alkali Ibn Abi Layla, wanda ya yanke hukunci, yana mai cewa “Ina ganin wannan maganar a bar ta kamar yadda take a lokacin da mai wannan gida yake raye”.
Ko da jin haka, sai Muhammad Ibn Muslim Al-Thaqafiy, wanda yake wurin ya yi farat ya ce; “Ai kuwa hukuncin da ka yi, ya sabawa irin wanda Imam Ali ya yi a matsala mai kama da wannan”. Alkalin ya tambaye shi, yana mai cewa; “Me ka sani game da yadda ake warware wannan matsala?” Sai ya ba da amsa da cewa; “Imam Muhammad Bakir, ya fadi cewa, Imam Ali (AS) a lokacin da aka kawo masa irin wannan matsalar, soke maganar ba da gidan ya yi, sannan ya raba gado ga masu gado”.
Nan take Alkalin ya tambaye shi idan yana da hujja mai kwari da za ta tabbatar da maganarsa. Daga nan, Muhammad Ibn Muslim Al Thakafiy ya gabatar da gamsassun hujjoji daga gidan Annabta, cikin littafin Sahifa na Imam Ali, wanda kuma ya gamsar da wannan Alkalin.
A cikin littafin Basa’ir Darajat, na Muhammad Ibn Hasan Al-Saffar, shafi na 165, Abdulmalik ya ruwaito cewa, wata rana Imam Muhammad Bakir (AS), ya sanya dansa Imam Al Sadik ya kawo masa littafin Sahifa na Imam Ali. A cikin littafin, akwai inda aka rubuta cewa: “Iyaye mata, ba su da wani kaso a cikin gadon filaye (gonaki) wadanda mijinsu ya mutu ya bari ga masu gado.” Daga nan sai Imam Bakir ya ce; “Na rantse da Allah, wannan rubutun Imam Ali ne (AS) ya rubuta da hannunsa, a lokacin da Manzon Allah ya yi masa shifta, yake rubutawa.
Haka nan kuma, a cikin dai wancan littafi na Basa’ir Darajat, shafi na 9, da littafin Al-Kafi, mujalladi na 1, shafi na 400; An karbo daga Abu Basir, wanda ya ce, wata rana ya tambayi Imam Muhammad Bakir, kan ko ya halatta ba da shaida kan masu zina, (ko kuma amsar shaidar mazinaci)? Imam Bakir ya ba shi amsa da cewa bai halatta ba. Abu Basir ya ci gaba da cewa; “Daga nan sai Hakam Ibn Uyayna da ke wurin, ya karyata Imam Bakir, yana mai cewa ba haka nan abin yake ba”.
Imam Bakir na jin haka sai ya ce; “Ya Allah! Kada ka yi masa gafara, Allah bai saukar da ayarsa ga Hakam ba, yana fadin cewa; “Wannan tunatarwa ce gare ka da al’ummarka ba”. (Kur’an:43:44). Daga nan Imam Bakir ya sake cewa; “Na rantse da Allah, babu inda za a sami ilimi na gaskiya (tsantsa daga Manzon Allah, sai daga gare mu Ahlul Baiti; mune wadanda Mala’ika Jibril ke sauka a cikin gidanmu yana kawo wahayi”.
A cikin littafin Al-Amaliy, na Shaikh Al-Mufid, a shafi na 64, Muhammad Ibn Muslim ya ruwaito cewa Imam Muhammad Bakir ya ce: “Hakika, duk mutanen da suke son neman gaskiya, da kuma ajiye bayani na gaskiya, babu inda za su same ta sai daga gare mu Ahlul Baiti. Ku sani, Aliyu Ibn Abi Talib, ta wurinsa wannan gaskiya ta fito, shi kuma ya samo ta ne kai tsaye daga Manzon Allah (S). A domin haka, idan aka sami wadansu jama’a suka rude, suka saki turbar gaskiya, to kada su yi kuka da kowa, sai dai su zargi kawunansu. Idan kuwa sun kasance a kan tafarkin gaskiya, to ba shakka ta hannun Aliyu Bin Abi Talib ne, wanda Manzon Allah ya shayar da shi.
Dadin-dadawa, Imam Muhammad Bakir, ya adana wadansu littafai na addini da yawan gaske domin masu zuwa daga baya, wadanda ya samu daga kakanninsa rassan itaciyar gidan Annabta, da kuma wadansu Sahabban Manzon Allah, wadanda suka yi riko da wasicin Manzon Allah, suka bi tafarkin Ahlul Baiti sak, ba su karkace ba, ballantana su ci amanarsa. Haka nan a lokacin rayuwarsa, ya ba da fatawowi da yawan gaske ga almajiransa wadanda su kuma suka rubuta cikin littafai.
A haka ne ma, a cikin littafin nan mai suna Al-Sunna Kablal-Tadwin, na Muhammad Ajjaj Al-Khatib, a shafuka na 354 da 355, ya ce “Imam Muhammad Bakir, dan Ali Ibn Husaini, ya rubuta littafai da yawan gaske, wadanda dansa Ja’afar Al-Sadiq ya gada daga gare shi, ya ci gaba da aiki da su”.
A cikin littafin Takyid Al-Ilm na Al-Khatib Baghdadiy, a shafi na 104, an ruwaito cewa Abdullahi Ibn Muhammad Ibn Akil, Ibn Abu Talib ya ce; “Imam Muhammad Baqir yana gayyata ta, a lokacin rayuwarsa, inda mukan ziyarci Sahabin Manzon Allah Jabir Ibn Abdullahi (wanda ya rayu har wannan zamanin, kuma ya yi riko da wasiccin Manzon Allah na babu wadanda za a bi sai Ahlul Baiti, kuma ya isar da sakon Manzon Allah ga Imam Bakir, wanda ya ce idan ya riski zamaninsa ya mika gaisuwarsa a gare shi). Idan za mu je gare shi, mukan tafi da abin rubutu wanda aka yi da kasa, domin mu ji sakon Manzon Allah daga gare shi domin mu rubuta.
Bari mu tsaya a nan kan bayanin yadda Khalifan Manzon Allah na biyar, kuma daya daga cikin wasiyansa, Imam Muhammad Bakir, ya gadar da tsantsar addinin Musulunci daga Kakansa Manzon Allah (S) da kuma iyayensa, rassa daga itaciyar gidan Annabta. Yanzu bari mu je ga Khalifa na shida.
KHALIFAN MANZON ALLAH (S) NA SHIDA, IMAM JA’AFAR IBN MUHAMMAD AL SADIQ.
Bayan wafatin Imam Muhammad Bakir, sai dansa Ja’afar ya ci gaba daga inda ya tsaya don isar da sakon Manzon Allah (S) gangariya, kai tsaye daga gidan Annabta. Babban abin da ya fi mayar da hankali a kansa shi ne tattara ilimomika wadanda ya gada daga iyaye da kakanninsa rassan itaciyar gidan Annabta, sannan kuma ya rika gabatar da littafin nan na Sahifa, mai dauke da rubutun hannu na Imam Ali, wanda ya gada daga mahaifinsa; yakan duba shi wajen amsa tambayoyin Sahabbansa.
Wata rana, Abu Basir Al-Muradiy, ya taba tambayar Imam Ja’afar kan hukuncin da ya shafi yadda ake yin rabon gado, a bisa koyarwar gidan Annabta. Sai Imam Ja’afar ya ce masa; “Kana so in nuna maka amsar wannan tambayar taka a cikin littafin Ali, wato Sahifa?” Abu Basir ya tambaye shi cikin mamaki yana mai cewa; “Har yanzu wannan littafi na Ali yana nan?”
Imam Ja’afar (AS) ya ba shi amsa da cewa, wannan littafi ba zai taba bacewa ba har abada”. Daga nan ya fito da wannan littafin ya nuna wa Abu Basir a cikinsa inda aka rubuta kamar haka: “Idan wadanda za su ci gadon mamaci, sun kasance ta bangaren iyayensa ne na maza da na bangaren mata, to iyayen ta bangaren maza, suna da kashi uku a cikin yawan abin da mamacin ya bari, su kuwa ta bangaren mata suna da kashi daya”.
Shi dai Abu Basir, yana daga cikin mabiya Ahlul Baiti, kuma dan Shi’arsu, amma duk da hakan nan ya rika kokwanto kan wannan littafi na Sahifa wanda Imam Ali ya rubuta da hannunsa, a lokutan da ya kasance tare da Manzon Allah (S) yana gaya masa yana rubutawa. Dalilinsa kuwa shi ne, yana sane da yadda wadansu da suka rike mulki da sunan Musulunci a bayan wafatin Manzon Allah, suka yi ta jirkita koyarwar Manzon Allah sahihi, zuwa ga son rayukansu, har ma wadansu daga cikinsu sun kona Hadisan Manzon Allah. Amma bayan da Imam Ja’afar Sadik (AS) ya nuna masa wannan littafi, kuma ya tabbatar masa da cewa ba zai taba bacewa ba har abada, daga nan ya aminta.
Ana yi wa Imam Ja’afar kinaya da Suhufi, domin irin yadda ya rika tattara bayanai da littafai na Kakanninsa itaciyar gidan Annabta (AS). Akan haka ne ma aka ruwaito cewa, Imam Ja’afar Sadik yana kaunar wannan suna da ake kiransa (suhufi), har ma yakan ce; “Gaskiya ne, domin ni ma’abocin littafi ne, domin na karance littafan kakannina Annabawan Allah, Ibrahim da Musa (AS). (Ilal Al-Shara’i, mujalladi na 5, shafi na 89).
Imam Ja’afar Sadik (AS), a lokacin rayuwarsa, ba shakka ya karfafa wa al’umma rubuta duk ilimin da suka samu daga gidan Annabta, kafin su soma yada shi, saboda ya zama wannan ilimi bai bace ba, kamar yadda aka yi ta kokarin yin hakan daga makiya gidan Annabtan. An ruwaito a cikin littafan Jami- A-Hadith Al Shi’a, mujalladi na 1, shafi na 298, da kuma Kitab Asim Ibn Hamid Al Hannat, a shafi na 33, an ruwaito cewa Abu Basir ya ruwaito yana mai cewa; “Imam Ja’afar Sadik ya taba gaya mana cewa ‘wata rana mutanen Basra sun taba zuwa suka same ni suna tambaya idan ya dace su rubuta ilimomin da suka samu’. Ni kuma na tambaye su cewa, me ya hana ku rubutawa? Bai kamata maku soma koyarwa ba, har sai kun rubuta”.
Imam Ja’afar, ya kara tabbatarwa al’ummar wancan zamanin, da mu kuma na wannan zamanin har zuwa karshen duniya cewa, koyarwar Manzon Allah tsantsa wanda ba a jikkita shi ba, ba zai taba bacewa ba har abada, sannan mutane za su same shi ne kawai idan sun kasance mabiya gidan Annabta. A domin haka ne kuma Imamin ya rika karfafa bayyanawa da gabatar da littafin Sahifa na Imam Ali, wanda ya gada daga mahaifi da kakanninsa, da kuma littafin Al-Jafr, wanda yake kunshe da wasu boyayyun ilimomi daga Manzon Allah (SAWA), wadanda babu wadanda suka san su sai Ahlul Baiti, wadanda Allah ya tsarkake-tsarkakewa, sune itaciyar gidan Annabta.
A cikin littafin Basa’ir Darajat shafi na 165, an ruwaito Imam Ja’afar Sadik yana fadin cewa; “Na rantse da Allah, mu Zuri’ar gidan Annabta, mun mallaki littafai guda biyu (baya ga Alkur’ani) wadanda aka yi su da fatun dabbobi; na farko yana dauke ne da rubutun Imam Ali (AS), dauke da dukkanin abubuwan da Manzon Allah (S) ya sanar da shi ya rika rubutawa. Na biyun kuma, littafi ne, shi ma yana dauke da rubutun Imam Ali, da Manzon Allah ya sanar da shi ya rika rubutawa, wanda a cikinsa yake kunshe da duk wata maslaha da bil’adama yake bukata. Idan ba zuri’ar gidan Annabta ba tsarkakakku, su wanene suka isa su mallaki wannan? To, daga wurinsu za mu nemi sanin addini ko daga wurin wadansu?
Za mu ci gaba insha Allah.
