NAZARI

Addinin Allah zai Tabbata (2)

Daga Haruna Shelleng


Mai karatu mun dan dawo baya kadan a wannan makalar saboda gyara wasu kurakurai. Sai ka ci gaba.

Akwai wani jawabi da Sayyid (H) ya yi a Ramadan din 1430 a lokacin da ya bayyana shirin jefa bom a gidansa, ya ce, “YAU SHEKARA 40 INA BAUTAR ALLAH BISA YAKINI”. A lokacin shekarunsa 58. Wato a cikin 58 ya yi shekaru 40 yana ibada bisa yakini. Wani Malami dan Darika da ya ji wannan, sai ya ce duk wanda ya fadi haka kuma bai kai matsayin ba, zai mutu ne. Wato duk abin da yake yi bisa tabbas babu shakka ko kokwanto, kuma ya bayyana masa a fili karara zahiri hakika bisa gaskiya kamar hasken rana.

Allah (T) ya ce, “ka bauta wa Ubangiji har sai yakini ya zo maka”. Shi ya samu wannan matsayin. Imam Ali (AS) ya ce, da za a yaye shamaki, da bai kara masa yakini ba. Wato ko da zai ga wuta da Aljanna ne babu abin da zai canza yakinin da yake da shi. Duk maganar iri daya ce, illa lafazin ne ya bambanta.

Mutane masu irin wannan ‘Qualities’ sune ya kamata a bi, don suna kan gaskiya kuma babu shakka suna kan shiriya, kuma za su kai mu ga tsira. Su ba irin mutanen da za su sayar da addininsu da abin duniya bane. Yanzu haka ana addini ne idan zai biya bukatar duniya, idan kuma bai biya ba, sai a ce karatu bai yi albarka ba, in kuma ya biya, sai a ce karatu ya yi albarka, ‘what a misconception?’

An ruwaito cewa wata rana Imam Ali (AS) yana Salla sai wani Bakhawarije ya karanta Ayar da ke cewa idan ka yi shirka da Allah sai ayyukanka su bace. Yana nufin Imam Ali (AS) ya yi shirka kenan. Sai Imam Ali (AS) ya ba shi amsa da wannan Ayar “ka yi hakuri lalle alkawarin Allah gaskiya ne, kuma kada wadanda ba su da yakini su ba ka tsoro.” To, ka ji kafa hujja har a cikin Salla. Imam Ali (AS) ya tabbatar wa Bakhawarije cewa ba shi da yakini a kan abin da yake yi. Saboda haka ba a bakin komai yake ba. Hukuncin wanda bai da yakini ne, wanda a kullum mu mutane masu yakini ya kamata mu bi irin su Maulana (H).

Sannan Sayyid (H) ya ci gaba da jawabi yana cewa, “wallahi ko an ki, ko an so, sai addinin Allah ya tabbata”. Bindiga ba za ta iya murkushe addinin Allah ba. Abin da hankali da ilimi ya gina, hauka ba zai iya rusawa ba. Bisa yakininsa ya fadi haka cewa addinin Allah sai ya tabbata. Ka ga babu makawa kenan. Ni dai tun bayan wannan jawabin na Sayyid (H) na yi masa wani sabon hukunci na cewa, duk abin da ya fada ko ya yi, to bisa yakini ne.

Malam Yakubu Yahya da yake yin sharhi a kan batun yakinin nan cewa ya yi, “dama haka muke zato, kuma wannan ya gaskata mana zatonmu, kuma yin Salla a bayansa ba karamin falala da daraja bane, kuma sai wanda Allah ya zaba”.

Wani Malami da ya zo Makon Hadin Kai, da ya yi Salla bayan Malam sai ya ce, bai taba jin sakina da natsuwa a Salla tunda yake ba kamar yadda ya ji sad da ya yi Salla tare da Malam. Alhaji Hamid Danlami cewa ya yi, idan ya bi Malam Salla abin da yake ji, to sai dai a bayan Ma’asumi ne zai ji kwatankwacinsa.

A laccar tunawa da Imam Khomaini (KS) ta bana, Sayyid (H) ya ce in Allah ya tsawaita rayuwarsa za mu ci gaba da amfana da wasu baiwa da Allah ya yi masa. Ma’ana har yanzu akwai wasu abubuwa muhimmai da yake ganin cewa lokaci bai yi ba tukunna balle ya bude mana su. Wato duk wadannan abubuwan da ya ba mu akwai wasu da bai nuna mana ba. Dama Sayyid (H) ya taba cewa, “duk abin da ya bai wa mutane ’yan uwa ko addu’a ko zikiri ko wata falala, to sai ya shekara 10 yana yin ta tukuna kafin ya ba su. Har iyalinsa haka yake yi masu, wato duk abubuwan da Sayyid (H) ya ba mu cikin cokali ne cikin abin da Allah ya sanar da shi.

Muna rokon Allah (T) Mahaliccin kowa da komai, Ubangijin bayi don albarkacin Manzon Tsira (S) da Wilayan Imam Ali (AS) da martabar Sayyida Zahra (AS) da A’imma (AS), muna rokon ka tsawaita rayuwar wannan bawa naka har zuwa bayyanar Imam Mahdi (AF). Kuma ka bar mu tare da shi duniya da lahira don mu ci gaba da cin gajiyar ajiyar da ka yi tare da shi, ya Allah.

A makon jiya na kawo wani waje da nake cewa Sayyid Ali Khamene’i ya gaya wa Malam Zakzaky wata magana a kunne, amma ban kawo takamaimen abin da ya fada ba. Mutane sun bukaci in bayyana. Shi ne na ga ya dace in kawo shi a wannan kashi na biyu. Ga abin da ya ce masa; “Inna lazi farada alaika Kur’ana laraddu ka ila mi’ad”. Ma’ana, wanda ya lizimta maka Alkur’ani zai mayar da kai zuwa makoma”. Malamai sun fassara wannan Ayar da cewa tana nufin cewa tunda ana magana ne a kan kissar Annabi Musa da Fir’auna ne Allah ya fadi haka, kuma ya halaka Fir’auna ya tabbatar da Musa. Sai Allah ya sanar da Manzonsa kisar ya nuna cewa shi ma zai yi galaba kan mushirikan Larabawa kenan.

Kenan tunda Sayyid Ali Khamene’i ya zabi ya karanta wa Malam wannan Aya a kunnensa yana masa albishiri ne da cewa shi ma zai yi galaba a kan azzalumai masu adawa da shi, kuma Allah zai tabbatar da addini ta hannunsa, kamar yadda ya tabbatar wa Musa, ya halaka Fir’auna, sannan ya tabbatar wa Manzon Allah ya halaka mushirikan Larabawa, to kai ma Sayyid Zakzaky ina maka bushara da cewa Allah zai tabbatar maka da addini, ya halaka azzalumai masu tsangwamar ka. Allahu Akbar! Bushara kan bushara, nasara kan nasara.

Sayyid Zakzaky (H) ya ce “akwai wata magana wanda a wuri na kawai za ku iya jin ta. (Ban da shi babu wanda zai iya gaya mana shi). Wannan Harka mustakilla ce, tana cin gashin kanta ne (independent) babu wanda yake ce mata ta yi ko ta bari.” Ko waye kuwa mutumin, a cikin gida yake (Nijeriya) ko wajenta (Iran dss). Sayyid yake ganin abin ya dace bisa mustawarmu da al’ummarmu da kasarmu, sai ya tsara manhajin Harka bisa inayar da Allah ya yi masa. Babu ‘External influence;’ ba mu ci ladan kuturu ba, balle mu yi masa aski. Babu shakka Harka bangare ce ta Harkar Musulunci ta duniya, amma bai mayar da mu masu karbar umurni ba daga wasu. Kowa yana gani ne, ba wai yana umurni ba. Har manyan Ayatullahi idan suka hadu da Sayyid Zakzaky (H) suna cewa ne kai ka fi sanin abin da ya dace da ita. Kuma gaskiya babu abin da ya fi ’yanci dadi. Idan har ka mika hannu, to ba za ka mike kafa ba. Muna kuma kara yi masa jinjina da ya sa muka zama masu ’yanci kuma ’ya’ya.

Sayyid Zakzaky (H) yana tausaya wa masu rauni, musamman mata, yara fakirai da marasa galihu na cikin al’umma. Misali Sayyid (H) ya ba da 200,000 ga wani Kwamiti na Sisters domin bai wa masu sana’a wanda ba su da jari su yi sana’a, sai su biya bayan wani lokaci. Wacce ta karbi 20,000 za ta biya cikin wata shida. Sai ka ba da 3,300 kuma wani wata; a wata na shida na karshe kenan sai su ba da 3,400. Wasu sun karbi 15,000 su za su biya cikin wata biyar. Masu 10,000 kuma wata hudu. Sannan masu 5,000 za su biya cikin wata uku. Wadda ta gama biya sai a bai wa wanda sunanta ke layi. Ya zuwa yanzu Sistoci kamar guda 30 suka amfana da ‘scheme’ din a tsakanin Zariya da Kaduna.

Lokaci bayan lokaci Sayyid (H) kan yi wa Sistas da yake majalisi da su kyautar kudi a munasaba, ko Ghadeer, Nisfu Sha’aban. Ko kuma haka ma kawai, kamar a Rajab din nan 17 ga wata ranar Talata ya ba su kyautar 50,000, kowacce ta tashi da 700. Wani lokaci har sukan samu 1000 har fiye ma. Tausayin Sayyid (H) ga Sistas bai faduwa ko a Maulud na Sayyada Zahra (AS) na bana ya ce ’yan uwa maza su shagwaba Sistas har sai shagwabar ta yi yawa tukunna. Ku tuna suna da rauni, sannan kuma aka sa su a karkashinku.

Da Ramadan Sayyid (H) na rabawa makusanta, makwabta na Gyallesu, Kwarbai, Malaman Allo da mabukata maza da mata marayu, yana ba su shinkafa masara, gero, suga, taliya. Ko a wannan Ramadan din ma ya yi haka. Sayyid Zakzaky (H) yana raba kamar kimanin buhu 100 na shinkafa, buhu 100 na marasa, haka ma gero. Wanda ya sani da wanda bai sani ba, ’yan uwa ma suna cin gajiyar haka, su ma suna shiga rabon. A gaskiya mu da muke kusa muna ganin irin tasirin da wannan tagomashi da su Sayyid (H) ke yi yake kawo wa Harka da Sayyid (H), da canza tunanin mutane da kusanta su ga Harka. Kyautar nan har da ’yan kaza Sayyid (H) yana ba su.

Shi dai Sayyid (H) yana da shimfidar fuska ga musakai da fukara’u, shi ya sa za ka ga su Sarkin Makafi na Tudun Wadan Zariya da su Sarkin Kutare Zariya suna zuwa tarukanmu, suna kuma ziyarar Sayyid (H) a shekara. Lalle kam Sayyid Zakzaky (H) gatan mararsa gata ne. Duk sad da suka zo sai mun buga zuwansu a jaridarmu da kuma a shafinmu na Intanet, wanda hakan yana nufin mu a wurinmu wannan muhimmi ne. Kuma labari ne da ya cancanta duniya ta sani.

Tunda aka fara Rajab da Sha’aban, kullum sai mun yi buda baki gidan Sayyid (H) mun ci dabino, mun sha shayi, mun ci shinkafa da nama kullum. Duk ran da aka yi babu nama sai Sayyid Zakzaky (H) ya yi fada, kuma har zuwa karshen Ramadan abin zai ci gaba, a kuma yi mana tuwon Salla har da abin sha. Kai wasu hidima sai su Sayyid Zakzaky (H). Shi kuma ba ya ma cin abinci, nasa shayin ma daban ne, bayan an ba mu wance sai ya kara mana da nasa. Wata buta mai sirri ga ta karama, amma irin albarkar da take da shi sai wanda ya gani.

Tambayi ’yan Hijira na Sakkwato da suke Zariya ka ji labarin hidima da su Sayyid (H) ke masu, ba zai fadu ba, wasu kaya ai sai su amale. Bari in dan misalta a duk watan duniya yana ba su 30,000 domin hidimarsu, ban da ya yi kaza da kaza. Kamar duk daki ya sa masu fanka, kafet, labule, katifa, sattelite, deep freezer a gidan Sistas da na ’yan uwa maza, ‘just to mention few’.

Sayyid (H) ba ya tausayin kudi idan dai don yi wa Allah da bayinsa ne hidima, akwai wani mai ’yan matsalar kwakwalwa yana ziyara majalisi na yamma a gidan Sayyid (H) duk san da ya zo, to kudi kam ya samu in har ya zo to babu makawa sai Sayyid (H) ya ba shi, kuma a ambulan kuma da yawa. Wata rana muna magana da wani dan Sayyid (S) sai ya ce min, ai abin hannun Sayyid (H) ba na ’ya’yansa bane, na masu bukata ne. Ya gaji iyayayensa da kakanninsa wurin karimci da baiwa. Wannan yana nuna cewa idan da baital mali yana hannunsa ne zai bai wa bayin Allah damarsu, sai ya ba su abin su.

Bari in dawo ga iftar da na yi a baya, akalla a kullum sai mutum kamar 200-230 sun sha ruwa a gidan Sayyid (H) tun Rajab da wanda ya yi Azumi da wanda bai yi ba. Almajiran Gyellesu da su ake yin buda baki. Kai ko abinci har da nama kyauta ga duk wanda ya zo. Wani lokaci adadin mutane kan fi hakan ko kasa da haka. Idan an yi ruwan sama akan ragu.

Lokacin da ake Kwarbai, Sayyid (H) ya taba cewa za a dinga cin abinci a gidansa bayan kowace Salla a lokacin ana fama da rashin abubuwa. A lokacin mun kasa fahimtar yadda za a yi, sai ga shi abu ya zama ‘reality’.

Sayyid (H) dai ya tafi da ladan kowa a komai; ‘zahab ahlul duthur bil ujur’. Ga ladan ciyarwa ‘at the same time’, ga kuma na shiryarwa a tafarkin Allah, lada goma da goma, kamar yadda wani Sharifi ya ce, “ ko Sayyid (H) bai cewa kowa komai ba, ladan da ya samu na shiryar da mutane tafarkin Iyalan Gidan Annabi ya ishe shi gobe kiyama”.

Wata baiwa da Allah ya yi masa shi ne, duk abin da ya ce, sai ka ga babu wani abu da wani zai ce fiye da abin da ya ce. Haka nan ma idan ya tsara abu babu wanda zai tsara fiye da nasa ballantana a fannin ilimi abin sai wanda ya sha. Ka saurari Rediyon Nagarta ranar Juma’a da Lahadi karfe 9:00 zuwa 10:00 na dare (kodayake a Ramadan an dan samu canji, ana sa wa ne daga karfe 11:00 na dare zuwa 12:00, a kuma maimaita da karfe 7:00-8:00 na safe. Akwai wanda ake sa wa da karfe 4:00-5:00 na Asuba a gidan talabijin na AIT. Ka ji Tafsir ga kuma Nahjul Balagah da yake karantawa a Fudiyyah Islamic Centre Dan Magaji duk Litinin da yamma. Ka saurara ka ji laccocinsa a kan Maudu’ai daban-daban. Abin sai wanda ya ji. Zuwa majalisi a gidansa kullum da yamma ban da Litinin da Laraba za ka amfana da dimbin baiwar da Allah ya yi masa na ilimi, fikira da bayani.

Ina taya Sayyid (H) murna da cika shekara 59 a duniya. Da fatan alheri da koshin lafiya, da tsawon kwana, da nasara a kan makiya na mutum da aljanni, da kyakkywan fata. Allah kuma ya bar mu tare da shi. Allah ka tabbtar mana da addini, ka kuma rusa azzalumai. ’Yan uwa mu yi koyi da Sayyid Zakzaky (H).


Shafin Farko