Tare da Musa Muhammad Awwal +23483 451 4631
A shirye muke mu taimaka wa harkar ilimi a Kano
Dakta Binta Tijjani JibrinDaga Alhusain Dakace
A kwanakin baya ne Dungiyar Makarantu Masu Koyar Da Darussan Musulunci, wato ‘Association of Model Islamic School (AMIS)’ da ke Kano suka gudanar da taron kungiyar na shekara-shekara, tare da kaddamar da sabuwar kalandar Musulunci.
Da take yi wa manema labarai bayani, jim kadan da kammala taron, Shugabar kungiyar ta jihar Kano, Dakta Binta Tijjani Jibrin, ta ce makasudin taron na bana shi ne su fadakar da al’ummar Musulmi muhimmancin watan Al-Muharram. Shi ne ma, in ji ta, ba sa gudanar da taron sai a watan na Muharram. Shugabar kungiyar ta ‘AMIS’ ta kara da cewa, taron nasu har ila yau na kara nuna wa mutanen jihar Kano karfin kungiyar, tare da yawan makarantun jihar. Haka kuma ta shawarci hukumar ilimi a jihar Kano da cewa, a duk lokacin da za a rika gudanar da wasu harkoki na ilimi a jihar, to a rika tuntubar su domin kungiyarsu a shirye take ta taimaka wa ilimi a jihar ta Kano. Dungiyar, in ji ta, masu makaranta ce, sannan kuma Musulmi zalla ’yan jihar Kano, kuma sune suka fi sanin iyaye ilimin da ya kamata yaro ya samu da kuma wata irin tarbiyya ya dace a ba shi.
Dakta Binta Tijjani ta ce, muddin ana bukatar yaro ya samu ilimi mai inganci, to dole sai an kashe kudi. Ta kara da cewa, ya zuwa yanzu akwai kimanin makarantu 53 a jihar Kano da suka yi rijista da su, duk kuma daukacin wadannan makarantu kafin a kafa su sai da aka bi hanyoyin da suka kamata sannan aka samar da su.
Daktar ta kuma ce, wannan kungiya an kafa ta ne a shekarar 1997 a garin Minna ta jihar Neja karkashin shugabancin Malama A’ishatu Lemu, matar Shaikh Ahmad Lemu. Kuma abin farin ciki, in ji ta, ya zuwa yanzu kusan daukacin jihohi duk akwai ta.
Daga karshe, ta yi amfani da wannan dama da yin kira ga iyayen yara da su rika yin taka- tsantsan da makarantun da za su kai yaransu, domin wasu makarantun da ake kai yara ba su dace da koyarwar addinin Musulunci ba, ballantana al’adunmu.
Moroko ta kori jiragen ruwan kasashen Turai daga gabar ruwanta Dasar Moroko ta bukaci jiragen ruwan kasashen Turai da su fice daga cikin iyakokinta na ruwa cikin gaggawa.
Wannan matakin na gwamnatin ya zo ne a matsayin mai da martani ga Tarayyar Turai da ta dakatar da aiki da yarjejeniyarsu, da ita.
Ma'aikatar harkokin wajen Moroko ta fitar da wani bayani ta ce: “Dukkanin jiragen ruwan da suke aiki a karkashin wannan yarjejeniyar su fice cikin gaggawa kafin daren Larabar makon jiya ya raba.”
Ma'aikatar harkokin wajen ta bayyana matakin na Turai da cewa abin takaici ne kuma yana da sakamako mai hatsarin gaske a kan yadda bangarorin biyu za su rika aiki tare a nan gaba.
Dungiyoyi masu zaman kansu da dama a Turai sun dade suna sukar yarjejeniyar wacce suke dauka tana cutar da yankin Yammacin Sahara.
Abin da ya sa muka hade waje daya
In ji Shugaban kungiyar IzalaDaga M. Umar Saye, Bauci
Gagarumin zaman da rassa biyu na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) suka shirya a garin Kaduna ranar Larabar makon da ya gabata ya samu gagarumar nasara, lamarin da ya samar da maslahar zama karkashin inuwa guda domin yin aiki ga addinin Musulunci tare a Dungiyar.
Zaman dai ya faro ne tun makonni uku da suka wuce bayan rasuwar Shugaban kungiyar reshen Kaduna, Alhaji Musa Maigandu Muhammad, inda Shugaban reshen Jos, Shaikh Sani Yahaya Jingir ya bukaci kowa ya taho a zauna a sulhunta, don a tafi tare a dinke duk wata matsalar jagoranci da ke tsakaninsu.
Kafin zaman na Kaduna, dukkan shugabannin sassan guda biyu kowanne ya gayyaci jama’arsa, inda suka zauna suka tattauna kan matsalolin da ake son tunkara kafin daga bisani aka hadu a garin Kaduna kowane sashe ya samar da wakilansa, inda suka shiga dakin tattaunawa rukuni-rukuni kafin daga bisani aka cimma nasara a zaman da ya gudana a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.
Zaman ya samu sanya albarkar duk wani mai fada-a-ji na kungiyar a kasar nan da kuma talakawan da suke ganin hakan babbar nasara ce ga kungiyar, don haka tun kafin ranar Larabar sai da aka gudanar da gagarumin wa’azi a ranar Talata da dare, inda aka sanya Shaikh Muhammad Kabir Gombe da Alaramma Yahuza Bauci, wato mai jan baki da Malamai daga sassan biyu, suka gudanar da wa’azi mai ratsa jiki, wanda mahalarta wajen na kusa da na nesa kowa ya bayyana jin dadi game da irin hadakar Malaman sassa da Alarammomi da aka rika yi suna gudanar da wa’azin tare da nasihohi ga juna don a samu nasarar abin da aka sanya a gaba.
Zaman ya samar da maslaha, inda sassan suka yarda da Shaikh Sani Yahaya Jingir, shugaban sashen Jos ya zamanto shugaba na kasa baki daya, yayin da kuma Sakataren kungiyar Izala na kasa gefen Kaduna, Shaikh Muhammad Kabir Gombe ya kasance shi ne Sakataren kungiyar na kasa.
Haka kuma mataimakin Shugaban kungiyar na Kaduna, Shaikh Abdullahi Bala Lau, ya kasance Shugaban gudanarwa na kasa. Shaikh Yusuf Sambo Rigachukun, wanda a baya shi ne Shugaban Majalisar Malamai na kasa reshen Kaduna yanzu ya kasance mataimakin Shugaban hadaddiyar kungiyar, wanda zai mara wa Shaikh Sani Yahaya Jingir baya a lokacin shugabancin kungiyar. Dukkan Malamai da shugabannin kungiyar da suka halarci zaman na Kaduna, sun yi farin ciki da wannan hadewa don fuskantar alkibla guda.
Cikin hirarsa da Wakilinmu, Shaikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa sulhu alheri ne, don haka suka yi farin ciki da wannan shawara da Shaikh Jingir ya kawo, kuma sun taho ne don a tafi tare a gina kungiyar don ciyar da addinin Musulunci gaba. Ya shawarci dukkan mabiyansu kan su dauki lamarin da muhimmanci, kowa ya cire son zuciya a yi aiki tare don a ciyar da kungiyar ta Izala gaba. Shi ma Sakataren kungiyar na kasa a yanzu, Shaikh Muhammad Kabir Gombe ya bayyana cewa wannan babban al’amari ne da kowa ke farin ciki da shi, don haka ya shawarci dukkan Musulmi su yi riko da igiyar Allah kada su rarraba, kamar yadda ya zo cikin Alkur’ani mai girma. Ya kuma bayyana cewa, za su ci gaba da ratsa kasar nan da kasashen Afirka har wasu kasashe na duniya, ta hanyar yin wa’azi kamar yadda Alkur’ani da Sunna suka bukaci a gudanar don gina addinin Allah.
Shi ma sabon Shugaban, Shaikh Sani Yahaya Jingir ya yaba da wannan majalisi da aka gudanar, haka kuma ya bukaci kowa ya yaki Shaidan ya tsaya da duga-dugansa wajen ciyar da hadin kan Musulmi da Musulunci gaba don a-gudu-tare-a-tsira-tare.
Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun, mataimakin Shugaba na kasa ya shawarci sauran kungiyoyin addinin Musulunci da suke da irin wannan matsala kan su hade waje guda don tunkarar kalubalen da ake fuskanta daga abokan gaban addinin Musulunci.
Ya ce, shaharar da kungiyar Izala ta yi shi ya sa ake gane bambancin da ke tsakani a baya, amma akwai kungiyoyin Musulmi da suka rarrabu, don haka su ma ya kamata su yi koyi da wannan shiri na kungiyar Izala su daidaita duk wata rashin fahimtar juna, don a samu ci gaban Musulunci da Musulmi a kasar nan da duniya baki daya.
Bayan wannan taron na hadin kan, kungiyar ta kira wani gagarumun taron wa’azin kasa a garin Dutse na Jihar Jigawa da aka gudanar a ranekun Asabar da Lahadi, inda a wajen taron suka jadadda wannan hadin kan da suka samu a tsakanin su.
Gwamna Gaidam ya rantsar da sabon Jojin Yobe
Daga Muhammad Maitela Damaturu (mmaitela@yahoo.com)
Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya rantsar da sabon Babban Jojin jihar, Mai Shari’a Garba Musa Nabaruma, da Shugaban Hukumar ba da ilimi bai daya (UBE) na Jihar, hadi da membobi biyu daga Hukumar zabe mai zaman kanta, a ranar Alhamis da ta gabata a Damaturu. Nadin sabon Babban Jojin ya zo ne bayan murabus da tsohon Babban Jojin jihar, Mai Shari’a Baba Saje Gujba (OFR) ya yi a watan da ya gabata.
Kafin nada Mai Shari’a Musa Nabaruma, shi ne Shugaban kotun sauraren kararrakin zaben Gwamnoni da Majalisun Tarayya a jihohin Yobe, Anambara, Ondo, Kaduna, Imo, Kano, Osun da Kuros Riba a 2003 zuwa 2011, kuma Shugaban Kwamitin Ma’aikatan Shari’a a Jihar Yobe daga 2005 zuwa nada shi sabon Babban Jojin.
A jawabin Gwamnan Jihar bayan rantsuwar kama aiki ga Babban Jojin, ya bayyana cewa: “Muna kyautata zaton sabon Babban Jojin da ya kasance mai gaskiya da rikon amana a lokacin gudanar da ayyukansa.”
Gwamnan ya kuma fadi cewa, ba da izinin nada sabon Babban Jojin ya fito daga gare shi kuma hakan ya fara aiki tun 30 ga watan Nuwamba 2011, bayan shaidar yabo daga Majalisar Shari’a ta kasa a kansa, tare da tabbatarwar Majalisar dokokin Jihar kamar yadda tsarin kundin mulkin kasar nan ya tanada.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya kara da cewa: “Mun tabbatar cewa Babban Jojin zai yi amfani da dimbin kwarewarsa da hazakarsa wajen ba da gudummawa ta hanyar kokari wajen sanya tsoron Allah da hangen nesa da kuma hana tarnaki ga cin hanci, wanda ta haka ne sashen shari’a zai habaka.”
Ya kuma kara cewa, ta la’akari da muhimmancin sashen, kuma akwai bukatar aiwatar da hazakarsa daidai wannan lokaci, wanda ta haka ne za a samu kyautatuwar al’amura tare da yaduwar adalci, wanda sune mahadin dorewar tsarin dimokradiyya. Kuma ya kara da cewa, gwamnatin Jihar za ta ci gaba da tallafa wa bangaren shari’a ta hanyar samar da motoci, gina wasu kotuna gami da gina gidajen ma’aikatan Ma’aikatar ta Shari’a a fadin Jihar.
A wani gefe kuma, Gwamna Gaidam ya ce gwamnatin jihar ta yanke shawarar nada Alhaji Gagarau Isa Bizi a matsayin Shugaban Hukumar ba da ilimin bai daya (UBE) ta jihar, gami da wasu kusoshi a Hukumar zabe mai zaman kanta (SIEC) ta jihar, Alhaji Abba Disa Gadaka da Alhaji Bulama Wakil Umar, wanda hakan ya zo bayan gamsuwa da cancantarsu, in ji shi.
A karshe, ya yi kira ga sabbin wadanda aka dankawa madafun ikon a kan su yi aiki tukuru wajen sadaukarwa gami da kyakkyawan kuduri, kuma ya umurce su da su ji tsoron Allah a lokacin gudanar da aikinsu.
