Shahid Usman Bello Gombe bai riki Harkar nan da wasa ba’
Daga Alh. Lawal K/madaki
Dan uwa Malam Abubakar Darda’u shi ne babban aminin Shahid Usman Bello, wanda ya yi shahada bayan auka wa ’yan uwa na Gombe a masallaci. Tare suka taso tun ba su fahimci Harka ba, har Allah ya fahimtar da su kiran Sayyid Zakzaky suna tare ba su rabu ba.
Ya shaida wa Wakilinmu cewa, da ma shi Shahid yana da zama ne a kauyen Abujaye Kalgo yankin Funakaye Jihar Gombe, sai ya ce wa abokansa shi fa zai koma Bajoga kusa da Malam Muhammad Abbari domin gudanar da harkokinsa na gwagwarmaya. Bayan komawarsa da iyalansa yana nan yana ci gaba da ba da kokari a wannan Harka sai Allah ya yi komawar shi Malam Abbari garin Gombe a matsayin Wakilin ’yan uwa na yankin. To, a nan ma sai Shahid Usman ya ce shi fa in ba ya kusa da Malam Abbari ba ya jin dadin gudanar da harkokinsa na gwagwarmaya, don haka sai ya kwaso iyalansa ya koma Gombe inda ya yi matsaguni a unguwar Tudun Wada Jauro da ke kusa da FCE Gombe, a nan ya kasance da iyalansa.
Malam Abubakar ya tabbatar mana da cewa shi kansa ya taba yin mafarki da Sayyid Zakzaky, inda wani lokaci sai ya ga wani babban kogi koren ciyawa ta lullube shi, sai kuma ga wasu Malamai da rawuna, duk wani Malamin da ya shiga yana zuwa tsakiya sai ya nutse, can sai ya ga Sayyid Zakzaki da farin rawani goshinsa na haske, yana zuwa sai ya ga ya tsallake ba tare da ya nutse ba. Sai ya farka. A nan ya yi godiya ga Allah, sai ya je ya samu Shahid ya fada masa abin da ya gani a mafarki. To, daga ranar suka kara kaimi a wannan Harkar. Shi ne ma dalilin Shahid na kin rabuwa da Malam Abbari. “Mun kasance kullum addu’armu ke nan, Allah ya azurta mu da shahada. Sai ga shi Allah ya karbi addu’ar Shahid Usman Bello. Don haka ni yanzu tashin hankalina shi ne rashin sanin karshena a wannan Harka”.
Malam Abubakar ya tabbatar mana da cewa tabbas su shaida ne, dangane da sadaukarwar Shahid Usman ga wannan Harka, domin kuwa ko a waki’ar farko ta ranar Litinin Shahid yana daga cikin wadanda aka yi masa rauni ta hanyar duka da sara a ka, amma ko da ya koma gida ya yi jinya, ranar Laraba ya sa matarsa ta yi masa tuwon kasa ta daddanna masa jikinsa a inda aka yi masa duka, sai ya yi wanka ya yi Sallar Azahar, da La’asar ya nufi masallaci. A nan Allah ya azurta shi da shahada ta hanyar suka da aka yi masa a daidai wuyansa, kuma shi ne sanadi shahadarsa.
Shi ma kanin Shahid din da suke uwa daya uba daya, Malam Abdullahi Bello, ya tabbatar mana da halayen Shahid din abin koyi ne ga jama’a, domin kuwa su ba su taba jin sa da wasu ba, tun tasowarsa kuma ya kasance mutum ne mai kokarin neman na kansa da tausayin na kasa da shi.
Ita kuwa matarsa Malama Hawwa mun so mu ji daga gare ta, amma abin ya ci tura, domin tana fama da rarrashin ’ya’yanta guda shida da Shahid din ya bari, ciki har da na goye, amma ba abin da ke fita daga bakinta sai dai kawai; “Usman Allah ya ji kanka ya karbi shahadarka, Allah ya albarkaci abin da ka bari.”
Tabbas ’yan uwa da dama sun ba da kyakkyawar shaida dangane da rayuwar Shahid Usman Bello, kuma an ji daga cikin ma’aikatan asibitin Gombe suna cewa su ba su taba ganin irin wannan gawa ba, a ce mutum ya mutu kwana 10, amma kamar yana barci, kuma har yanzu yana zubar jini. Suka ce duk lokacin da aka kawo gawa ta hatsari tana kwana uku za ta fara wari.
Tabbas haka ne, Shahid Usman Bello har aka gama yi masa wanka jini ne ke fita daga inda aka soke shi, sai da aka toshe da auduga amma bai bar fitar da jini ba, kuma dukkanin gabobinsa suna motsawa.
Shahid Usman Bello Gombe da ake wa lakabi da Shahidin Masallaci, ya yi shahada ne a ranar Laraba 2l/l2/20ll sakamakon harin ta’addanci da wasu zauna-gari-banza (’yan Kalare) karkashin jagorancin Ardo Chindo Sarkin Lema, suka kai a masallacin Juma’ar Gombe a lokacin da ’yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Zakzaki (H) ke gudanar da Ta’alimi (karatu) da suka shafe sama da shekaru 20 suna gabatarwa a masallacin.
Shahid Usman Bello ba a sami tabbacin shahadarsa ba sai a ranar Laraba 28/l2/20ll, yayin da labari ya zo na ganin gawarsa a babbar asibitin Gombe, bayan ya shafe kwanaki takwas ba a san inda yake ba. Daga lokacin ne ’yan uwa Musulmi suka fara shirye-shiryen yi masa janaza bayan an sha fama da ’yan sanda kafin su sanya hannu a takarda a ba da gawar. A ranar Juma’a 30/l2/20ll aka dauko gawar Shahid din bayan an gama wanke shi, zuwa babban masallacin Juma’ar Gombe domin yi masa Salla a bainar jama’a domin kowa ya shaidi ta’addancin da aka yi.
’Yan uwa Musulmi daga sassa daban-daban ne suka halarci jana’izar, wadda Wakilin ’yan uwa na Gombe Malam Muhammad Abbari ya jagoranta. Daga nan ne aka shiga sahu domin raka shi makwancinsa. Harisawa ne suka dauki gawar Shahid din tare da faretin girmamawa bayan an yi kwalliya ga gawar Shahidin, dubban ’yan uwa Musulmi ne suka shiga sahun Muzahara cikin izza, domin raka Shahidin. A lokacin rakiyar an rika raba takardu ga al’ummar gari, domin sanar da su hakikanin gaskiyar abin da yake faruwa a masallacin Juma’ar na fadar Gombe. Sannan kuma an sami wasu daidaikun ’yan uwa suna bin duk wani taron jama’a da suka gani domin yi masu karin bayani, wanda hakan ya sanya jama’a da dama suka tausaya tare da yin tofin Allah tsine ga fadar Sarkin Gombe.
An binne shi ne dai a makabartar Tudun Wadan Jauro Abbari da ke unguwar FCE mai tazarar kilomita bakwai daga cikin garin Gombe, kuma an isa makabartar ne cikin sahu, bayan an shafe tafiya ta awanni uku, yara da manya maza da mata. Bayan an sanya shi a makwancinsa ne Malam Muhammad Abbari ya dan tunatar da ’yan uwa matsayin shahada da Shahidi.
Da muke ganawa da ma’aikatan makabartar, dayansu ya shaida mana cewa ya shafe sama da shekaru goma sha bakwai yana wannan aiki, amma wallahi bai taba ganin mutumin da aka rako shi da jama’a haka ba, sai wannan Shahidin. Kuma babu wata jama’a ko kungiya da suka taba yi masu alheri irin wannan, sai ’yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Zakzaky da suka hada masu gudummawa ta sama da Naira dubu 30 nan take.
Tun da farko a tunatarwar da ya yi a masallacin Juma’a, Malam Muhammad Abbari, ya tunatar da jama’a irin rawar da kowa yake takawa a waki’a, inda ya ce gwamnati tana buya a bayan masarautar Gombe, ita kuma masarautar Gombe tana buya a bayan ’yan Kalare domin yin ta’addanci a masallaci; “To gara ma ku fito fili kawai mu gano ku”.
Sannan sai ya ci gaba da cewa; “Duk wani kulle-kulle da mitin-mitin da kuke yi duk mun sani, mun san irin rawar da kowa yake takawa a wannan ta’addancin da aka yi mana. Su kuwa ’yan Kalare duk muna da sunayensu a hannu, inda abin hauka ne, ko kuma a ce mu ma ’yan sara-suka ne kowa mun san inda za mu same shi. To, amma mun bar Allah ne zai yi maganinku”.
Dangane da rade-radin da ake yadawa a gari na cewa wai ’yan uwa suna neman su kwace masallacin, Malam Abbari cewa ya yi; “Wannan batu karya ne, mu almajiran Malam Zakzaky ba mu da matsala da Limaman masallatai, mu muna bin kowa Salla. Mu kwaci masallaci mu kai ina? Ko kuma ana sanya masallaci a aljihu ne? Ko kuwa saidawa za mu yi?”
Da yake magana game da neman ’yan uwa su ware masallacinsu kuwa, Malam Abbari cewa ya yi, “Ware masallaci wannan ba shi ne hadafinmu ba. Mu so ma muke al’ummar Musulmi su dunkule wuri guda ba tare da kafirta wani sashe ba, kuma shi ne hadafin wannan kira na Malam Zakzaky”.
Malam Muhammad Abbari ya ja hankalin jami’an tsaron da ake amfani da su wajen auka wa ’yan uwa; “Ga ku nan ai muna rana muna bautar Allah, kuma kuna rana kuna bautar Shedan, kuma duk wani shiri da kuke yi a kanmu muna da labarin komai domin kuwa ba duka ne suka yarda da abin da ake mana ba”.
Wakilinmu ya gano cewa al’ummar garin Gombe sun fara gano wannan makirci, domin kuwa wani na kusa da fadar Gombe ya tsegunta mana cewa ko a fadar ma wasu ba su goyon bayan abin; “Kawai dai abin ya fi karfinsu ne”
Kuma yanzu haka Wakilanmu sun dukufa wajen bin diddigin wasu bayanai da sunayen wadanda suka taka rawa a waki’ar, ta yadda zai zama in lokaci ya yi za a bayyana su duniya ta san su.
