Yadda zaman sabuwar Majalisar Masar bayan kifar da Mubarak ya gudana
A ranar Litinin 23 ga watan Janairu ne aka bude zaman farko na sabuwar Majalisar dokokin Masar bayan kifar da gwamnatin Husni Mubarak.
Sabanin shekaru 30 da su ka gabata, a wannan karon jam'iyyun masu kishin Musulunci sun sami rinjaye a zaben da aka yi. Jam'iyyar 'yanci da adalci ta kungiyar Ikhwanul-muslimin ta sami kujerun guda 235 na kujerun Majalisa, sai kuma jam'iyyar Nur ta ’yan Salafiyya, wacce ta sami kujeru 123. Sai kuma jam'iyyar Wafd da ta sami kujeru 38.
A lokacin mulkin kama-karya na Husni Mubarak, jam'iyyarsa ce take samun rinjaye a Majalisa duk lokacin da aka yi zabe, abin da ya mai da tsarin tafiyar da mulkin kasar na jam'iyya guda.
Sabuwar Majalisar da ta bude zamanta na farko ta mai da hankali ne wajen rubuta sabon tsarin mulkin kasar.
Adaidai lokacin da ake bude zaman Majalisar, wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar kasar suna neman da sojoji su gaggauta sauka daga kan karagar mulkin kasar.
Shugaban Majalisar koli ta sojojin kasar Masar, Janar Muhammad Husain Tantawy, ya jaddada cewa sojojin kasar za su ci gaba da tafiyar da mulki har zuwa karshen watan Yuli idan an zabi sabon Shugaban kasa.
Bugu da kari matasan da suke adawa da zaman soja a kan karagar mulki, sun gudanar da gangami da kuma zanga-zanga a ranar 25 ga Janairu domin bikin zagayowar shekara guda da juyi. Kuma dubban jama’a sun halarci wajen, inda suka bukaci sojoji su gaggauta sauka daga kan madafun iko.
Sabanin da yake a tsakanin sojoji da kuma masu adawa da sune ya sa manazarta suke yin hasashen cewa za a iya samun tashe-tashen hankula a cikin kasar a nan gaba.
Dalilai biyu ne suke sa sojojin riko da mulki. Na farko shi ne kasantuwar mafi yawancinsu suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Husni Mubarak. Shi ne kuma abin da wasu tsoffin fararen hula da suke damfare da tsohuwar gwamnatin Mubarak suke fadi-tashin ci gaba da dawo da matsayinsu na baya bisa samun kariya daga soja. Sune kuma masu amfani da karfi a kan masu zanga-zangar nuna adawa da gwamantin soja.
Na biyu: Sojojin da suke mulki a kasar suna da cikakken goyon bayan kasashen waje kamar harmatacciyar kasar Isra'ila da kuma Yammacin Turai da Amurka. Sai dai abu ne da yake a fili cewa ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da sojan kasar yana nuni da yadda masu kishin Musulunci da suke cikin sabuwar Majalisar suke da goyon bayan al'umma.
A wani mataki na saukaka irin gabar da ke tsakanin da al’umma, Shugaban Majalisar sojoji wacce take iko a kasar Masar ya ba da sanarwan dage dokar ta-bace wacce aka kafa tun lokacin yakin shekara 1967 da HKI. Dokar mai lamba 162, wacce kuma aka samar da ita a shekara 1958 ta bai wa jami'an tsaro karfin da ba da iyaka. Har ila yau dokara ta yi watsi da hakkokan mutane da dama.
A karkashin dokar dai gwamnatin kasar Masar ta tsare mutane fiye da dubu 17 tun lokacin da aka samar da ita. Sannan akwai wasu dubu 30 da ta tsare kan abin da ya danganci siyasa.
An dage dokar na watannin 18 a shekara 1980, sannan aka sake dawo da ita bayan kisan da aka yi wa Shugaban kasa na lokacin Anwar Sadad.
Field Marshal Husain Tantawi ya bayyana dage dokar, in ban da abin da ya shafi abin da ya kira ’yan banga, a wani jawabin da ya yi a gidan talabijin na kasar.
Tantawi ya ba da wannan sanarwan ne kwana guda bayan da sabuwar Majalisar dokokin kasar ta fara zamanta. Sannan ya zo daidai da cika shekara guda da juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Husni Mubarak.
