Duniyarmu A Yau

’Yan sandan Nijeriya na cin zarafin bil’adama

In ji Human Rights Watch

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta ‘Human Rights Watch’ ta zargi Hukumar ’yan sandan Nijeriya da aikata wasu abubuwa da dama da ke barazana ga sha’anin tabbatar da doka da oda a kasar.

A cikin wani rahoto da ta fitar a Legas, kungiyar mai hedikwata a birnin New York, ta ce cin hanci da rashawa da ya yi wa Hukumar katutu, yakan sa a wasu lokutan, ’yan sanda su tsare mutane wadanda ba su ci ba, ba su sha ba.

Kungiyar ta zargi ’yan sandan da neman kudi a wurin wadanda aka tsare, a yayin da wasu ma akan gana musu azaba, har ma ta kai ga kisa.

Rahoton ya ce ana sanyawa kananan ’yan sanda ka’idar abin da za su kawo a matsayin hancin da suka karba, domin a samar masu da matsayi mai maiko.

Rahoton ya kara da cewa direbobi a shingayen bincike na ’yan sanda, da ’yan kasuwa, da attajirai da wadanda aka kama, suna daga cikin na gaba gaba a wadanda ake bukatar su ba da wani nau’i na hanci.

Kuma akwai ma lokutan da wasu ’yan sandan ke bindige mutanen da suka ki ba da hancin.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki mataki, tare da kaddamar da wani bincike mai zaman kansa domin gano jami’an da ke da laifi da nufin hukuntasu.

A yayin da wannan kungiya ta fito da wannan rahoto, wasu na ganin jama’ar kasa ma na kara yawaitar wannan al’amari tsakanin ’yan sandan, inda sukan yi kokarin bai wa ’yan sanda abin da suke kira, ‘na goro’, da zarar sun shiga cikin wata matsala.

Amma a martanin da ta mayar, rundunar ’yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ba ta ji dadin rahoton da kungiyar kare hakkin bil’adaman ta fitar ba, saboda da ganinsa an tsara shi ne da nufin cimma wata manufa.

Kuma ko kadan bai ba da hoton gaskiyar abin da yake faruwa a tsakanin jami’an ’yan sandan kasar ba.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar, Mista Emmanuel Ojukwu ya shaida wa BBC, an kara wa rahoton gishiri ne don a cimma wata manufa.

“Kuma rahoton yana kunshe wasu zane-zane da dama da aka yi da nufin kafa hujja wadanda kuma suka harzuka mu. Ba gaskiya bane a ce ’yan sanda mahara ne ba masu kare jama’a ba,” in ji Ojukwu.

Ya kara da cewa, “a baya rundanarmu ta janye ’yan sanda da ke kula da wasu, amma haka aka yi ta kokawa lalle sai ’yan sandan su koma. Da mahara ne ai da ba wanda zai so su kusance shi”.

Dangane da zargin almubazzaranci da kungiyar ta yi wa ’yan sandan kuwa, kakakin cewa ya yi: “Mun yarda ce akwai wasu matsaloli tattare da jami’anmu ta fuskar karbar taro da sisi daga hannun jama’a da cin hanci da rashawa da kuma tsare jama’a da yi musu kisan ba gaira babu dalili”, in ji Ojukwu.

’Yan sandan Nijeriya sun fi kowa fuskantar sa-ido a Nijeriya, “saboda akwai bangarori da dama da ke sa-ido a kanmu, wadanda kuma ba mu da ikon taka musu birki a aikinsu”, in ji shi.

Rundunar ’yan sandan dai ta ce da wuya na waje ya fahimci abubuwan da ke hana-ruwa-gudu a aikin ’yan sanda, amma babbar matsalar ita ce yadda aka yi watsi da su a baya, ba sa samun isasshen kudin gudanarwa da sayen kayan aiki da kuma rashin horar da jami’ansu a kan dabarun aiki irin na zamani.


Shafin Farko