Daga Gidan Annabta

WASU NAFILOLIN RAMADAN


Allamah Majalisi (RA) ya ce, ana son yin nafiloli da dare kamar haka: DAREN HUDU: Raka’a takwas, kowacce Fatiha da Inna Anzalnahu ashirin. DAREN BIYAR: Raka’a biyu, kowacce Fatiha da Tauhid hamsin. Bayan salla salatin Annabi dari. DAREN SHIDA: Raka’a hudu, kowacce Fatiha da Tabaraka. DAREN BAKWAI: Raka’a hudu, kowacce Fatiha da Inna Anzalnahu 13. DAREN TAKWAS: Raka’a biyu, kowacce Fatiha da Tauhid 10. Bayan salla a karanta Subhanallah sau dubu. DAREN TARA: Raka’a shida tsakanin magriba da isha, kowacce Fatiha da Ayatul Kursiy bakwai. Bayan salla kuma a yi salatin Annabi sau hamsin. DAREN GOMA: Raka’a 20, kowacce Fatiha da Tauhid 30. DAREN 11: Raka’a biyu, kowacce Fatiha da Inna A’adainaka 20. Muna barar addu’a kan manufofinmu na alheri da neman Allah ya karya mana azzalumai.

Karin bayani a duba Mafatiyhul Jinan.


Shafin Farko