Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Tambihi

Arba’in din Imam Husain (AS)


Tare da Daga Muhammad Sulaiman 08029493717

Ranar Arba’in din Imam Husain (AS) rana ce wadda take da muhimmanci, musamman ga mabiya Ahlul Baiti (AS). Kuma kiyaye ranar yana daga cikin alamomin Mumini, kamar yadda haka ya zo daga Imam Hasan Al’askari (AS), inda ya ce; “Alamomin Mumini (wato dan Shi’a) guda biyar ne. 1. Yin Salla raka’a 51 ko wace rana, 2. Ziyarar Arba’in. 3. Sa zobe a dama. 4. Sa goshi a kasa (ta’afir). 5. Bayyana karatun Bismillah a Salla”.

Amma kafin bayani dangane da wannan Hadisi da kuma ranar Arba’in din, zai yi kyau mu dan yi bayani a takaice dangane da matsayin adadin Arba’in a addinin Musulunci. Adadin 40 yana da wani ‘asrar gaibiyyah’ a wajen Allah (T) da kuma Tarkizi na musamman a wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma, da kuma wasu Hadisai da aka samo daga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Bait (AS). Ga misalin wasu daga cikin wadannan Hadisai. An samo daga Imam Sadik (AS) ya ce; “Idan Mumini ya rasu, mutane 40 daga Muminai suka halarci jana’izarsa, (cikin addu’ar da suka yi masa) suka ce ‘Ya Ubangiji! Ba mu san komai ba dangane da shi face alheri. Kai ka fi mu sanin sa’, Allah (T) zai ce na zartar da shaidarku, na gafarta masa na abin da na sani, da wanda ba ku sani ba”.

Haka nan kuma daga Imam Sadik (AS) ya ce; “Babu wasu jama’a su 40 da za su hadu su yi addu’a a kan wata bukata tasu face Allah (T) ya karba masu”. Har ila yau daga Imam Sadik (AS) ya ce; “Duk wanda ya gabatar da Muminai 40 gabanin addu’arsa, bayan haka ya gabatar da addu’a na bukatarsa, to Allah (T) zai karba masa.” Kuma wannan wani abu ne wanda yake da gayar muhimmanci da falala, na kowannenmu ya saba wa kansa da yin haka, wato na addu’o’i ga Muminai guda Arba’in, in so samu ne a kowane dare a kunut na Witri, ko kuma bayan ya gama Sallar Tahajjud dinsa, in ba zai iya yi kowane dare ba, to akalla duk daren Juma’a mutum ya lizimci hakan. Domin yin hakan yana da fa’idodi masu yawan gaske, kuma sunna ce daga cikin sunnonin Ma’asumai (AS). Alal misali ya zo a kan cewa Sayyida Fatima (AS) in ta gama Sallar Tahajjud dinta takan yi addu’o’i ga Muminai na kusa da na nesa, shi ne har Imam Hasan (AS) yake ce mata, “Nakan ji kikan yi addu’o’i ga mutane, amma ban ji kina addu’a gare ki ba”. Shi ne ta ce masa; “Makwabci gabanin gida”.

Haka nan kuma akwai Hadisi da aka samo daga Manzon Allah (S) ya ce; “Duk wanda ya kiyaye wa al’ummata Hadisai 40 da suka shafi al’amarin addininsu, ba ya nufin komai face neman yardar Allah (T) da kuma gidan lahira, to Allah zai tashe shi ranar kiyama a matsayin Fakihi kuma Malami”. Wannan Hadisin ya sa da yawa daga cikin Malaman Madrasah din Ahlul Bait (AS) da kuma ta Ahlus Sunnah suka rubuta littafai na Hadisai 40, domin samun falalar wannan Hadisi. Misali a nan shi ne littafin Hadisi 40 na Imam Khumain da kuma littafin Hadisi 40 na Imam Nawawi. In mutum ya duba littafin Hadisi 40 na Imam Khumaini zai ga cewa a wajen gabatarwa na littafin yana cewa ya tattara wadannan Hadisai ne da fatan ya samu shiga cikin Hadisin Manzon Allah (S) da ya zo a kan cewa; “Wanda ya kiyaye wa al’ummata Hadisai 40 da suke amfana da su, to Allah zai tada shi ranar alkiyama a matsayin Fakihi kuma Malami”. Da dai Hadisai da dama da suka zo a kan Tarkizi kan 40, wanda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.

Dawowa ga wannan Hadisi da aka samo daga Imam Askari (AS) na alamomin Mumini guda biyar; alama ta farko, kamar yadda ya zo a Hadisin yin Raka’a 51 kowace rana. Wannan raka’a 51 ya hada da sallolin wajibi da nafilfilinsu da kuma Sallar Tahajjud tare da Shafa’i da Witri. A warware ga lissafin adadin raka’o’in na Sallolin wajibai, wato daga Sallar Asuba zuwa Sallar Isha’i in mutum ya hada zai ga 17 ne, sai nafilfilinsu raka’a 2 gabanin Asuba, raka’a 8 gabanin Sallar Zuhur, raka’a 8 gabanin Sallar Asar, raka’a 4 bayan Sallar Magrib, raka’a 2 a zaune bayan Isha’i (watira), amma biyun nan yana makwafin raka’a 1 ne, Sallar Tahajjud raka’a 8, shafa’i 2 Witri 1, in mutum ya hada zai ga lissafin ya tashi 34, wato na raka’o’i na nafilfilin, in mutum ya hada da wadancan raka’o’i na wajibi 17 zai ga ya tashi a kan 51.

To, wadannan raka’o’i 51 sune ake so kowane Mumini, wato mabiyin Ahlul Baiti (AS) ya tsayu da yin su kowace rana ba tare da yin fashi ba. Ko da za ta kai a ce mutum bai samu yin su nafilfilin ba saboda wani uzuri, to ya zo a kan cewa ana son mutum ya rama su. Misali a ce bai samu yin nafilfilin Sallar Zuhur da Asar ba, yana iya ramka su a cikin yini din, ko kuma da daddare. In kuma bai samu yin nafilfilin dare ba, wato kamar nafilar Magrib, Isha’i, ko kuma Tahajjud dinsa, to yana iya ramka su a daren, ko kuma kashe garin a ciki yini. Wato dai ya tsayu a kan yin haka kowace rana ba tare da fashi ba. A inda kawai wadannan nafilfili suke faduwa shi ne a halin tafiya. A nan nafilfili na Sallar Zuhur da Asar sun fadi, amma sauran nafilfilin na Sallar Magrib da Isha’i da Asuba, da kuma Tahajjud, Shafa’i da Witri, su ba su fadi ba, kuma wadannan raka’o’i 51 mutum ya kwatanta su da raka’a dubu daya da Imam Ali (AS), Imam Husain (AS) Imam Zainul Abidin (AS) da kuma Imam Ridah (AS) suke yi kowace rana zai ga daya bisa 20 ne. Kuma su wadannan raka’o’i 51, su ake ce wa Salloli na yaumiyyah. Akwai kuma Salloli na Usbu’iyyah, wato na mako, su ma an ruwaito su ne daga Manzon Allah (S) da kuma A’imma na Ahlul Baiti (AS), wato wadannan kwanaki bakwai na mako. Misali daga Jumma’a zuwa Asabar to kowace rana da kuma dare na wadannan kwanaki na da nata Sallolin. Littattafai da dama sun kawo wadannan Sallolin, misali littafin Diya’us Salihin. Ga wanda bai da wannan littafi ko kuma littafan da suka kawo wadannan Salloli, to ga yadda Sallolin na mako din suke.

Daren Juma’a raka’a 2, kowace raka’a mutum zai karanta Kulhuwallahu 70. Wannan an samo daga Manzon Allah ne. Sai kuma ranar Juma’a raka’a 8, kowace raka’a Kulhuwallahu 1. Daren Asabar raka’a 4, kowace raka’a bayan Fatiha, sai Kulhuwallahu bakwai. Sai kuma ranar Asabar raka’a 4, kowace raka’a bayan Fatiha, Kulya Ayyuhal Kafirun sau uku bayan sallama ta raka’a 4, sai mutum ya karanta Ayyatul Kursiyu sau daya. Sai daren Lahadi raka’a 6, kowace raka’a bayan Fatiha, Kulhuwallahu sau bakwai. Sai ranar Lahadi raka’a 2, raka’a ta farko bayan Fatiha, Inna A’adaina sau uku. Raka’a ta biyu bayan Fatiha, Kulhuwallahu sau uku. Sai daren Litinin raka’a 2, kowace raka’a bayan Fatiha, Ayatul Kursiyu, Kulhuwallahu, sai Suratul Falaki da Naasi, dukkansu sau daya. Bayan sallama sai Istigfari sau 10. Sai ranar Litinin raka’a 4, raka’a’a ta farko bayan Fatiha Ayatul Kursiyu daya. Raka’a ta biyu bayan Fatiha, Kulhuwallahu daya. Raka’a ta uku bayan Fatiha, Suratul Falaki. Raka’a ta hudu bayan Fatiha Suratul Nasi. Daren Talata raka’a 2, raka’a ta farko bayan Fatiha, Inna Anzalnahu sau daya. Raka’a ta biyu bayan Fatiha, Kulhuwallahu bakwai.

Ranar Talata raka’a 2, kowace raka’a bayan Fatiha, Wattini, Kulhuwallah, Falaki da Nasi dukkan su sau daya. Daren Laraba raka’a 2, bayan Fatiha, kowace raka’a Ayyatul Kursiyu, Inna Anzalnahu, Izaja’a sau dai-dai, sai kuma Kulhuwallah sau uku. Ranar Laraba raka’a 2, kowace raka’a bayan Fatiha, Iza-zul sau daya, sai kuma Kulhuwallah sau uku. Daren Alhamis raka’a 6, kowace raka’a bayan Fatiha Kulya Ayyuhal Kafirun sau daya, sai Kulhuwallah sau uku. Bayan sallamewa duka, wato raka’a 6 din, sai mutum ya karanta Ayyatul Kursiyu sau uku. Sai ranar Alhamis raka’a 2, bayan Fatiha kowace raka’a Iza-ja’a da kuma Inna A’adaina kowace sau biyar.

To, irin wadannan Salloli su ake ce wa Sallolin Usbu’iyyah, wato na mako. In mutum ya duba cikin littafin Jamalul-Usbu’i na Sayyid Ibn Dawus da kuma littafin Mir’atul kamel, zai ga duk sun kawo su. Su ma wannan yana da kyau kowannenmu ya tsayu da su, wato baya ga wancan raka’a 51 na Yaumiyyah.

Sai kuma Sallah ta Shahariyyah, wato ta wata; ita kuma yadda take shi ne; idan ka yi ta a daren farko na kowane wata, sai kuma wani sabon wata a daren farko. Haka nan in ka yi a ranar farko na wata, sai kuma wani wata a ranar farko. Shi ne ake ce mata Shahariyya. Mutum na iya duba Sallolin a littafi Mafatihul Jinan babi na biyu fasali na 11. Ga wanda bai da Imkaniyyar dubawa ga yadda Sallolin suke. Daren farko na kowane wata raka’a 2, kowace raka’a bayan Fatiha, sai ya karanta Suratul An’am, idan mutum bai haddace ba yana iya amfani da Alkur’ani domin karanta Suratul An’am din. Sai kuma ranar farko ta kowane wata, shi ma raka’a 2, raka’ar farko bayan Fatiha, Kulhuwallah 30, sai raka’a ta biyu bayan Fatiha, Inna-Anzalnahu 30. Su ma wadannan Salloli an samo ne daga A’imma na Ahlul Bait (AS), su ma wadannan salloli na wata-wata ana son mutum ya tsayu da su, wato kowane wata daren farkonsa da kuma ranar farkonsa ya zamto mutum na yi ba tare da fashi ba, sai in da wani uzuri.

Sai kuma Salloli na Sanawiyya, wato shekara-shekara, su kuma yadda suke, in ka yi su misali yau, to sai kuma wata shekara za ka sake yin su. Irin wadannan Salloli sun zo ne jefi-jefi a cikin kwanuka na shekara, wato ba kullum ake yin su ba. Misalan irin wadannan Salloli na Sanawiyya su ne kamar Sallar ranar karshe ta shekara, ko kuma Sallar daren Ashura, to ire-iren wadannan Salloli su ne ake ce wa Salloli na shekara. Misali Sallolin da suka zo na daren Ashura, yanzu mutum ba zai sake yin su ba, sai kuma shekara mai zuwa in Allah (T) ya kai mu wani daren Ashurar na shekara mai zuwa. Yanzu Sallah ta Sanawiyya da ke gabanmu ita ce ta 17 ga watan Rabi’ul Awwal, wato ranar Maulidin Manzon Allah (S), in mutum ya duba Mafatihu zai ga Sallah din, kuma wadannan watanni 12 na Musulunci, in mutum ya bi su daya bayan daya zai ga babu wani wata, wanda babu Sallar Sanawiyya a cikinsa. Shi ma wannan, wato Sallah na shekara-shekara yana da kyau kowanenmu ya tsayu da su.

Saboda haka in muka duba a wannan nizami, za mu ga akwai Salloli na Yaumiyya, Usbu’iyyah, Shahariyya, da kuma Sanawiyya, kuma duk wadannan Salloli an ruwaito su ne daga Ma’asumin (AS). Saboda haka yana da muhimmancin yin wadannan Salloli domin koyi da su. Kuma kamar yadda muka ga wannan nizami guda hudu na Salloli, to haka nan ma addu’o’i su ma suna da shigen wannan nizami guda hudu, wato akwai addu’o’i na Yaumiyya, Usbu’iyyah, Shahariyya da kuma Sanawiyyah. Haka nan shi ma Azumi yana da wannan nizamin guda hudu. Haka nan surori na Alkur’ani, su ma suna da wannan nizami guda hudu, wato akwai surorin da ake son karantawa Yaumiyya, akwai Usbu’iyya, Shahariyya da kuma surori na Sanawiyya. Insha Allah dukkan su za a yi bayanin su a muhallinsu.

Wannan shi ne bayani a takaice dangane da alamar Mumini na farko. Sai kuma alama ta biyu kamar yadda ya zo a Hadisin, wato Ziyarar Arba’in din Imam Husain (AS) a 20 ga watan Safar, wato kwanaki 40 bayan Shahadarsa (AS), yana daga cikin alamomin Mumini wato Mabiyin Ahlul Baiti (AS). Kuma ita wannan ziyarar imma ta kasance daga kusa ne ko daga nesa, wato in mutum yana da iko da kuma damar zuwa Karbala domin ziyarar ko kuma yin ziyarar daga garin da yake. A kan wannan asasin ne za mu ga mabiya Ahlul Baiti (AS) daga sassan duniya daban-daban da suke da imkaniyyar zuwa Karbala, musamman ma wadanda suke cikin kasar Iraki, suke tururuwan zuwa Karbala domin wannan ziyarar ta Arba’in, wanda mutum zai iya dukan kirji a wannan zamanin namu ya ce babu wani taro da yake tara mutane a doron kasa, kamar wannan ziyarar ta Arba’in a Karbala.

Ta yiwu mutum ya yi tunanin taron aikin Hajji. To, duk shekara taron bai kai wa miliyan biyar, galibi miliyan biyu ne zuwa uku. To, amma mu duba taron jama’a na ziyarar Arba’in din Imam Husain (AS) a Karbala na shekarun bayan baya nan da suka wuce a kan samu jama’a sama da miliyan 15, kuma kowace shekara adadin karuwa yake yi. Wannan aya ce babba ga masu tunani. Kuma wani abin lura shi ne wasu da ke nan cikin kasar Iraki sukan tako ne da kafa daga garuruwansu, har ya zuwa Karbala domin wannan ziyarar. Za ka gan su maza da mata yara da manya da ma dattijai. Kuma a irin wadannan hanyoyi na zuwa Karbala za ka ga akwai bayin Allah (T) daban-daban da suke gabatar da hidima ta fuskoki daban-daban ga wadannan matafiyan zuwa Karbala, kuma dukkan wadannan hidimomin kyauta suke gabatar da su. Akwai masu ba da abinci a hanyoyin, akwai masu ba da masaukai. Misali mutum yawo tafiya kwanaki daya daga garin su, yana so ya huta kafin ya ci gaba da tafiya, to, ga masauki Fisabilillah. Akwai Likitoci, ga masu gyaran takalma, ga masu hanyoyi na sadarwa, wato tarho shi ma duk kyauta ga wadannan matafiya zuwa Karbala da dai abubuwa da yawa da ba a ambata ba na hidimomi da wasu bayin Allah ke gabatarwa Fisabillahi.

Ita ziyarar Imam Husain (AS) ta kasu kashi biyu, akwai ziyara Mudlaka, wato ita ce ziyara wadda ba ta kebanta da wani zamani ayyananne ba. Akwai kuma ziyara Maksusa, wato ta kebanta da wani zamani ayyananne. To, Ziyarar Arba’in tana daga cikin ziyara Maksusa. A wata ma’ana ziyara Maksusa ana ce mata ziyara Sanawiyya, wato ta shekara-shekara. Domin idan ka yi ta sai kuma wata shekara. Misali wannan ziyara ta Arba’in, ziyarar Imam Husain (AS) Maksusa, kuma Sanawiyya guda 10 ne sune: 1. Ziyarar Ashura, wato 10 ga Muharram. 2. Ziyarar Arba’in, wato 20 ga watan Safar. 3. Ziyarar ranar farko ta watan Rajab. 4. Ziyarar 15 ga watan Rajab. 5. Ziyarar 3 ga watan Sha’aban, wato ranar haihuwar Imam Husain (AS). 6. Ziyarar daren 15 ga watan Sha’aban. 7. Ziyarar daren Lailatul Kadr 19, 21, 23 na watan Ramadan. 8. Ziyarar daren Idi karama da kuma babbar Sallah. 9. Ziyarar ranakun Idin karama da babbar Sallah. 10. Ziyarar ranar Arfa, wato 9 ga Zulhijja. To, dukkan wadannan kwanaki da aka ambata mustahabbi ne mutum ya ziyarci Imam Husain (AS) a cikinsu daga kusa ko nesa.

Baya ga wannan ziyarar ta Sanawiyya ta Imam Husain (AS), akwai kuma ziyarar Usbu’iyya tasa, wato ta mako, shi ne ranar Litinin. Ga mai bukatar ganin wannan ziyara da ma sauran ziyarori na Manzon Allah (S) da kuma A’imma na Ahlul Baiti (AS) na mako wato na kowace rana daga cikin mako ya duba littafin Mafatihul Jinan babi na daya fasali na biyar. Baya ga wadannan mustahabbi ne yin ziyara a ranakun wilada da kuma wafati na Ma’asumin (AS), wato Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS), musamman ma ranaku na wafatinsu. Wato yana da kyau mutum ya sunnanta wa kansa wannan sunna din, ya kasance duk ranar wilada ko wafati na daya daga cikin Ma’asumai mutum ya kasance ya ziyarce shi ziyara ta kusa ko ta nesa. Domin yin haka yana daya daga cikin hanyoyin kyautata alaka da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) da kuma damfaruwa da su kalbiyyan, wato a zuci. A takaice dai kiyaye wadannan ranaku na wilada da wafati na Ma’asumin (AS) a matsayi na dai-daiku da kuma jam’i, yana da gayar muhimmanci.

Ga wata da kuma ranar wafatin kowanne daga cikin Ma’asumin (AS) 1. Manzon Allah (S) 28 ga watan Safar. 2. Sayyidah Fatima (AS) 3 ga watan Jimada-Sani. 3. Imam Ali (AS) 21 ga watan Ramadan. 4. Imam Hasan (AS) 7 ko 28 (a wata ruwayar) ga watan Safar. 5. Imam Husain (AS) 10 ga watan Muharram. 6. Imam Zainul-Abidin (AS) 25 (a wata ruwaya) 12 ga watan Muharram. 7. Imam Bakir (AS) 7 ga watan Zulhijja. 8. Imam Sadik (AS) 25 ga watan Shawwal. 9. Imam Kazim (AS) 25 ga watan Rajab. 10. Imam Ridha (AS) 23 ga watan Zulkidah (a wata ruwaya) a watan Safar. 11. Imam Jawad (AS) karshen watan Zulkida. 12. Imam Hadi (AS) 3 ga watan Rajab. 13. Iman Askari (AS) 8 ga watan Rabi’ul Awwal. Wadannan su ne ranaku na wafatinsu, wato rasuwarsu.

Sai kuma na wiladarsu, wato haihuwarsu kamar haka: 1. Manzon Allah (S) 17 ga Rabi’ul Awwal. 2. Sayyidah Fatima(AS) 20 ga watan Jimada Sani 3. Imam Ali (AS) 13 ga watan Rajab. 4. Imam Hasan (AS) 15 ga watan Ramadan. 5. Imam Husain (AS) 3 ga watan Sha’aban. 6. Imam Zainul-Abidin (AS) 5 ga watan Sha’aban. 7. Imam Bakir (AS) 1 ga watan Rajab (a wata ruwaya 3 ga watan Safar). 8. Imam Sadik (AS) 17 ga watan Rabi’ul Awwal. 9. Imam Kazim (AS) 7 ga watan Safar. 10. Imam Ridah (AS) 11 ga watan Zulkidah. 11. Imam Jawad 10 ga watan Rajab. 12. Imam Hadi (AS) 2 ga watan Rajab. 13. Imam Askari (AS) 10 ga watan Rabi’us-Sani. 14. Imam Mahdi (AS) 15 ga watan Sha’aban.

Haka nan baya ga ziyara a wadannan kwananki na wafati ko wilada na kowannensu, akwai yin juyayi in na wafati ne, da kuma yin murna in na wilada ne, da kuma mika ta’aziyya ga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) in na wafatin Ma’asum ne, in kuma na wiladar Ma’asum ne wannan mika murnarsa ga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Baiti (AS) duk sai bayan mutum ya yi masu sallama.

Insha Allah sauran alamomin Mu’umin sai wata munasabar za a dora.

Zalunci da ta’addancin da aka yi a Karbala

Daga Haruna Shelleng

“Shin akwai mai taimakon da zai taimake mu?” in ji Imam Husain (AS) a falalin hamadar Karbala. Babu gida gaba da bayansu, kuma babu mai taimakon da zai taimake su. Mun amsa kiranka ya Imam! Labbaika Ya Husaini (AS)!!

Zaman Makokin da ake yi tun kamawar watan Muharram a duk duniya, kuma jama’ar da ba za su lissafu ba suka yi dandazo a Hubbarenka a Karbala, da Muzaharorin da aka yi Ranar Ashura, wanda miliyoyin jama’a suka fito suna kuka da juyayi a kan abin da ya samu Imam Husaini da sauran Ahlu Baitin Annabi (SAWA), gami da irin miliyoyin jama’ar da za su fito a ranar Arba’un dinsa, ya gaskata, ya kuma nuna hakika Imam Husaini (AS) ya raya wannan addinin da jininsa, an kuma amsa kiran sa. Mun kuma yi bara’a daga makasanka gaba dayansu, ba mu ba su duniya da lahira. Muna kuma fatan Allah ya sanya mu a cikin masu daukar fansar kisan sa a karkashin dansa, Imam Mahdi (AF). Muna fatan Allah ya sanya mu cikin rundunarsa. Kuma wannan ya nuna a fili ga azzalumai cewa: ‘Kisa bai taba kaiwa ga nasara ba’, domin makasa Imam Husain (AS) ba su yi nasara ba.

Imam Husaini (AS) ya ce: “Ba na fita ne don shisshigi da dagawa ba, amma na fito ne don na kawo gyara a addinin Kakana. Kuma idan har addini ba zai tabbata ba sai da raina (an kashe ni), to ya masu da takubba ku rike ni (ku kama ni).” Wannan shi ne dalilin fitowar Imam Husaini (AS), kamar yadda ya fada a wasiyyar da ya bar wa dan uwansa Muhammad Ibn Hanafiyyah da Bani Hashim. Ya ce masu duk wanda ya bi shi zai yi shahada, wanda kuma bai bi shi ba, ba zai yi nasara ba. Daga wannan magana za mu fahimci cewa, Shahada ita ce nasara. Duk abin da wani zai fada sabanin haka, ko wanene shi a matsayin dalilin fitar Imam, kire ne da karya. Ko waye shi kuwa, komai girmansa kuwa. Domin shi Imam (AS) ya zayyana dalilin fitarsa a wasiyyarsa.

Imam (AS) ya fito don kwato wannan addini daga jahiliyyar da ake so a mai da shi. Hakika kafin halakar Mu’awiyyah, ya nada dansa Yazidu (LA) a matsayin Magajinsa, shi kuma Yazidu bai san addini ba, da ma uwarsa Kirista ce, kuma ya girma ne a dangin nono. Banda shan giya da wasa da kare da biri, babu abin da ya sani. Saboda haka, an jarabci wannan al’umma da makiyayi irin Yazidu dan Mu’awiyyah.

Shi dai Yazidu ya umurci Gwamnansa na Madina da ya karbi mubaya’ar Imam Husaini (AS) a madadinsa. Hakan bai yiwu ba. Imam ya fita zuwa Makka don Hajji, sai Yazidu ya tura sojoji da umurnin cewa ko da labulen Ka’aba Imam Husaini (AS) ya lulluba da shi, su kashe shi. Sai Imam ya ga bai son a keta hurumin Makka da jini, sai ya fita ranar Tarwiyya tare da Iyalan gidansa da Sahabbansa.

Kafin nan dan uwan Imam Husaini (AS), Muhammad Ibn Hanafiyyah shi ma dan Imam Aliy (AS) ne, amma ba dan Sayyida Fatimah (AS) ba ne, ya yi iya kokarinsa ya hana Imam Husaini (AS) fita. Sai Imam ya ce masa, “jiya na yi mafarki da Manzon Allah (SAWA), ya ce mani, Allah ya ga dama ya gan ka an kashe ka.” Sai Ibn Hanafiyyah ya yi kuka, sai ya ce; “Babu makawa. To, mata da yara fa ka bar su a gida mana”. Sai Imam Husaini (AS) ya ce; “Har ila yau Manzon Allah (SAWA) ya ce, Allah ya ga dama a gan su ribatattun yaki”. Ya sake yin kuka. Ba wata sauran shawara ke nan. Sai Imam ya ba shi wasiyyarsa a rubuce. Ga abin da ya ce wa Bani Hashim: “Duk wanda ya biyo ni zai yi shahada, wanda kuma bai bi ni ba, ba zai yi nasara ba.”

Za mu fahimta a fili a wasiyyar Imam Husaini (AS) cewa, bin sa shi ne nasara, duk da ko shahada za su yi, ashe shahada nasara ce. Shi kansa Imam ya fadi cewa, zai yi nasara a fitarsa duk da ko ya san cewa za a kashe shi ne. Daga nan za mu fahimci cewa, akwai nasara a cikin shahada ke nan. Kuma yanzu a zahiri za mu iya fahimtar abin da Imam (AS) ke nufi na cewa zai yi nasara, kuma wanda bai bi shi ba, ba zai yi nasara ba.

A bana kuwa 1433, wadanda suka je Karbala tunawa da shahadar Imam (AS) sun kai miliyan 36, ban da sauran kasashe kamar Iran, Lebanon, Turkiyya, Afganistan, Pakistan, Indiya, Amurka da Turai, kai har Nijeriya, Kenya, dss. Duk duniya ana tunawa da wannan sadaukar da kai da Imam Husaini (AS) ya yi a falalin Hamada, babu kowa tare da shi, fiye da shekaru dubu da dari uku da tamanin da daya.

A kullum sai an tuna da shi da Sahabbansa managarta duk lokacin da aka ziyarci Imam Husaini (AS) a Karbala. Ga ambatonsa ya dawwama, balle a ce ma ranar shahadarsa ta kewayo. A wasu wurare tun daga farkon watan Muharram ma har zuwa kusan karshen watan Safar, ana Juyayin shahadar Imam (AS) a Karbala. Kai wasu shekara cur ma shi ake yi, kamar tashar satilayit ta ANWAR, kullum cikin Juyayin Ashura suke.

Wannan ya nuna akwai sako a cikin jini. Jini bai taba zuba haka kawai ba, na ma kowa ke nan ba, balle na Jikan Annabi (AS). Jini ya yi galaba a kan takobi. Kuma maganar da ake cewa da jinin Shahidai itacen Musulunci ke habaka, mun gan shi aikace. Domin sanadiyyar shahadar Imam Husaini (AS), ya kwato wannan addini daga hannun azzalumai, fajirai, makiya Allah da Manzonsa da addininsa. Ga shi nan ‘practically’ muna gani a zahiri. Wannan kuma ya sake nuna mana zancen Allah da ya ce: “Kada mu zaci cewa wadanda suka mutu a tafarkinsa matattu ne, a’a rayayyu ne, Allah na azurta su.” A wani wurin ma cewa ya yi, kada mu ce su matattu ne, su rayayyu ne.

A fili za mu iya fahimtar wannan abin da ya faru a Karbala da Imam Husaini (AS), tunda abin ya faru babu wata rana cikin raneku wadda ba a tuna da Imam (AS) ba da abin da ya faru da shi. Duk abin da ake tunawa da shi kullum kuwa, ai rayyaye ne ba yadda za a yi a manta da shi. Su masu aika-aikar fa, su Yazidu, Umar Bin Sa’ad, Shimru, dan Ziyad, dss? Kullum sai an tsine masu, tarihi ya ambace su a munanan kama. Yau suna ina? Wa ke ziyarar su? Wa ke tunawa da su? Sai dai tsinanne.

Wannan ya nuna labudda mutum ya yi abin kirki a rayuwarsa, saboda shi ne kawai zai amfane shi duniya da lahira. Kuma lallai azzalumai ba su nasara, kamar yadda Allah ya fada, ba su yi ba, kuma ba za su yi ba nan gaba.

Tun bayan nada Yazidu da babansa ya yi, mutanen Kufa suka dinga rubuta wa Imam Husaini (AS) wasiku cewa, ya zo gare su a Kufa ko Allah ya tattara al’amuransu a karkashinsa. Da wasiku suka yi yawa suka kai dubbai, sai ya tura dan uwansa Muslim Bin Akil, ya je can Kufa ya ga shin da gaske suke, sai ya aiko wa Imam sako. Shi Muslim Bin Akil, dan sakon Imam Husaini (AS) ga mutanen Kufa, ko da ya je Kufa jama’a sun taru bayansa. Shi ke masu Salla, sun mika lamarinsu gare shi a madadin Imam Husaini (AS). Ganin yadda suka karbe shi, sai ya aika wa Imam Husaini (AS) cewa yana iya karasowa zuwa Kufa.

Shi Yazidu (LA) sai ya nada Dan Ziyad a matsayin Gwamnan Kufa ya hada masa Kufa da Basra, da ma kuma dan Mamansa ne, shi ya yi ba-sani-ba-sabo da karin runduna mai yawa, da umurnin kada a bar Imam Husaini (AS) ya iso Kufa. Isowar Ibn Ziyad Kufa al’amura suka canza, mutane suka juya wa Muslim Bin Akil baya, saboda tsoron sharri da makircinsa da muguntansa.

Shi kansa Muslim Ibn Akil ya shiga damuwa ganin cewa, ya riga ya aika wa Imam Husaini (AS) cewa, yana iya karasowa ga kuma al’amura sun canza. Shi kansa Muslim Bin Akil da ’ya’yansa guda biyu ya sa a kashe su, aka kuma sa farashi a kansa duk wanda ya kawo bayanin inda yake za a ba shi kudi masu yawa. An wayi gari bai da inda za shi a garin Kufa, sai gidan wata tsohuwa da ta gan shi ta ce; “Ya kai bawan Allah! Ba za ka je gidanka ba, iyalinka su gan ka ga dare ya yi?”. Ya ce ai bai da iyali, bai da gida. Daga nan kuma har dai ta fahimci cewa shi ne dan sakon Imam Husaini (Muslim Bin Akil), sannan ta gayyace shi gidanta. Danta yana dawowa dama shi dan sanda ne, da ya fahimci cewa Muslim Bin Akil ne a gidansu, duk da mahaifiyarsa ta roke shi da kada ya fada, amma ina! Sai da ya fada. Ya je ya fada, aka hada shi da rundunar soja. Da ma Muslim Bin Akil yana Sallar dare yana jin kofatun dawakai, ya san abin da ke faruwa. Sai ya sallame Sallar ya dauko takobinsa suka fafata, ya kashe na kashewa, saura suka gudu.

Fada ta zarge su da cewa, yaya aka yi ba su iya kamo shi ba shi kadai su da yawa? Suka ce, ba ku san cewa shi Jinin Hashimawa ne tare da shi ba? Aka turo ‘reinforcement’, sannan fa suka iya masa. Shi ma sai da suka harbe shi da wuta daga soron gini tukunna suka ba shi amana, a karshe Ibn Ziyad ya sa aka kashe shi.

A bangare guda kuma, Ibn Ziyad bisa umurnin mai gidansa Yazidu, sun tura runduna akalla dubu 65, a wata ruwaya ma su dubu 80 ne, su rutsa da Imam Husaini (AS) karkashin Umar Dan Sa’ad a wurin da ake kira Karbala – Karbun wa bala. Kafin nan da ma an turo Hurr da wasu runduna shi ma da umurnin cewa ya tsare Imam, kada ya bar shi ya yi gaba ko baya, ya tsare shi a nan. Shi Imam Husaini (AS) shi da Sahabbansa 72 sai mata da yara. Amma kuma dubi rundunar sojojin da aka tura su yake su.

Suka tsare Imam Husaini (AS) a wannan wurin, suka hana su gaba ko baya, babu kuma ruwan sha balle abinci tsawon kwanaki. Jarirai da yara suna tsananin jin kishi, amma ina! An hana su ruwa su sha. Har dan Imam Husaini (AS) Abdullahi dan yaro mai shan nono ya bukaci ruwa don tsananin kishi har fitar da harshensa yake yi, sai Imam Husaini (AS) ya ce: “Idan ni na yi maku laifi, to wannan jaririn fa laifin me ya yi muku? Ku ba shi ruwa ya sha. Idan kuna bukatar in ba ku shi ku je ku ba shi ruwa ku dawo mani da shi, idan kuna ji tsoro kada ku ba da ruwa ni in ma sha.”

A nan sai aka rabu kashi biyu, wasu suna cewa a ba da ruwa, wasu na cewa ba za a ba da ba. Da ma yaron na hannun Imam Husaini (AS), nan sai Umur Dan Sa’ad ya ce wa Harmala (wani tsinanne) ya raba gardama. Da ma gwanin kibiya ne, sai kawai ya harbe yaron a makogoronsa. Sai Imam Husaini (AS) ya tattara shi a bayansa ya dawo tantinsa. Sai mahaifiyar yaron ta ce ya samu ruwan kuwa ya sha? Sai Imam ya ce ina! Sun shayar da shi ruwan kibiyi ne. Imam ya tattara jinin dan nasa ya watsa sama ya ce, “Ya Allah ka karbi wannan sadaukarwar daga gare ni.” Jinin bai fado kasa ba.

Tun da farko sai da Imam Husaini (AS) ya tambaye su, ko akwai wani abu da ya yi masu ne? Suka ce babu. Ya ce masu; “Ko kun san ni waye? Ni ne Husaini (AS) Dan ’Yar Manzon Allah (SAWA), yanzu haka a doron kasa babu wani Dan ’Yar Manzon Allah in ba ni ba”. Suka ce sun sani. Ya kara ce masu; “Kun san wannan rawanin da ke kaina ko na wanene?” Suka ce, na Manzon Allah (S) ne. “Ko kun san wannan dokin da nake kai na wanene?” Suka na Manzon Allah (S) ne. “Ko kun san wannan abayar da take jikina ta wanene?” Suka ce ta Manzon Allah (S) ce. “Ko kun san cewa Manzon Allah (S) ya ce ni da dan uwana Hasan mu ne ‘Sayyidaa Shababi Ahlil Jannah’? (Shugabannin Samarin Aljanna)?”.

Ya ci gaba yana ta yi masu magana. “To, da wane dalili ne za ku kashe ni?” Suka ce don kin Babanka ne. Sai Imam Husaini (AS) ya ce; “Ashe fadan ba nawa ba ne?”. Da ma Imam (AS) ya ce, a Sakifa aka kashe shi, da ba don juyin mulkin da aka yi wa Wasiyyin Annabi (S) kuma Baban Husaini, yaya za a yi a yi wannan aika-aikar a Karbala? Da ya ci gaba, sai suka ce, mu fa ba mu fahimtar maganar da kake yi, me kake cewa? Sai Imam Husaini (AS) ya ce; “Ba mamaki, cikuna ne da aka cika su da haram, ba zai yiwu su fahimci wa’azi ba”. Wannan yana nufin idan mutane suka ci haram, ko wa’azi ba su ganewa. Mu guji cin haram!

Haka abin ya faru, Imam (AS) ya tura ’ya’yansa suka fita daya bayan daya, duk wanda ya fita sai ya yi mubaraza da su sai su kashe shi. Da ’ya’yansa suka kare, sai ya tura ’ya’yan dan uwansa Hasan (AS) su ma aka kashe su. Lokacin da Ahmadus-Sani ya fito sai da suka gudu, sun dauka Manzon Allah (S) ne saboda kamar sa da Manzon Allah (S). Sai suka dawo suka ce ba Manzon Allah ba ne Ahmadus-Sani ne. Suka dawo suka kuma kashe shi. Ya Allah!

Da farko, ka ga sun san kamannin Manzon Allah (S) sarai. Ba ma ana maganar ko su Musulmi ne ko ba Musulmi ba. Sun yi wa Manzon Allah (S) farin sani, amma suka bututtuke idonsu suka yi abin da suka yi. Don Allah wane irin uzuri za a bai wa irin wadannan mutane? Zuciyarsu ta kekashe.

Da aka kashe ’ya’yan Hasan (AS), sai ’ya’yan Imam Ali (AS) (’ya’yan Ummu Banin), sai na Zainab, da ’yan uwansa na jini suka kare, sai Sahabbansa su ma dukkansu aka kashe su. Kwamandan Imam Husaini (AS) shi ne Abul Fadhlil Abbas, Kamaru Banu Hashim (kane gun Imam Ali). Sakina ’Yar Imam Husaini (AS) kishi ya dame ta, sai ta ce ya debo masu ruwa su sha. Ya dauki salkan ruwa ya nufi rafi don debo ruwa. Suka tare shi, ya keta tsakanin su kamar walkiya da takobinsa ya isa ya kuma debo ruwan. Har ya diba zai sha, sai ya tuna da Imam Husaini (AS) bai sha ruwa ba, sai ya fasa sha. Ya kama hanyar dawowa, sai makiya suka yi masa ‘ambush’ suka sari hannunsa da yake rike da ruwan ya mai da dayan hannun, shi ma suka sare shi ya rike da baki, suka cillo kibiya ta huda salkan rowan, suka sake saran sa, sai ya fado daga kan abin hawan da yake. Sai ya kira Imam Husaini (AS), sai ya taho kamar zaki ya dira kamar mikiya suka watse, sai ya rungume Abbas.

Ya dauka daya daga cikin makiya ne sai ya ce masa, don Allah ka bari mu yi bankwana da Maulana kafin ka kashe ni. Sai Imam (AS) ya ce, ai shi ne. Abul Fadhli Abbas ya yi Shahada, sai Imam Husaini (AS) ya ce, yanzu an karya mani kashin bayana, wato an kashe ‘standard bearer’ dinsa. Yanzu babu sauran mai rai tare da Imam Husaini (AS) cikin Ahlul Baiti dinsa da Sahabbansa, sai Imam Aliy Zainul Abidin (AS) yana fama da rashin lafiya mai tsanani, sai kuma mata da yara. Sai Imam Husaini (AS) ya bukaci da su saurara masa zuwa washe-gari, domin ya kwana yana Munajati da Ubangijinsa. Wannan ranar tara ga wata ke nan (Tasu’a).

Akwai ruwayar da ta nuna cewa, yana cikin ayyukan Daren Ashura, ya raya daren da Salla da Addu’a. Akwai Salla mai raka’a 100, kowace raka’a Kulhuwallahu (Suratul Ikhlas) 3, sai Salla mai raka’a hudu, kowace raka’a Suratul Ikhlas 50, sai kuma mai raka’a hudu, shi ma kowace raka’a za a karanta Ayatul Kursiyyu, Ikhlas, Falaki da Nasi kowacce sau 10. Bayan Salla sai kuma a karanta Suratul Ikhlas sau 100, sai kuma a yawaita zikirin Allah ne, Salati ga Manzon Allah (S), a kuma tsine wa makiyansu. Cikin Sallolin sai mutum ya zabi daya.

Sun saurara wa Imam Husaini (AS) suka ce, ai ko wani ne ya nemi hakan za mu yi masa, balle Jinin Manzon Allah (S). Ajib! Ran 10 ga wata (ranar Ashura ke nan), Imam Husaini (AS) ya fito, mata da yara suna kuka. Ya yi wa Sayyidah Zainab wasiyya da dauriya, kamar yadda yake al’adarsu, ya kiraye su ya yi masu wa’azi. Kafin nan sai da ya kira Umar Dan Sa’ad (Kwamandan sojojin Yazidu) da ma shi abokin Imam Husaini (AS) ne suna yara, ya ce masa ya rabu da wadancan mutane ya dawo gare shi. Sai ya ce, iyalinsa? Sai Imam ya ce, zai hada su da nasa iyalin. Sai ya kuma ce, gonarsa za a kwace. Sai Imam Husaini (AS) ya ce, zai ba shi shahararriyar gonarsa ta Madina, wadda Mu’awiyyah ya so ya saya, ko nawa ne? Amma aka ki sayar masa. Duk uzurin da ya bijiro da shi, sai Imam (AS) ya ba shi mafita, har ya zama babu sauran uzuri.

Da ma kuma shi Umar Dan Sa’ad an yi masa alkawarin Gwamnan Rayy a matsayin tukwicin aikin yakar (kashe) Imam (AS). ‘Appointment letter’ ma tana hannunsa, zai wuce kai tsaye ne. Sai Imam Husaini (AS) ya ce masa, “kamar ina ganin kanka a sagale a kofar gari, yara na harbi da dutse.” Sai Umar Dan Sa’ad ya ji haushi, ya tafi. Kamar yadda Imam Husaini (AS) ya ce ya faru, Gwamnan da bai yi ba ke nan, aka kashe shi aka sagale kan a kofar gari yara na jafan sa. Asara biyu ke nan, ba shi ga tsuntsu, ba shi ga tarko.

Umar dan Sa’ad ya ce, me kuke jira da shi ne? Suka yi kan Imam Husaini (AS), ya shiga fafatawa da su, sai da ya kashe mutane masu yawa a cikinsu, sannan suka iya masa. Shimir, tsinanne ne, ya yanka wuyan Imam Husaini (AS). Inna lillahi wa inna ilahi raji’un. Imam (AS) ya ce, hakika Kakansa (S) ya yi gaskiya, “ya ce mai siffar kare ne zai kashe ni.” Da Shimir ya ji haka sai ya fusata ya shiga dirza wukansa a wuyan Imam Husaini (AS), sai da ya raba kansa da gangan jikinsa. Ya Allah!

Zuljanan dokin Manzon Allah (S) wanda Imam (AS) ya gada, ya dawo ba Imam. Jikinsa duk jini yana ta kartar kasa, ba Imam (AS) a kansa. Dama kuma an bai wa sojojin Yazidu umurni cewa, su tsinke kan duk wanda suka kashe, sannan kuma su yi sukuwa a kan gawawwakin. Hakan ko suka yi, suka tsinke kawukan, suka kuma yi sukuwa a kan gawawwakin da dawakansu. Dama kuma sun yi kwanaki ba ci ba sha. Ga kishi ga kisa. Suka kuma nufi tantin a guje don dibar ganima suka kwashe duk abin da suka gani a tanti, suka kuma kwace wa mata abin kunne da abin wuya na zinari, duk suka sace har ma da Hijabansu sun kwace masu, suka kuma cinna wa tantin wuta.

Za mu ci gaba insha Allah.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan