HANTSI
Tare da Danjuma Katsina 0803 590 4408 katsinaoffice@yahoo.com
Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa:
Kule ga masu kaunar ci gaban ilimi a Jihar KatsinaWani littafi da aka rubuta mai suna ‘ISLAM AND HISTORY OF LEARNING IN KATSINA’, wanda Farfesa Abdallah Uba Adamu na Jami’ar BUK Kano da kuma Dakta Isma’ila Tsiga suka tace suka buga kuma ya fito a shekarar 1997, wanda madabba’ar kamfanin buga littattafai na Spectrum Ibadan suka buga, sun bayyana cewa a tarihin zuwan ilmin Musulunci a kasar nan, KATSINA ta taka rawar da ba inda ta taka kamar ta.
Littafin an samar da shi ne sakamakon wani taro na kasa da kasa da aka yi, wanda gwamnatin Jihar Katsina ta waccan lokacin ta dau nauyin shiryawa mai suna INTERNATIONAL SEMINAR ON ISLAM AND HISTORY OF LEARNING IN KATSINA STATE,wanda aka yi a shekarar 1992.
Taron ya tattaro masana daga kasashen duniya wadanda suka gabatar da laccoci na ilimi da aka gina su bisa bincike a kan wannan mas’alah. Taron yana daya daga cikin taron karawa juna sani, wanda aka yi nasarar haduwar masana daga ciki da wajen kasar nan, kuma aka yi baje kolin ilmi da bincike don gano yadda lamarin da ake tattaunawa yake a ilmance, kuma ya yi nasara sosai.
Daga cikin takardun da aka gabatar a lokacin wadanda suka ja hanakalin mahalarta, akwai mai suna ISLAMIC FUNDIMENTALISM; SHI’A IN KATSINA, wadda Dakta Muhammad Dahiru Sulaiman na Jami’ar BUK ya gabatar.
A kuma shekarar 1999, Wazirin Katsina, Dakta Sani Abubakar Lugga, ya buga wani littafi daya da Hausa mai suna GAWURTACCEN LARDI da kuma na Turancinsa mai suna GREAT PROVINCE. A littafin na Dakta Lugga ya kawo yadda Katsina ta fara zama kashin bayan ilimin zamani a arewacin kasar nan. Ya kuma kawo wasu fittattun mutane a kasar nan wadanda suka yi karatu a Katsina, wadanda suka taka rawar da ba wanda ya taka kamar ta a Nijeriya, ko kuma sune suka fara yin fice a wani fage na ilimi kafin wasu su biyo baya.
A shekarar 2008 Malam Labo Yari dan Arewa na farko da ya fara buga littafin zube na labari kirkira da Turanci, ya buga littafi mai suna MUHAMMAD DIKKO; HIS LIFE AND TIMES, wanda a ciki ya kawo tarihin Sarkin Katsina Dikko, ya kuma kawo dalilan da ya sa Turawa suka so mai da birnin ya zama cibiyar ilminsu.
A lokacin kaddamar da littafin ne, wanda Alhaji MD Yusuf ya dau nauyin bincike da bugawa, Labo Yari ya sanar cewa manufarsu ita ce; kudin da za a samu a wajen kaddamarwar a gina dakin karatu da su a cikin Jami’ar a sanya wa ginin sunan Sarkin Katsina Muhammad Dikko saboda irin gudummuwwar da ya bayar ga ilmin zamani a Jihar Katsina, tare da irin rawar da ta taka sosai wajen taimako da gudummuwa ga wasu Jami’o’in da ’yan Jihar Katsina kan je karatu, musamman Jami’ar ABU Zariya, BUK Kano, Usman Danfodiyo Sakkwato da wasunsu. Da kuma Kwalejojin Kimiyya da Fasaha da Kwalejojin Tarbiyyantar da Malamai don koyarwa a makarantu (NCE).
Jami’ar farko da Jihar Katsina ta fara mallaka Jami’a ce mai zaman kanta ta farko a tarihin Nijeriya ta Musulunci, kuma wadda wasu jama’u suka gina, suka kuma yi ikirarin ta al’ummar Musulman kasar nan ce mai suna KATSINA ISLAMIC UNIVERSITY. Jami’ar da tsarinta ya burge hamshakin Attajirin nan na Kano, Alhaji Alhasan Dantata har ya ba ta kyautar Naira biliyan daya, wanda suka ce ya yi masu aikin kudin, ba ya ba su kudin ba.
Jami’ar da kuma babu kamarta a yanzu a fasalin gini na zamani, wanda ya yi daidai da karatu a zamance da tsari na zamani da kayan aiki na zamani da ka’ida da Malamai daidai irin daliban da ke gare ta kamar Jami’ar UMARU MUSA ’YAR’ADUWA . Irin yadda aka zayyana ta, kuma aka gina ta, wannan ya sa farfajiyarta har ta zama wajen yawon bude ido da kuma daukar sina-sinai na yin fim ko waka. Marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa shi ne ya kafa ta a shekarar 2006 bayan rahoton wani Kwamiti mai karfi da aka kafa wanda ya yi ta yawo manyan Jami’o’in duniya yana ganin ya suke aikinsu. Kwamitin ya ba da rahontonsa da ba da shawarar yadda za a kafa ta da kuma kudurin gaba kadan ta zama abin misali da kuma ba kamar ta a kasar nan.
Gwamnan Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema shi ne wanda ya aiwatar da ginin Jami’ar baki dayansa. Ya kuma tabbatar da komawa mazaunin nata na din-din-din daga inda ta fara zaman wucin-gadi a harabar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Polytechnic, ya kuma tabbatar da budewa da sa mata sunan Umaru Musa ’Yar’aduwa.
Jami’ar ta fara yaye dalibai a shekarar 2009, inda ta dau dalibai 500, ta yaye 132 a shekarar 2010, ta yaye dalibai 343 a shekarar 2011, ta yaye dalibai 469. A yanzu Jami’ar na da dalibai sama da dubu shida a cikinta. Tana da ma’aikata 708. Tana yin kwasa-kwasai har 26, wadanda dukkanin su Hukumar kula da Jami’o’i ta kasa ta yarda da su dari bisa dari. A kuma wannan shekarar ta 2012 za su fara wasu sabbin kwasa-kwasan, ciki har da Likitanci, da sashen binciken cututtuka da magunguna da wasu kwasa-kwasan kimiyya da ilmin dan Adam.
A wannan tanadi gwamnatin Jihar ta fara shirin gina shiyyar karatun ilmin Likitanci na Jami’ar da kuma kokarin kammala katafaren Asibitin kashi na Jihar, wanda ke jere da Jami’ar, wanda ake sa ran a gaba ya zama Asibitin koyarwa na Jami’ar. Kashi casa’in na daliban Jami’ar sun fito ne daga Jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Zamfara. Sauran kashi goman kuma suka fito daga Jihar Kaduna da sauran Jihohin kasar nan.
Jami’ar daga kafa ta ta samu nasarorin da ba wata Jami’a da ta samu irin su. Wannan ya sa ta a matsayi na dubu tara daru uku da casa’in (9390.000) a duniya. Wanda ba karamin hobbasa ba ne in ka dubi yawan Jami’o’in da ke a duniya. Kasar Indiya kawai tana da sama da Jami’o’i dubu goma. Ban da Chaina da kuma sauran kasashe. Wannan matsayi ne na kayan aiki da karatu ingattace.
Hakika gwamnatin Jiha Katsina na iyakar kokarinta a kan ganin Jami’ar ta tsere wa sa’a, kuma ta kai ga gacin da gurin da aka kafa ta. Amma tabbas akwai bukatar masu hannu da masu hannu da shuni da Attajiarai da kuma masoya ilimi su kawo dauki don ganin tabbatuwarta da ganin cewa wannan Cibiyar Ilimi ta tsayu da duga-duganta.
Yanzu yadda tattalin arzikin duniya ke tanga-tangal da kuma yadda harkar ilimi ke da tsadar gaske, akwai bukatar gidauniya don ganin Jami’a kamar wannan ba abin da ya shafe ta, domin nan ne za a iya horar da matasan za su gina al’umma.
A kasashen da suka ci gaba, Attajiran yankin kan ware kaso mai tsoka don ganin sun tallafa wa ilimi a inda suke. Wasu kan gini da sunan kakaninsu ko wasu masoyansu, wasu kan dau nauyin wani bincike ko wani kwas, kamar yadda gwamnatin Katsina a zamanin Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ta taba yi a kan Marigayi Yusuf Bala Usman a Jami’ar ABU Zariya.
A baya wadansu bayin Allah masu kishi sun kawo dauki da kuma yake taimakon Jami’ar, mutane irin su Alhaji Abdu’azeez Maigoro, Alhaji Ma’a Gafai, Mai Shari’a A. Ahmad, Injinya Muttaka Rabe Darma, Tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Tarayya, Alhaji Umaru Abdullahi da kuma Shugaban Kwastam na kasa da Alhaji Dikko Abdullahi Inde, da kuma wata niyya daga kamfanin MAXAIR wanda ba su kai ga aiwatarwa ba.
Jami’ar na kara bunkasa, kalubalenta na kara yawa, a yanzu haka ana gina dakin kwanan dalibai mai daukar sama da dalibai dubu biyu, wanda akwai bukatuwa masu yawa a kan wannan. Yayin da tattalin arzikin kasar nan ke rawa da fitintinu a cikin kasar, ya za ta iya tsayuwa da fuskantar duk kowane irin kalubale ta yi nasara?
Wannan yana bukatar dauki na duk wani mai son ci gaban ilimi. Lamarin na bukatar addu’a da fatan alheri. Yana bukatar kishi da sadukarwa. Yana bukatar Attajiranmu su kafa wata gidauniya ta sa ido don ganin ci gaban wajen. Yana bukatar a ji cewa ba wai gwamnati kawai za a bar wa ba ita kadai, kowa ya zama yana da ruwa da tsaki wajen nasararta. Yana bukatar duk wani kamfani mai mazauni a Katsina a kulubalance shi a kan ci gaban ilimi a Jihar nan? Me ka yi wa Jami’ar ’Yar’aduwa?
Jami’ar na da sashen ayyuka don samar mata da kudin shiga, wanda kwarraru ke aiki a wajen; kuma da a ce Attajiranmu da ’yan kwangila, ma’aikatun gwamnati da na Kananan Hukumomi da za su rike wannan sashen, da tabbas Jami’ar ta samu karin tsaba a aljihunta, da kuma ayyukan su masu ba ta aiki sun kara inganta. Ko’ina kake Jami’ar na bukatar kyakkyawar addu’arka.
