|
|
Juma'a 30 Ramadan, 1431 Bugu na 939 ISSN 1595-4474 |
|
|
|
Rubutun da na yi a makon da ya gabata, wanda a ciki na bayar da shawarar cewa ya kamata ’yan uwa su fito da wani tsari na rage farashin yadda suke more rayuwarsu da kadan don a ba ginin HUSAINIYYA. Wani kaso kawai za ka bayar wanda ba zai taba komai na dukiyarka ba, sai dai kawai ya rage dan holewa da fantamawa da ake yi.
Na sami sakonnin wayar hannu da yawan gaske wadanda ke karfafa wannan shawara, wanda saboda yawansu na ga kamata ya yi in sake wani rubutu, in kuma hada da duk wata shawara da wasu suka kawo domin mu hada karfi da karfe a wannan aiki. Kuma wannan fili a shirye yake duk wanda ya kawo wata shawara ko gudummuwa a kan wannan lamari a buga shi, wanda wannan zai kara ta da hamasar nan ta ’yan uwa ga ganin cewa mun ba da wannan kyauta a badi da izinin Allah.
Sakon farko da na samu na same shi ne daga wajen wani mutum mai suna Abubakar Sani, wanda ya ce ya aiko ne daga Kaduna. Ya rubuto cewa; “Danjuma Katsina, ba ka yi mana adalci ba. Don kuwa ka mai da lamarin cewa taimakon na masu kudi ne, su za su bayar. Mu da ke rayuwa da kyar fa, kana nufin ba mu da wata hobbasa da za mu iya kenan? Me kake nufi? Ku ji dadin nan, can ma ku kankange? Wallahi sam ba ta yiwuwa. Ni nakasasshe ne, amma sai na tara kwata miliyan, kuma in ba da ta ga IMAM HUSAINI (AS). Wallahi na dau alkawarin ba na wulakanta gobe kiyama”.
Wannan shi kuma cewa ya yi, “HANTSI Allah ya huci zuciyarka na tuba.” Daga Abubakar.
Wani sakon kuma cewa ya yi: “Na lissafa na ga nakan kashe kudin katin waya a kullum Naira 75, kuma wayar da nake yi wata ba ma ta dole bace. Sannan ina kashe kudin man janareto na kullum 500, kuma kallo nake yi kawai. Sai na ga cewa ina iya mai da kashe kudin katin waya 300 in samu rarar 450. A janareto ina iya mayar da shi 250, in samu rarar 250. Idan aka tara 450 da 250, sun zama 700 kenan a kullum, a wata dubu 21 kenan, a wata shida dubu 126 kenan. Da izinin Allah zan yi wannan tsarin kuma zan bayar don kar a yi ba da ni ba.”
HANTSI: Aiki da hankali ya fi aiki da agogo. Wannan bai rubuta sunansa ba, Ubangiji ya ida nufi, amin.
Ita kuwa wata Malama daga Kano tambaya ta yi, “Danjuma, menene hukunci idan ni da abokiyar zamana muka tsara wata dabara, daga abin da Maigida ke ba mu don cefene a gida, mu yi asusu, mu kuma tanada mu bayar? Don gaskiya mun lura Maigidan namu fa sai a hankali, in abu ya shafi a fitar a bayar ne, amma dai alhamdulillahi, akwai kokarin zuwa abubuwa, ko nawa zai kashe. Kuma muna tsoron mu yi masa maganar ya gwasale mu, kuma ya sa mana idanu.”
HANTSI: Na boye sunanta da lambarta don gudun fitina. Tambayarki ta shiga Fikihu, kuma ni ma dai a nan sai a hankali. Amma ina ba da sharwarar ku tambayi Malamai yadda mijinku ba zai gane ba. Maslahar addinin da aka bayar sai ku yi aiki da ita. Allah ya sa a cimma guri, amin.
Malam Mai Zanen Hula cewa ya yi, “abokinka da kuka yi waccar tattaunawa da shi ya rubuta cewa yana da motoci uku da kuma daya da ya saya don ya kashe wata wuta, sai aka zuba wutar fetur, don haka take ajiye, shawarata gare shi ya bayar da wannan motar da ya yi niyyar kashe wutar da ita. Ina jin lalle wannan kyautar za ta kashe waccan wutar”.
HANTSI: Malam Mai Zanen Hula, na yi masa wannan zancen. Amma sai ya bayyana min matsalar da ke ga ita motar, kisan wutar ita ce sai ya nemi izinin mai motar? Wadda yana ganin da wuya ta yarda. Amma ya dau alkawarin sayar da karamar cikinsu ya hada da wani abin. Don Allah ka yi koyi da shi mana.
SANI daga Kano cewa ya yi, “haka ya kamata a yi rubutun da zai amfane mu ya kuma zaburar da mu, ya kuma kara sa wa mu sallama, ya kuma tabbatar da mu. A sha ruwa lafiya”.
HANTSI: Mun gode mai magani. A tarbiyyar da muka samu duk abin da za mu yi a tsakani da Allah muke yi. Sai dai a samu kuskure ko ajizanci ko rauni, amma a rika kyautata mana zato, kuma a rika yi mana nasiha don mu gyara. Allah ya bar zumunci. Da fatan kai ma za ka rage farashin jin dadin rayuwa don Husainiyya.
“Wai Malam me kake nufi ne a rubutunka? Don mun karanta, amma sai muka rasa alkiblar da ka dosa”. Wasu da suka kira kansu ’Yan Group.
HANTSI: A’a ba matsala. Abin da na rubuta shi nake nufi, amma in an shiga rudu, to, Allah ya yi agaji, addu’armu kenan. Rokona a rage farashin rayuwa a sai tikitin shiga Aljanna, kila kun san ta ko?
“To Malam Danjuma, muna bukatar fili a ALMIZAN wanda zai hada zumuncin wannan ra’ayin naka na ginin Husainiyya. Allah ya ba mu ikon taimakawa albarkar wanda za a yi aikin domin sa, amin”. Daga Musa Usman Jos Jihar Filato.
HANTSI: Wannan sakon ba nawa bane na Edita ne. Allah ya ba da ladan niyya, ya kuma ba da ikon taimakawa ta rage jin dadi da dadin dindindin.
Wani da ya rubuto, amma ya ce daga Zariya yake, ba suna sai lamba. “Don Allah wannan wane dan uwa ne da ka buga hotonsa a filinka? Kuma yanzu a ina yake?”
HANTSI: Ba ni na buga ba, Edita ne, amma ga labarinsa da sunansa. Ba tambayar sunan mai hoto da aka buga ba, me ka tsara wa HUSAINIYYA?
“Gaskiya wannan fomula taku mai shiga ce, kuma mai niyyar zai fitar da kudi ba tare da wani tsuwwa ba, amma don me ba za a yi kira mu yi amfani da ita ba?” Wani mai suna Danlami daga Batsari Jihar Katsina.
HANTSI: Malam ka san shirin da kowa ke yi ne a boye? Iya ruwa fa fid da kai. A aikin alheri irin wannan ba a jiran kowa, ana kowa tasa ta fisshe shi ne, don mazaunin kowa daban a gobe kiyama. Babbar matsalar ita ce ba wanda ya san yaushe zai mutu, don haka rage jin dadi ka yi tanadin rayuwa bayan mutuwa. Yi gaggawar kai taka gudummuwar ga HUSAINIYYA.
Isah daga Gombe, “jiya na karanta abin da ka rubuta a kan HUSAINIYYA, kuma da shi na kwanta har na yi barci, na kwanta da alwala, na kuma yi duk ayyukan ranar kafin in kwanta. Na yi wani mafarki mai dadi cewa da ’yan uwa za mu dukufa a wannan aikin na HUSAINYYA gadan-gadan, idan muka kara son juna, kanmu zai kara haduwa. Da mun samu babbar fa’ida. Don Allah ka isar da sokona.”
HANTSI: Dan Gombe ajiye mafarkin gefe guda. Abin da ka fadi haka yake ko a zahiri, kamar ka ce ne jiya na yi mafarkin ina jin yunwa, kuma na ci abinci na koshi. Darasi da tarihi ya tabbatar mana duk lokacin da ’yan uwa suka sa gaba ga wani aikin alheri, sukan zama ’yan uwan sosai. AMMA TUNDA KA GA DIL ME KA TSARA? DON MAFARKI NA IYA ZAMA UMURNI?
“Bayan gaisuwa gare ka, da fatan Allah ya saka maka da alherinsa a kan wannan fadakarwa da zaburantarwa da aka yi. Da kuma fatan ’yan uwanmu mawaka za su zauna su fito da wasu baituka na zaburar da mu a kan gina wannan HUSAINIYYYA. Zan ba da shawara kamar kari guda uku, Allah ya sa su dauki ko da daya ne. Karin farko shi ne “da kudinmu da jikinmu za mu gina HUSAINIYYA.” Kari na biyu shi ne “gina HUSAINYYA na cikin babban gurinmu,” da dai sauransu.” Uwaisu Adamu daga Kano.
HANTSI: Malam Uwaisu, na san gwarazan mawakanmu sun ji ka, kuma ko ma menene in dai aka ce umurnin su Malam (H) ba sa wasa da shi, jira kawai ka ji baituka nan da kwanaki kadan. Tambaya; kai kuma wane tanadi ka yi? Don ba wai kawai zuga wasu ba, kai ba ka komai.
“Danjuma wannan kira naka ina ganin a ba da karfinsa ga Sistoci, don kuwa sune za ka ga suna ajiye kayan kyale-kyale a cikin dakunansu, kuma kullum kara tara su suke, wanda kuma ba sa son abin da ya taba su. Su ya kamata a fada masu cewa a rage yayume-yayume da rarume-rarume ana ajewa. A fito da gwala-gwalan da aka boye a ba da ga ginin HUSAINYYA”.
HANTSI. To, kun ji fa ’yan uwanmu Sistoci daga wanda kila tsoron fushin matarsa ya hana ya rubuta sunansa, har ma ya roke ni in tace rubutun kafin in buga.
“Daga ’yan filin kai tsaye, dandalinmu zai fito da wani tsari na rubutu, wanda zai kara taimakawa wajen fadakar da ’yan uwa wajen ganin cewa lamarin ya shiga zuciyar kowa kuma ya zama wani kalubale, kuma za mu ba da tamu daidai gwargwadon iyawa”.
HANTSI: Allah ya ida nufi, dama ai Allah bai dorawa bawa abin da bai iyawa, ku dai ku tabbatar da kun yi daidai kima ba gwargwado ba.
“Daga ’yan Dandalin Matasa na Katsina, wannan kalubale ne gare mu”.
HANTSI: Wannan shi ne mafi ala fiye da yawan fitowa a cikin ALMIZAN. Allah ya sa ALMIZAN ta ba da labarinku da cewa kun yi kaza na rawar gani da nuna misali. Dama duk kalubale mai gasa wajen matasa ake jefa shi. Muna ji muna gani muna kuma saurare.
“Don Allah ka taimaka min in turo da tawa gudummuwar, ka aika da ita. HANTSI ka turo min lambar asusun ajiyarka ta Banki insha Allah zan yi tarayya a wannan aikin.”
HANTSI: Allah ya ba da ikon aikatawa. Sai dai gaskiya ba aikina bane amsar na kowa in kai. Kar ma ka fara, don ina jin tsoron suka shigo hannuna su zama bashi. Don haka, don Allah ka rufa min asiri.
Wani cikin fushi wai yana ta bugawa ban dauka ba, alhali ina wajen tafsir ne da maraice. Bayan shan ruwa da na ga ‘miss calls’ dinsa ya fi dozin sai na kira shi, tana kadawa ya dauka cikin fushi sai ce min ya yi, ta ina ake aikawa da gudummuwar ginin HUSAINIYYA?
HANTSI: Don Allah yi hakuri zan kyale tsokacina a kan yadda ka hassala, saboda ka riga ka tanadi abin da za ka bayar ka dan kara hakuri kila masu ruwa-da-tsaki a kan aikin su ba da sanarwar yadda taimakon mai niyya zai kai ga aikin na HUSAINYYA.
Akwai sakonni da yawa da na samu ciki har da wannan: “Malam Danjuma ina wuni? Yaya aiki? A gaskiya rubutunka na wannan makon ya caza ni matuka, to yaya zan yi ni ma in kai nawa ’yan kudin da zan tara? Ko kuma wa zai karba?”
Bari in rufe rubutun wannan makon da wannan sakon da na samu daga Rabi’u Hamza Gujungu. “Muhimmiyar kyauta ga Malam (H) ta cika shekara 60 a duniya. Kai Malam Danjuma Allah ya saka da alheri albarkacin Ramadan.”
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |