Wa ke aiko da bindigogi Nijeriya?
Ana tuhumar wani da shigo da guda 80,000
A bisa zahirin gaskiya ban so na dami masu karatuna da wannan rikitaccen rubutun ba, sai dai kawai domin dalilai biyu ne na ga ya kamata na kawo maku su.
Na farko dai saboda abubuwan da ke ta faruwa ba tare da kakkautawa ba a cikin wannan kasar da kuma halin da ta fada na rashin tsaro. Don haka ne na ga cewa wannan nauyi ne da ya hau kan ’yan jarida da su fahimtar da al’umma matukar iyawarsu, yin hakan zai sanya ko dai ita kasar ta fadaka ta tsira, ko kuma ta ruguje saboda munafunci da kuma halin ko-in-kula.
Na biyu, wannan sako dai yana zuwa ne daga wata majiya da za mu iya cewa ko ma me ya faru a kasar bai shafe ta ba, wato daga wanda shi ba dan kasar ba ne. Ya zo da magana daidai sani da kuma fahimtarsa ba tare da nuna tsoro ko son kai ba, wannan hukunci da ya yanke ko da ya sha bamban da fahimtarmu, yana da dukkanin hujjojin da za mu iya cewa lallai biri ya yi kama da mutum.
Don haka masu karatu, a sha karatu lafiya!
Naku Dakta Aliyu U. Tilde
Ci Gaban Jawabin
Tweet
Ranar Juma’a da ta gabata ne kotun kolin kasar nan, wacce ake wa lakabi da ‘daga ke sai Allah ya isa’, ta yanke hukuncin cewa Gwamnan Jihar Sakkwato, Alu Magatakarda Wamakko da wasu Gwamnoni hudu su sauka daga kan mukaminsu bisa cewa sun zarce ka’ida a zaman mulkin nasu.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Jama’a na kuka da hana hawa mashin a Potiskum
Wasu mazauna tsakiyar garin Maiduguri sun zargi Rundunar hadin gwiwa ta tsaro ta jihar (JTF) da kashe wasu mutane 11, wadanda suka ce galibinsu matasa ne ba tare da sun aikata wani laifi ba. Tun ranar Asabar ta makon jiya ne jami’an Rundunar hadin gwiwa ta JTF din a Maiduguri suka sanar da cewa sun halaka wadansu mutane 11 wadanda suke zargin cewa ’yan boko-haram ne. Tuni dai wasu mazauna birnin Maiduguri suka bukaci gwamnatin Tarayya da ta gaggauta janye wasu sojojin da ke sintiri a wasu sassan jihar ta Borno.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Ba wanda aka kama
Daga jihar Bauchi mun sami labarin wasu mutane da ake zargin ’yan kabilar Bachama ne sun lalata masallatai da gine-ginen gwamnati a Karamar Hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi a cikin makon da ya gabata. Ci Gaban Labarin
Tweet
A ranar 5 da 6 ga Rabi’ul Awwal 1433 ( 28-29 ga Janairu 2012) ne ’yan uwa na Ahlud Duthur na Harka Islamiyya suka gabatar da taron kara wa juna sani mai taken “Harkokin Kasuwanci a Musulunci” a karo na biyu a dakin taro na multipurpose da ke garin Katsina, inda aka samu mahalarta daga sassa daban-daban na kasar nan, kuma Sayyed Ibraheem Zakzaky (H) ya kasance Babban bako da ya rufe taron a ranar Lahadi, inda ya bayyana muhimmancin taimaka wa jama’a da dukiyar da Allah ya hore wa masu.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Wasu mata kiristoci sun kai wa Sayyid Zakzaky ziyarar godiya
Wani gungun Kiristoci mata da ke zaune a rukunin gidaje na ‘Danraka Estate’ da ke daura da ABU Congo Campus, Zariya, sun kai wa Sayyid Ibraheem Zakzaky ziyara. Sun ce sun zo ne saboda su nuna godiyarsu game da irin karamci da yake nuna masu kowane lokaci, “musamman ma lokacin rikicin day a faru, inda yake turo mutanensa su kare mu daga masu kawo mana hari”, in ji su.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Tambihi
Arba’in din Imam Husain (AS)Tare da Muhammad Suleiman 08029493717
Ranar Arba’in din Imam Husain (AS) rana ce wadda take da muhimmanci, musamman ga mabiya Ahlul Baiti (AS). Kuma kiyaye ranar yana daga cikin alamomin Mumini, kamar yadda haka ya zo daga Imam Hasan Al’askari (AS), inda ya ce; “Alamomin Mumini (wato dan Shi’a) guda biyar ne. 1. Yin Salla raka’a 51 ko wace rana, 2. Ziyarar Arba’in. 3. Sa zobe a dama. 4. Sa goshi a kasa (ta’afir). 5. Bayyana karatun Bismillah a Salla”.
Ci Gaban Labarin
Tweet
Hannunka mai Sanda
Nasiha ga iyaye game da tarbiyyar yara
Hannunka mai sanda ya lura cewa wasu iyaye na halin ko oho da dora wa yara nauyin da ya fi karfinsu, wanda hakan kan sa yaran rayuwa a wahalce. Yara, kiwo ne da Allah Ta'ala ya damka wa iyaye, kuma zai tambaye su a kan yadda suka tafiyar da kiwon, kamar yadda su din ma za a tambayi nasu iyayen a kan yadda suka lura da su lokacin suna kanana.
Ci Gaban Labarin
Tweet
