Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           



Muna Facebook


 


 

Ku bimu a Twitter

  


 


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan


Ta imel a takaice,
kai tsaye

Sunanka:

Imel din ka:

Ra'ayinka:


 

Janye yajin aiki

Jama’a sun fasata da NLC

Jama'a sun fusata matuka da matakin da kungiyar kwadago, NLC, ta kasa ta dauka na mika wuya ga tayin Naira 97 ga litar mai da gwamnatin Goodluck Jonathan ta bayar, inda ta bukaci kowa ya koma bakin aikinsa duk da kuwa a baya suna korarin cewa ba za su koma bakin aiki ba, matsawar an kara kudi a kan Naira 65.

Jama'a da dama a Kano, Kaduna da Legas sun bijire wa umurnin uwar kungiyar kwadago ta kasa da ta bukaci mutane su ci gaba da zama don yajin aiki a ranar Litinin, amma kar su fito zanga-zangar adawa da cire tallafin mai da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.
    Ci Gaban Jawabin

Wanda ake zargi da kai harin coci ranar Kirsimeti Ya tsere daga hannun ’yan sanda

Mutumin da ake zargi da kai hari a wani Coci da ke Garin Madalla, Suleja ranar Kirsimeti, kuma aka ba da sanarwar cafke shi ranar Asanar da ta gabata, mai suna Kabiru Sakkwato, a halin yanzu dai ya tsere daga hannun ’ya sandan dake tsare da shi. Wanda kuma wannan ya sa hukumar ’yan sandan ta kasa ta dakatar da Kwamishian ’yan sanda, Zakari Biu, wanda shi ke da alhakin kula da gudnar da binciken.     Ci Gaban Labarin

 

Sojoji sun ci zarafin Alkur’ani a Maiduguri

Jama’a sun koka matuka da matakin cin zarafin Alkur’ani mai tsarki da wasu daga cikin sojojin rundunar musamman don wanzar da zaman lafiya (JTF) ke yi a yankin Ummarari da ke Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
    Ci Gaban Labarin

Akwai siyasa a tsare Kwamared Nuhu Muhammad

Ranar Litinin da ta gabata ne jami’an soja a Kaduna suka gabatar da tsohon Shugaban kungiyar direbobin tanka ta Kaduna, kuma Marafan Narasawa Kaduna, Kwamared Nuhu Muhamamd da dansa Musa ga manema labarai bisa zarginsa da mallakar bindigogi da sauran wasu makamai ba bisa ka’ida ba, wanda kuma Lauyansa ya ce wannan kamu yana cike da siyasa.     Ci Gaban Labarin

Juyayin Yaumu Arba’een na banaYa zo da sabon salo

’Yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky na wannan kasa sun bi sahun ’yan uwansu na duniya ta hanyar yin tattaki a kafa zuwa taron juyayin kwana 40 da shahadar Imam Husaini (AS), inda suka taka daga sassa daban-daban na kasar nan zuwa Husaniyyar Bakiyyallah, Zariya.
Ci Gaban Labarin

Jami’an leken asiri na Mossad ne suka kashe masanin nukiliyar Iran

Wata jaridar London da ake kira SUNDAY TIMES ta bayyana cewa jami’an Hukumar leken asiri na Haramtacciyar Isra’ila, MOSSAD ce ke da alhakin kisan dauki dai-dai da aka yi wa wani masanin fasahar nukiliyar Iran a makon jiya.
    Ci Gaban Labarin

Tambihi

Arba’in din Imam Husain (AS)
Tare da Muhammad Suleiman 08029493717

Ranar Arba’in din Imam Husain (AS) rana ce wadda take da muhimmanci, musamman ga mabiya Ahlul Baiti (AS). Kuma kiyaye ranar yana daga cikin alamomin Mumini, kamar yadda haka ya zo daga Imam Hasan Al’askari (AS), inda ya ce; “Alamomin Mumini (wato dan Shi’a) guda biyar ne. 1. Yin Salla raka’a 51 ko wace rana, 2. Ziyarar Arba’in. 3. Sa zobe a dama. 4. Sa goshi a kasa (ta’afir). 5. Bayyana karatun Bismillah a Salla”.
Ci Gaban Labarin

Hannunka mai Sanda

Zanga-zangar cire tallafin mai

Tabbatar da karin kudaden albarkatun man fetur da cire tallafin gwamnati, wani rashin imani ne gami da kokarin aiwatar da muradun Amurka da sauran kasashen Turai.
    Ci Gaban Labarin

Tunatarwa:
Tare da Sayyid Ibrahim Zakzaky

Al’amarin Imam Husain ya ma zama mahadan ‘Insaniyya’

Mai karatu a yau mun tafe ne da jawabin da Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya yi ga dubun-dubatan jama’ar da ta taru a Husainiyya Bakiyyatulla da ke Zaria a ranar Arba’in na Imam Husain wanda aka yi ranar Asabar 20 ga Safar, 1433. Ibrahim Musa ne ya nakalto maku daga wayar salula, ya rubuta.
A sha karatu lafiya.


Saurari Tafsirin Sayyid Zakzaky: 

 Farkon Suratul Muhammad (S)

 


Daga Gidan Annabta
Na Marigayi Abubakar Abdullahi Almizan

ADDU'AR NEMAN TSARI A WATAN SAFAR

Wannan ita ce addu’ar da ake karantawa sau 10 kullum a cikin wannan watan na Safar da nufin neman kariyar Allah daga bala’in da yake ciki.

“Ya shadidal kuwwa, wa ya shadidal mihali, ya azizu,ya azizu, ya azizu dhallat bi’azmatika jami’u khalkika fakfiniy sharra khalkika ya muhsinu ya mujmilu ya mun'imu ya Mufdhilu ya la ilaha illa anta subnanaka inniy kuntu minaz zalimin, fastajabna lahu wa najjainahu minal gammi wa kazalika nunjil mu'uminin wasallahu ala muhammadin wa alihi addayyibinad dahireen

Daga Injiniya Abdussalam Shu’aibu


Hotunan wannan mako: