Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           



Muna Facebook


 


 

Ku bimu a Twitter

  


 


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan


Ta imel a takaice,
kai tsaye

Sunanka:

Imel din ka:

Ra'ayinka:


 

Sojan Amurka sun shirya wa rugujewar Nijeriya

In ji wata mujalla a Amurka

Akwai kwararan alamu da ke nuna cewa Amerika tana shirye-shirye tarbar yiwuwar wargajewar kasar nan daga abubuwan da suke faruwa tun a ’yan shekarun nan.

Wadannan alamu sun fito ne a wani bayani da wata mujalla da ake kira NEWSRESCUE a Amerika ta wallafa a shafinta na intanet www.newsrescue.com , inda aka yi bayanin wata makala da Daraktan AllAfrica Global Media, Mista Daniel Volman, ya gabatar a taron kara wa juna sani da AFRICOM ta shirya a Fort McNair na Amurka.
    Ci Gaban Jawabin

Tashin bama-bamai a Kano:An ga wasu cikin kayan jami’an tsaro suna kisa

Mutumin da ake zargi da kai hari a wani Coci da ke Garin Madalla, Suleja ranar Kirsimeti, kuma aka ba da sanarwar cafke shi ranar Asanar da ta gabata, mai suna Kabiru Sakkwato, a halin yanzu dai ya tsere daga hannun ’ya sandan dake tsare da shi. Wanda kuma wannan ya sa hukumar ’yan sandan ta kasa ta dakatar da Kwamishian ’yan sanda, Zakari Biu, wanda shi ke da alhakin kula da gudnar da binciken.     Ci Gaban Labarin

 

Wasu Kiristoci sun shiga hannu
Bisa zargin watsa sakonnin ‘Jihad’

Jami’an tsaro farin kaya, wadanda aka fi sani da SSS, sun gabatar da wasu ’yan siyasa a gaban kotun Majistare da ke Yola bisa zargin watsa sakonni ta wayar salula don neman ta da ricikin addini a jihar ta Adamawa.
    Ci Gaban Labarin

Sakon Shaikh Jingir ga Jonathan
Ka fito da ’yan Boko Haram da ke cikin gwamnatinka

Kungiyar Izalatul Bid’ah Wa ‘iklamatis Sunnah ta kasa, ta bukaci Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana sunayen ’yan Boko-Haram din da suke tare da shi a cikin gwamnatinsa suke zama teburi guda suke cin abinci suke shan shayi tare.     Ci Gaban Labarin

Bin tafarkin Shehu Danfodio ne zai warware matsalolin kasar nanSayyid Zakzaky a Abuja

Daga Aliyu Saleh, MSU Abuja da rahoto daga www.harkarmusulunci.org A ranar Asabar 27 ga watan Safar, (21/1/2011) ne ’yan uwa na Resource Forum da ke Abuja suka shirya tare da gabatar da wani gagarumin taron tunawa da haihuwar Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo (RA) karo na hudu a babban dakin taro na masallacin kasa da ke Abuja.
Ci Gaban Labarin

An gudanar da taron juyayin wafatin Manzon Allah (S) a Zariya

Daga www.harkarmusulunci.net da Musa Muhammad Awwal

A ranar Lahadin 28 ga watan Safar 1433, wanda kuma ya zo daidai da 22 ga watan Janairu aka gudanar da taron juyayin tunawa da rasuwar Fiyayyen halitta, Manzon Allah, Annabi Muhammadu (S) a Husaniyya Bakiyyatullah, Zariya, wanda kuma Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sayyid Ibraheem Zakzaky ya gabatar da jawabi.
    Ci Gaban Labarin

Tambihi

Arba’in din Imam Husain (AS)
Tare da Muhammad Suleiman 08029493717

Ranar Arba’in din Imam Husain (AS) rana ce wadda take da muhimmanci, musamman ga mabiya Ahlul Baiti (AS). Kuma kiyaye ranar yana daga cikin alamomin Mumini, kamar yadda haka ya zo daga Imam Hasan Al’askari (AS), inda ya ce; “Alamomin Mumini (wato dan Shi’a) guda biyar ne. 1. Yin Salla raka’a 51 ko wace rana, 2. Ziyarar Arba’in. 3. Sa zobe a dama. 4. Sa goshi a kasa (ta’afir). 5. Bayyana karatun Bismillah a Salla”.
Ci Gaban Labarin

Hannunka mai Sanda

Zanga-zangar cire tallafin mai

Tabbatar da karin kudaden albarkatun man fetur da cire tallafin gwamnati, wani rashin imani ne gami da kokarin aiwatar da muradun Amurka da sauran kasashen Turai.
    Ci Gaban Labarin

Tunatarwa:
Tare da Sayyid Ibrahim Zakzaky

Al’amarin Imam Husain ya ma zama mahadan ‘Insaniyya’(11)

Mai karatu a yau mun tafe ne da jawabin da Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya yi ga dubun-dubatan jama’ar da ta taru a Husainiyya Bakiyyatulla da ke Zaria a ranar Arba’in na Imam Husain wanda aka yi ranar Asabar 20 ga Safar, 1433. Ibrahim Musa ne ya nakalto maku daga wayar salula, ya rubuta.
A sha karatu lafiya.


Saurari Tafsirin Sayyid Zakzaky: 

 Farkon Suratul Muhammad (S)

 


Daga Gidan Annabta
Na Marigayi Abubakar Abdullahi Almizan

TASBIHIN GAFARAR ZUNUBAI

An ruwaito daga Kulainy, da isnadi mai girma daga Imam Bakir (AS) ya kasance yana cewa; “Wanda ya karanta wannan tasbihi sau uku bayan kowace Sallar farilla kafin ya canza daga zamansa, Allah zai gafarta masa zunubbansa ko da sun kai kamar kumfar kogi ne: “Astagfurullahallazi la’ilaha illahuwa hayyul kayyum zuljalalu wal ikram wa’atubu ilaihi”.

Har ila yau daga gare shi (AS) yana cewa; “An so mutum ya yi istigfari sau 70 bayan kowace Sallar subahi”. Akwai falala mai yawa ga wanda ke aikata hakan.

Karin bayani a duba Mafatihul Jinan shafi na 639-646.

Daga Alkazeem M. Al-Hassan, 08062740226.


Hotunan wannan mako: