Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



A Takaice kai Tsaye:
Na Aliyu Saleh, Ta GSM: 0803 698 3947

ZUWA GA MA’ABOTA WANNAN FILIN

Zuwa ga ’yan uwana, ’yan uwa ma’abota wannan filin yana da kyau mu fahimci cewa, muna da bambancin mahanga, kar wannan ya sa mu mayar da filinmu kamar dandalin mayar da martani, mu yi uzuri ga junanmu, in kuma za mu mai da martani ga wani, to mu yi cikin hikima da girmama juna.

Daga Kabiru Karkarku 0706 095 7510

SADAKA RASULUL KAREEM!

Manzon Allah (S) ya ce, “babu mai son Ali sai mumini, babu mai kin sa sai munafiki”. To, in ma ba ka fahimci Hadisin ba, ga misali kusa da ni, Hadisi na alamomin munafiki uku ne, yana cika su sai gaskiya ta bayyana, ga Hadisin farko dauki abin a hankali ka gani.

Daga Muhammad Ghali A. Garo

WANNAN ITA CE RANAR ASHURA

Ranar Ashura ita ce ranar da aka kashe dan Manzon Allah tare da iyalansa da Sahabbansa da ’yan uwansa kuma cikin azaba, yunwa da tsananin kishin ruwa, wanda Banul Umayya da ’yan kanzaginsu suka aikata da niyyar kawo karshen addinin Musulunci. Don haka ’yan uwa Musulmi na kowane bangare ko mazhaba mu gane ranar Ashura ba ranar cika-ciki ba ce, ranar kuka ce don mika ta’aziyya ga Manzon Allah (S).

Daga Ibn Aliyu Guri (Pharmacy) 0706 326 5152

ALLAH SARKI TALAKAN NIJERIYA

Allah Sarki talakan Nijeriya, ba ka da mai tausaya maka. Dalilin wannan magana tawa shi ne duk wanda ka ga yana fafutika a kan talakawa in ka bibiya yana son cimma wata manufarsa ne kawai. Misali Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Malam Sunusi Lamido Sunusi yadda yake sukar lamirin ’yan Majalisa, musamman kan kudaden da ake kashewa a kansu, sai a yanzu talaka ya gane ma’anar hakan. Tunda yake ta caccakar sa ba mu taba jin sa yana sukar lamirin Majalisar Zartarwa ba, duk da kuwa babu wanda ya san iya adadin kudaden da suke batarwa a kowace rana. Wannan yana nuni ga irin rashin adalci na manyan Arewa. To, ai sai ku kashe mu, sai ku ci gaba da mulkar duwatsu da tsirrai.

Daga Ishaka Bagwai Kano (ishaqb93@gmail.com)

ABIN BOYE YA FITO SARARI

Ina masu tababar hannun Kanwa Uwar Gami a tashin bama-bamai a Nijeriya? To, ina fatan dai kun ga bukatar Isra’ila ga gwamnatin Nijeriya, wai za ta taimaka a yi maganin Boko Haram. Tuni dama mun san su ne ke so su mamaye wannan kasar. Allah ya kara tona asirinsu

Daga Almujtaba Haruna (almujitabaharuna@yahoo.co.uk)

WACCE GUDUMMAWA KA BAI WA ALMIZAN?

Kada mu zama dutsen bakin ruwa mana, idan ba mu son ALMIZAN ta rika sanya tallace-tallacen wadansu, to mu kuma sai mu rika aika mata da tallace-tallacen namu mana? Misali mu aika da tallan ‘programe’ na da'irorinmu ko shagunanmu ko gidajenmu, sanarwar bukukuwanmu ko hidimominmu. Kuma ’yan uwa mu tuna, a bayan jaridar ma an ce “BA LALLE NE DUK ABIN DA KE CIKIN JARIDAR NAN YA ZAMA SHI NE RA'AYIN HARKAR MUSULUNCI BA.' Don haka ’yan uwa sai mu yi yunkurin tallafa wa Harkar yada labarai na Harkar nan, musamman ALMIZAN da sauran yunkurin da ya dace, irin su samar da gidan rediyo da talabijin mallakar Harkar Musulunci a Nijeriya. Wannan kuwa kule ne ga ’yan uwa; idan mun isa mu ce cas!

Daga Abdullahi Gambo Katsina

‘WAKAFALLAHUL MUMININAL KITAL

Na san kowa ya ga sakamakon mawallafin littafin nan na ‘Mutu'a Tarkon ‘Yan Shi'a.’ Tunda yanzu ga shi ya yi sabuwar wallafa ‘Tarkon Kwarto.’ Don haka masu yi wa Shi’a da ’yan Shi’a sharri sai su yi hattara, don kuwa “Wakafallahul mumininal kital.”

Daga Muhammad Sani Harbo 0706 649 7195

JINJINA GA SISTOCI MA’ABOTA WANNAN FILI

Ina kara jinjina ga Sistoci ma’abota wannan fili, saboda yadda suke yin rubutu mai ma’ana. Gaskiya sun cancaci yabo.

Daga Sayyid Suleja 0704 340 1233

MARABA DA WATAN FARIN CIKI

Alhamdulillah, maraba da Mauludi, Allah ya kawo mu watan da aka haifi Fiyayyen Halitta Manzon Tsira Muhammad (S), watan farin ciki ga dukkan al’ummar Musulmai, to amma kash! Sai ga shi wasu karnuka farautar makiya har sun fara haushi a masallacinsu sabila da kiyayyar da suke yi da wannan wata mai albarka. Up maulud! Up maulud!!

Daga 0705 732 3862

SAYYID ZAKZAKY MAGANIN RUDUN ZAMANI

Al'ummar Najeriya, Musulminsu da Kiristocinsu, sun zama tamkar kwallon kafa, ana buga su yadda aka ga dama. Amma da za su ringumi kiran Sayyid Zakzaky, da wallahi sun yi bankwana da duk wani rudu na wannan zamanin. Ba ku ga ’yan uwa ba? Ai ba su rudewa. Kun san dalili?

Daga 0805 636 0157

KU AMSA KIRAN SAYYID ZAKZAKY KAWAI

Kafirai fa kansu na hade ne, sashe na karfafa sashe, to haka ya dace (Musulmi) ku kasance, in kun ki kuwa, za ku watse, ku lalace, sai karfinku ya tafi a rinjaye ku. To, yaya kuke ganin kiran da Sayyid Zakzaky ke ta yi fiye da shekaru 30 na neman haduwar kan dukkan Musulmi gaba daya da umurnin Allah?

Daga Hajiya Fatima Fatimiyya Foundation Jos

GASKIYA ALMIZAN KUN BURGE NI

Gaskiya ALMIZAN ta burge ni, dubi yadda kuka dauko bayanin hadewar Izala bangaren Jos da Kaduna ba tare da son rai ba. Haka ake son jarida. Allah kara albarka.

Daga 0803 568 7311

WA YA TURO KU YIN KISA A MASALLACIN JUMA’A?

’Yan Kalaren Gombe wa ya turo ku yin kisa a masallacin Juma’a? Allah ya fallasa wadanda suke da hanu a ciki, amin.

Daga Adamu Muhammad Azare

SU WANE NE ’YAN SHI’A?

Imam Assadik (AS) yana cewa; “Su ’yan Shi’armu ana gane su ne da abubuwa guda uku. Yawan fara'a da (yawan) kyauta, da kuma yin Salla raka 51 a dare da yini. Ba sa haushi irin haushin kare, ba sa wuce iyaka su yi zalunci ko da za su mutu saboda yunwa”.

Daga Ibrahim Ahmad 0818 280 5587

NA GOYI BAYAN RA’AYIN SUNUSI LAMIDO SUNUSI

Ni dai a nawa rayin maganar Sunusi Lamido Sunusi a kan alfanun janye tallafin mai ya yi ne da kyakkyawar niyya, duk da ba na tare da shi a wannan bangaren! Ya ce; “Mu kasa ce da ke samar da mai, amma ya aka yi fiye da kashi 70% suna rayuwa kasa da Dala daya a rana? Sannan ya aka yi matanmu da yawa suke mutuwa wajen haihuwa? Don Allah mu yi nazarin wannan maganar. Daga Shamsu Kano 0803 747 3350.

MUNA DA YAKINI A KAN ABIN DA MUKE YI

Masu kai wa ’yan Shi’a hari kune ku kuka yi asara, mu burinmu ke nan, mu yi shahada, don mu muna da yakini a kan abin da muke yi, ku kuma ku tabbata a duniya!

Daga Musa Shukura Karmu Abuja 0805 393 1158

ZUWA GA SHAIKH AMINU DAURAWA

ALMIZAN don Allah ku tambaya mana Shaikh Aminu Daurawa wace irin annoba ce ’yan Shi'a da Shi'anci suka addabi kasar nan da ita? Ya fada mana cutarwa daya da ’yan Shi'a suke wa al'ummar kasar nan. Ai babu mummunar annobar da ta shigo kasar nan irin Wahabiyanci da Wahabiyawa, su suka rarraba zuwa kungiya-kungiya, su ke tayar da fitina a duniya. Daga cikinsu aka samu Alka’ida da makamantan su. Shi’a kuwa da ta shigo kasar nan ba ta kafirta Musulmi ba, ba ta halatta jininsu ba, ba ta kira zuwa ga rarraba ba, amma ta kira mutane ne zuwa ga hadin kai, sannan tana gwagwarmayar kwatar wa dukkan Musulmi ’yancinsu daga hannun azzalumai.

Daga 0706 353 8104

TABBATAR ALLAH NA TARE DA MU

Hasken da ya bayyana a Husainiya Bakiyyatullah, Zariya, tabbas yana nufin Allah na tare da mu. Allah ya bar mu da Sayyid Ibraheem Zakzaky.

Daga Musty Badawa 0805 424 0550

ANYA WANNAN BA WATA MAKIDA BA CE?

Menene ya sa sai a Arewa ne kawai kashe-kashe ya yawaita? Anya ba wata manufa ce ta daban na kokarin fada da Musulunci ko dakusar da Arewa ba?

Daga 0803 207 5124

WANNAN ITA CE MAFITARMU

Maganar da Sayyid Zakzaky ya yi a Kebbi kan yajin aikin da aka yi shi kadai ne zai gyara Nijeriya.

Daga Yusuf Karim Lamido Taraba 0813 915 1815

WA ALLAH (T) YA FI SO BAYAN ANNABI(S)?

Mala'ika Jibrilu ya zo wa Manzon Allah (S) da gasasshen tsuntsu, sai Manzon Allah (S) ya ce; “Ya Ubangijina ka zo min da mafi soyuwar halittarka mu ci wannan tsuntsun tare da shi”. Sai Imam Ali (AS) ya zo, kuma suka ci tare da shi. Ya kamata a daina damun mu cewa wai Manzo (S) Allah ya ce a mata ya fi son wance, a maza kuma wane. A ina ya fadi haka? Alhali Muslim ya kawo Hadisi Manzon Allah yana cewa; “Fatima bangare ne daga jikina”. Ya kuma ce; “Ni daga Ali nake, Ali daga ni yake”. Manzon Allah yana cewa; “Ni ina son wanda Allah yake so ne, kuma Allah ya fi son ni da Ali da Fatima da ’ya’yanta”. (Masabihus Sunna juz'i na daya shafi na 516).

Daga Huzaifa Abdullahi Wunti Street Bauci 0706 914 0703

INA JAMA’AR NIJERIYA?

Ba kudi, ba aiki, ba sana’a, ba karatu, ga tsadar rayuwa, ga ta da bama-bamai. Ina mafita? Mafita ita ce da’awar Sayyid Ibraheem Zakzaky.

Daga Rayyan Adam Iran, Kum +9893 621 85765

RANAR MAULIDIN MANZON ALLAH

An haifi Annabin Rahma Muhammad (S) mai ceton wannan duniyar ranar Juma’a 17 ga Rabi’ul Awwal, kuma abubuwan al’ajibi da yawa sun faru a wannan ranar kamar karyewar katangar Kisira da ta rushe da gumakan da suka kakkarye duk a ranar. Sannan an haife shi ne da hakora a bakinsa. Lallai wannan babban al’amari ne.

Daga 0808 279 9950

LALLAI WANNAN FIM DIN YA TSARU

Hasashen Goodluck Jonathan da ya yi na cewa akwai 'yan Boko Haram a gwamnatinsa da jami'an tsaro ya fito fili, an shirya wasan kwaikwayo. Shirin ‘kama’ Kabiru Sakkwato da ‘sakin sa’ da aka yi ya isa abin kallo. Tabbas Daraktan shirya wannan fim din ya Iya tsara shiri. Muna nan mun zura ido mu ga yadda za ta kaya a karshen fim din.

Daga 0807 576 0264

BA GA IRIN TA NAN BA

’Yan Nijeriya lokacin zabe kun bata lokacinku, kudinku da mutuncinku a kan wasu katti, wadanda ko kansu ba su gama sani ba. To, ga irin ta nan dai, kun ga sakayyar da suke muku. Sun talauta ku, sun hana ku hakkinku, kuma suna bin ku suna harbewa a gidaje da wajen harkokinku, suna tayar maku da bama-bamai a wajen ibadunku. Badi ma kwa kara!

Daga Zainab Aliyu Garo

ZAKZAKY ZALLA!!!

Soja ma sun kasa ruda shi, ’yan siyasa kwa yi kwa bar shi, yaudararku ba za ta rude shi ya biye maku ya kyale Allah ba.

Daga Shafi'u Lawal Layin Minista Malamfashi 0706 489 7151

SHAIKH SANI YAHYA JINGIR YA BURGE NI

Allah ya ganar da Malaman kasar nan da mabiyansu makircin Yahudu. Ina jinjina ga Shaikh Sani Yahya Jingir, wanda ya nuna ya fara ganewa.

Daga Usman S. Yola 0806 022 6936

MENENE KARAMCI NE?

Imam Ali (AS) ya ce, karamci shi ne bayarwa ba a tambaye ka ba, amma bayarwa idan an roke ka yakan zama daya biyu ne; imma dai don samun girma, ko don gudun zargi.

Daga 0818 685 6550

TALAKAWA ANA CUTAR MU A KASAR NAN

Mu dai talakawan Nijeriya mun zama kwallon kafa, Shugaban kasa ya harbo mu daga tallafin man fetur, sai ’yan kwadago suka tarbe mu suka yi ta juya mu har kusan kwana 10. Daga nan ba mu yi aune ba sai ga mu a ragar Yakowa awa 24 ba shiga ba fita. Daga karshe suka ruga, suka bar mu da zare idanu, ba wani mai tamakonmu.

Daga Kabiru Bade Mando Kaduna 0803 764 6491

ALLAH KA GANAR DA TALAKAWA

Ya Allah ganar da sauran 'yan uwana talakawan Nijeriya su fahimci da'awar Sayyid Ibraheem (H) don azzalumai su daina yi musu WUJU-WUJU.

Daga Baban Abba Garo

TALAKAWAN NAJERIYA KU GANE MAFITA

Janye tallafi ko barin sa ba shi ba ne mafita ba, a dai zurfafa tunani. Ya Allah ka kara wa su Malam Ibraheem Zakzaky lafiya.

Daga Umar Sabo 0803 318 2268

ALAMAR MUMINI 5 NE

Imam Assadik (AS) ya ce: "Alamomin mumini 5 ne: 1- Yin Sallah raka'a 51 a wuni (farillai da nafiloli). 2- Ziyarar arba'in na Imam Husaini. 3- Sanya zobe a hannun dama. 4- Bayyana Bisimillah a karatun Sallah. 5- Sanya kumatu a kasa idan ka gama Salla (ta’afir).

Daga Umar Maigatari Jihar Jigawa 0806 586 4763

ZUWA GA DAKTA AHMAD GUMI

Ina yi wa Dakta Ahmad Gumo barka da dawowa, kuma ina yi masa jaje da kamun da aka yi masa a Saudiyya. To, yanzu lokaci ya yi da za ka natsu ka yi tunani, ka sa hankali ka tuba da abin da ka shuka a nan kasar wanda ka girba a Saudi Arebiyya. Yanzu ka dawo za mu zauna da kai a nan kasar. Da mu da kai duk mafitarmu tana ga da’awar Sayyid Zakzaky.

Daga 0703 960 8605

KIRANA GA 'YAN UWANA MATA

Kirana ga 'yan uwana mata shi ne mu zage damtse, mu tashi tsaye mu duba yadda muka yi sake har 'yan uwanmu Burazu suka yi mana fintinkau ta bangarori da dama. Gaskiya wajibi ne mu farka daga dogon barcin da muke yi mu fadada tunaninmu, musamman ta wajen rubuce-rubuce a cikin wannan jarida mai farin jini (ALMIZAN), ko kuma dai mu ba mu da abin cewa ne? Rokona a gare mu shi ne mu farka daga dogon barcin da muke yi mu fadada rubutunmu don kuwa gari ya waye. Daga Shamsiyya Murtala Funtuwa

WAI SAI KANA DA KUDI ZA A BA KA AURE?

Ina mamakin wani abu da ya fito cikin ’yan uwa, wai sai kana da kudi za a ba ka auren Sista, amma in ba ka da kudi, ba za a ba ka ba. Shin ba ku sani ba kudi na Allah ne, talauci na Allah ne? Don Allah don Annabi ’yan uwa mu shiga taitayinmu, mu gyara dabi'unmu, kada mu sake abin duniya ya rude mu. Mu bai wa kyawawan dabi’u, tsoron Allah da riko da Harka Islamiyya muhimmanci fiye da komai.

Daga Yunusa Umar Afakallah Jaji 0803 624 6071

MU BI SHI KAWAI MU SAMU MAFITA

Allah Sarki Sayyid Zakzaky ya yi gaskiya, duk abubuwan da ya fada sai ga shi suna ta bayyana. Ya al’ummar Nijeriya mu zo mu bi shi don mu samu mafita duniya da lafirarmu. Tunda kun gwada CPC ba ta kai ku ba, kun gwada labour ba ta kai ku ba, to ku gwada da’awar Sayyid Zakzaky mana.

Daga 0708 530 1822 da 0803 099 8678

GWAMNATINSA ’YAR BOKO HARAM CE

Mutanen Nijeriya dai yanzu mun gane, tunda ta bayyana karara Jonathan ya ce gwamnatinsa ’yar Boko Haramu ce.

Daga Ashafa M. Lawwali Shinkafin Zamfara 0816 001 2920

ZUWA GA MASU AUKA WA ’YAN UWA A GOMBE

Ina kira ga ’yan Kalare da ku ji tsoron Allah, domin abin da ake ba ku kuna yakar ’yan uwanku Musulmi a Gombe zai kare, kuma za ku hadu da Allah ranar sakayya.

Daga Lawan Bala Gogori 0704 424 4121

AN GAISHE KU NA ZAKZAKY MASU KWANA SALLA

Gaskiya wadanda suka yi koyi da Sahabbai da Iyalan Imam Husain (AS) wajen tattaki daga yankuna kamar Bauci, Kano, Kaduna da sauran wurare zuwa taron Arba'een na Imam Husain a Zariya, sun cancanci matukar yabo da godiya. Domin abin da suka yi ya kara tabbatar mana da cewa Sayyid Zakzaky hakikanin Jagora ne, wanda rashin sa asara ne har ga marasa Salla. Ya kuma kara mana yakinin cewa Sayyid Zakzaky yana da zaratan Almajirai masu masa biyayya domin daukar fansar kisan da aka yi wa Imam Husain da sauran Imamai (AS). Allah ya ba mu sabati ya kare mu.

Daga Umar Hasan Gololo 0803 069 3615

HARIN BOM BA ZAI RAUNANA HUSAINAWA BA

Tashin bom a Iraki, Iran, Siriya, Somaliya da Nijeriya duk aikin Turawa ne, kuma ba zai raunana gwagwarmayar Husainawa ba, in ji Sayyid Hasan Nasrallah na Lebanon.

Daga Yusuf Hamza Ibrahim 0703 931 2332

TUNANIN TARON ASHURA NA SHI’A NE?

In mutum Musulmi ne sai ya kalli taron Ashura, sai ya yi tunanin na wadansu mutane ne sunansu Shi’a, to sai mu ce ya binciki imaninsa. Domin abin da yake cewa shi ne wadannan mutanen su ne magoya bayan Annabi Muhammadu Manzon Allah (S), amma shi ba ya goyon bayansa ke nan. Eh mana! Saboda haka in dai har mutum mai imani ne da addini ya dame shi, ya kamata ya sake duba zuciyarsa.

Daga Muhammad Sani Yaregoma Azare Layin Mai Kaulasan 0705 991 1360

HABA BURAZU DA SISTOCI!

Haba Burazu da Sistoci! Yanzu kun koma kuna zargin juna a kan bidar aure, har kuna komawa ga Amawa? Shin da haka za ku kawar da azzalumai? Tsarki ya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda shi rayyaye ne ba ya mutuwa. Ku sani fa addini ba shi tabbata sai da al'umma ta gari, kuma al'umma ta gari ba ta samuwa sai da iyali ta gari. Na taba jin Sayyid Zakzaky (H) ya ce; “Auren Ba’ammiya hadari ne a Harka”. Kamar yadda kuma auren Ba’ame shi ma yake da nasa hadarin.

Daga Jibreel Gimba, Jihar Nasarawa 0703 850 2147

KARKU MANTA DA HADISIN ANNABI (S)

ALMIZAN ku fada wa Malamai masu boye gaskiya a kan al’amuran addini, Manzo (S) yana cewa; “ASSAKITU ANIL HAK SHAIDANUN AKHR”.

Daga 0805 389 1084




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan