A Takaice kai Tsaye: Na Aliyu Saleh, Ta GSM: 0803 698 3947
KU DAINA YI WA MUSULMI SHARRI
Kana Musulmi amma kai burinka a kullum yaya za ka yi ka ga bayan Musulmi dan uwanka? Ba za a ji wani alheri a bakinka ba a kan Musulmi sai sharri. Ya kamata ka yi wa kanka fada, ka san cewa Musulmi dan uwan Musulmi ne.
Daga Ibrahim Danladi Guy Zariya
KU BINCIKO MANA AMSAR TAMBAYAR
ALMIZAN, ku binciko mana amsar wannan tambayar da aka yi wa Abubakar Gumi, ta cewa ina hukuncin wanda ya mutu hannun arna? Kuma don Allah ku gaya wa ’yan Izala sune ba su saba da dauri ba.
Daga Sirajo Gusau 0808 351 2131
GOODLUCK IN KA GYARA ZABE…
Goodluck in ka gyara zabe, sai kuma ka gyara wadanda za a zaba, ko?
Daga Al-kazeem Gezawa.
WAMAKKO YA SAKE DAWOWA RUWA
Wamakko yanzu da yake ka ga zaben 2011 ya gabato, shi ne ka dawo da wancan tsohon makircin naka kuma. Don na ga ka haukace da kame-kamen ’yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) a jihar Sakkwato. Ka sani an gano ka, kuma za ka sha mamaki a zaben 2011 insha Allah, sannan za ka san jiya ba yau bace.
Daga Iliyasu Bali.
ZUWA GA GWAMNA DANJUMA GOJE
In dai ana maganar aiki, ko makiyinka dole ya jinjina maka. To, amma maganar hanyar Kinafa, tana son ta zama gagara-badau ne? Mu fa marayu ne, kai ne uba a gare mu. In har ba mu samu a zamaninka ba, sai dan buzunmu.
Daga Sulaiman Adamu (Sallaman Kinafa)
MU GUJI TAIMAKA WA AZZALUMAI
’Yan uwa, mu guji taimaka wa azzalumai ta kowace hanya, mu tuna Hadisin Safwan tare da Imam Kazim (AS) dangane da taimakon azzalumi ko son rayuwarsa. Imam ya ce: Ya Safwan komai naka mai kyau ne, sai abu daya. Sai ya ce, wane abu ne? Sai Imam ya ce da shi hayar rakuma da yake bai wa azzalumi, wato Haruna Rashid. Sai ya ce da Imam ba yana ba shi bane don sharri ko barna, ko don farauta, ko don wasa kawai, yana ba shi ne don ya je aikin Hajji. Sai Imam ya ce masa yana so ya dawo ya biya shi? Sai ya ce, na’am, sai Imam ya ce masa duk wanda yake son wanzuwar azzalumai, to yana daga cikinsu. To, ina kuma ga wanda ya taimake su a kan zaluncinsu da addu’a. Imam ya ce, duk wanda ya zamo daga cikinsu, to ya gangara wuta. Allah Ya tsare mu, amin.
Daga Rayyan Adam Dan Marke Makoda 0703 594 3360
INA ZA MU SAMU TAHFIZ TA KWANA?
Don Allah ALMIZAN ku gaya wa ’yan uwa, mu mutanen kauye muna son makarantar haddar Alkur’ani ta kwana, domin mu ba mu da wadataccen ilimi a kauyuka. Muna son ’ya’yanmu su tashi da karatun Ahlul Baiti. A taimaka inda wanda ya san akwai wanda ya san wata tahfiz ta kwana, to ya sanar da mu.
Daga Musa Kallamu Kano Gezawa Gammawa 0813 466 3938
DALILIN TAKURA WA ’YAN UWA NA SAKKWATO
’Yan uwa na Sakkwato sun yi nasara da dukkan ma’anar kalmar. Duk da yake cewa waki’ar Sakkwato ta riga ta faru, kuma ta fara kwaranyewa, har kullum laifin ’yan uwa shi ne soyayyarsu da Allah (T), Manzo (S), Ahlul Baiti (AS) da Muminai. Illa iyaka. Ba su takura masu ba, sai don sun yi imani da Allah Mabuwayi, abin yabo.
Daga Rabi’u (Kurma) 08087961473
DA KITAB WAS SUNNAH MUKA DOGARA
Zuwa ga dan uwana a Musulunci, Abu Mus’ab! Yana da kyau idan ba ka san abu ba kada ka yi saurin yanke hukunci da cewa Shi’a ba gaskiya bane. Ina ba ka shawara ka dauki littafan Shi’a ka karanta, ka kwatanta da abin da kake a kai yanzu ka zabi wanda ya fi daidai, ka bi tsakaninka da Allah. Sannan ka sani ba a yanke hukunci bisa jahilci. Ka lura ka gane cewa dubban jama’ar da ke Shi’a ba an haife su ’yan Shi’a bane, sun karanta ne suka fahimci cewa ashe ta samo asali ne daga Sahaba da Iyalan Gidan Manzo tsarkaka. Dogaronmu Kitab Was Sunnah.
Daga Muhammad Sani Tela Dandume 0808 211 2266
SHAWARATA GA MASU SUKAR MUSULMI
Masu kirari da AHLUS SUNNAH, me ya sa ba ku da abokan gaba sai wasu bangare daga cikin Musulmi? Ku duba rayuwarku ku kwatanta ta da rayuwar munafukan zamanin ANNABI (S), ku ga ko akwai wani bambanci da taku. To, ni dai shawarata gare ku shi ne, ya kamata ku yi wa kanku nazari, ku gane, ku daina gaba da kuma daura damarar yaki da masoya AHLUL BAITI (BABBAN GIDA) da wasu bangare kuma na Musulmi. ALLAH (T) Ya sa mu gane.
Daga Sabi’u Dahir Ungwar Zariyawa, Suleja, jihar Neja 0805 915 1991
BA A MUBAHALA A TSAKANIN MUSULMI
ALMIZAN don Allah ku gaya wa mai sakon kalubalenku ’yan Shi’a; cewa ba a yi wa ’yan Shi’a kalubale. Kodayake don dan firamare ya kalli Farfesa ya ce masa kai ba ‘teacher’ bane, babu mamaki. Mu dai ba ma mukabala, kuma mun ga amfanin hakan! Don kuwa mun ga wasu suna yi, a karshe babu wata natija da suke samu. Mubahala kuma ana yi ne tsakanin Musulmi tsantsa da wadanda ba Musulmi ba. To, mu a wurinmu ku Musulmi ne, da wa za mu yi!? Haba Abu Mus’ab a dai yi ta karatu da kokarin fahimtar karatun da kyau.
Da a Umar Abdullahi Sakafa, Suleja. 0703 182 6672
BANA A INA ZA MU JI MURYARKA?
ALMIZAN, don Allah ku tambayar min Shaikh Gabo, bana a wane gidan rediyo za mu saurari barambaramarsa? Bara mun ji a Kaduna, ko bana ba hali? Allah Ya bar mu da Iyalan gidan Manzo (S).
Daga Salihu Abdurrahman Abubakar Shanono.
’YAN UWA MU ZAMA ’YA’YAN MALAM NA HALAS
Don Allah ’yan uwa mu zama ’ya’ya na halas. Kowa ya ji ran Maulidin Fatimah (AS) yadda Sayyid (H) ya yi jawabi kan hakkin mata da yadda za a zauna da su. Kuma lalle ya kamata mu canza. Sannan Sistoci ya kamata su tuna maganar Imam Ali (AS) da ya ce kishin mace zindikanci ne. Burazu don Allah duk mai halin kara aure, ya kamata ya kara don a taimaka ma Musulunci.
Daga Abu Muhammad Mani.
MASU SHIRYAWA ’YAN SHI’A KULLE-KULLE
Masu shiryawa ’yan Shi’a kulle-kulle kun makara, duk kulle-kullen da za ku kulla da karairayin da za ku yi ba zai cutar da Shi’ar Ahalul Baiti da komai ba. Duk abin da za ku yi, wasu sun yi kafin ku, babu abin da za su fada da wasu ba su fada ba, ko kun manta irin kokarin da Dakta Ahmad Gumi ya yi a shekarar da ta gabata wajen kawo karshen Shi’a da ’ya’yanta? Sai ga shi yanzu ya zama abin ban tausayi. Don haka Malaman da suka halasta jinin ’yan uwansu musulmi ku yi hattara da taka-tsantsan.
Daga Al-kazeem S. Musa Alhasan Fudiyya U/ma’azu Kaduna 0806 274 0226
BAN GANE MA’ANAR HORON DA IZALA KE BAI WA LIMAMAI BA
Ni ban gane horarwar da Izala ke wa Alkalai da Ladanai da Limamai ba. Don na ga a Ladanai masu barna a ladanci sun fi masu yi daidai yawa, ga gyaran kurakuran a Izziyyah da wani kaset na Marigayi Maishafi (RA), amma duk da gwarzanta horarwar da ake yi, sai ka rasa wa aka horar. Da wani ne ya ba dan sallama biyu ’yarsa da ya haifa da ka ji hayagaga.
Daga Abdu Bello Mai Alfanu Bishiyar Shayi, ’Yankwalli Jos (josrisawa22@yahoo.com)
WAMAKKO KA JI TSORON ALLAH
Wamakko ka ji tsoron Allah, ka sani akwai hisabi, akwai wuta, sannan akwai mutuwa. Ka sani hukuncinka zai yi daidai da aikinka.
Daga Ibn Aliyu Guri 0708 334 7727
…AI WAMAKKO BAI SAN ALLAH BA
Na ji wasu suna kiran Wamakko wai ya ji tsoron Allah. Ai shi bai san Allah ba. Shi mutane yake jin tsoro. Ko ba ku ji inda Allah Yake cewa su ba tsoron Allah suke ji ba, ku suke jin tsoro? Ku bar shi duk abin da zai yi, wallahi ba zai maimamata abin da ya yi a baya ba.
Daga Nura Rogo 0808 785 9333
RIGAKAFIN KAMUWA DA CUTAR ZUCIYA
’Yan uwa kada mu yi butulci bayan Allah Ya lullube mu da rahamarsa, mu sani fa fahimtar kiran nan da Malam Zakzaky yake yi falala ce daga Allah, wanda ya yi mana ba don mun fi kowa ba. Me ya sa muke sakaci da falalar da Allah Ya yi a gare mu? Abin da yake damu na dangane da wasu ’yan uwan shi ne yadda aka wayi gari sakacinmu da rashin neman kusanci da Allah har ya kai mu ga sukar juna da aibata juna. Tsarki ya tabbata ga Allah! ’Yan uwa kada fa a shagala da cewa addini muke yi. Me ya sa muke kokarin kore wasu daga cikin Harkar nan tunda Maulanmu bai yi haka ba? Sannan wane dadewa ko matsayi muke son mu samu idan har mun fitinar da wasu sun bar Harkar nan? Yaya za a yi Malam yana gini, mu kuma muna rusawa? Don rigakafin kamuwa da irin wannan tunanin ka nemi kasetocin nasihohi ga ’yan uwa na Shi’a/Sunna, Fitina Tawayiyya, Abincin Ruhi da aikata abin da aka ji daga wajen Malam, zai taimake mu.
Daga Abdullahi Gambo Katsina 0803 282 6097
KWANAKI 40 NA RASUWAR SAYYID FADLULLAH
Ka zama dalibi mai gane isdilahohi a makarantar Ahlul Baiti, wannan kadai ya ishi mutum alfahari, kuma abin kwatance a duniyar Musulunci, domin fahimtar zantukan Ma’asumai da gane ayyukansu a matsayinsu na masu tarjamar wahayin Annabci, balle har mutum ya taka matsayin Malanta ya isa ga matsayin Ijtihadi da Marja’iyya, wadanda ke mai da mutum ‘kas’ daga al’umma Mumina, musamman irin shi Marigayi Sayyid Husaini Fadlullah, wanda mumbarinsa na Juma’a ya yanke hannun ’yan mamaya, haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka daga babban birnin kasar Labanon, Beirut. Sannan ya samar da dandamali na tattaunawa da fahimtar juna tsakanin al’ummar Labanon, musamman su wadanda suke ’yan tsiraru da kiristocinsu mafiya rinjaye, bayan nasarar hada kan Musulmin Sunna da Shi’arsu wadanda ya kawo haihuwarsu a karkashin tuta guda ta Hizbullah da irin wannan aiki ya shahara da ma’abocin kira zuwa ga fahimtar juna. A yayin da yake cika kwanaki 40 da rasuwa muke rokon Allah Ya gafarta masa.
Daga A. A. Gama 0808 413 6819
AFUWA GA MAKIYI
Imam Ali (AS) yana cewa: “Idan Allah Ya ba ka iko da fifiko a kan makiyinka, to ka yi masa afuwa, ita ce godiyarka ga Allah wanda ya kaskantar da shi a kanka.”
Daga Sakina Umar Aliyu Rigasa Kaduna
YAUSHE ZA KU GWADA TSARIN MUSULUNCI?
Haba ’yan Nijeriya! A 1999 zuwa yanzu kun gwada tsarin karba-karba a matsayin wata Mazhaba daga cikin Mazhabobin dimokradiyya. A da can kuma kun gwada “kwata-kwata”, wato mulkin soja, duk babu wanda ya hada kan kasa daga cikin wadannan tsare-tsare, alhali ga mu da tsarin Musulunci addinin da ya hada kan Larabawa ya daukake su suka zama ’yan uwan juna a lokacin Manzon Rahma (S). Da shi ne kuma Shehu Dan Fodiyo ya ’yantar da talakawan mafi girma daga yankunan Nijeriya ta yanzu daga kangin zaluncin Sarakuna a karni na 18, Imam Khumaini kuma ya ’yanto kasar Iran daga danniyar yammacin Turai a karni na 19. To, wai sai yaushe ne hankalin ’yan Nijeriya zai dawo a kan tsarin Musulunci, domin samun waraka ta dindindin a duniya da lahira?
Daga Salisu T. Gaiwa 0703 339 9834
SUN YI WA MATAR YAKOWA KABBARA!
Kungiyar Mata Musulmi sun yi abin kunya, wai sai ga ’yan kungiyar ‘Woman in Da’awa’ a gaban arniya matar Gwamnan Kaduna Yakowa, lokacin tana jawabi suna mata kabbara! Ko sun manta kabbarar da suke yi sunan Allah suke fada? Ashe kuwa ya kamata su kiyaye.
Daga Jamilu A Haruna Rafin Guza Kaduna 0802 980 5554, 0703 165 9493
SISTOCI TARO KUKE ZUWA KO DAI KASUWANCI?
An ware mu nesa da su Malam (H) a lokacin Maulidin Manzo (S) saboda hayaniyarmu, amma maimakon mu canza sai kuma a Shuhada su Malam na jawabi mu kuma muna kasuwanci. Anya taron addini muke zuwa, ko kuwa dai kasuwanci?
Daga Sadiyya Bello S. Gwarzo.
MALAMAN SAKKWATO ALLAH YA ISA
Abin da zauna-gari-banza ke yi a Sakkwato da sunan Sunna kuna ji kuna gani kun kyale. Kun sani abin da suke ba ya kama da Sunna. Wallahi sai Manzo (S) ya tuhume ku a kan mashaya, ’yan iska wadanda ko Salla ba su yi, suna yadda suka ga dama da sunan Sunna, kuma kun yi shiru kuna ma goyon baya. Ku tanadi amsar da za ku fada gobe kiyama.
Daga Dan Sunna sak ba bidi'a. 0803 803 9863
KOWA YA YI DA KYAU YA SANI!
Na ji maganar da kika yi Malama Ikilima, wai me Wamakko ya yi wa ’yan Shi’a suke ce masa Barawon Akuya? Sai in ce maki ki bincika. Kuma kina cewa duk wanda ya ce masa Barawon Akuya, Allah Ya tsai da shi ranar shaida. Sai in ce maki, amin. Mu kuma Allah Ya yi mana sakayya a kansa.
Daga Abdul Hamid Namadobi 0703 367 4602
IKLIMA KIN SAN WAYE WAMAKKO?
Malama Ikilima Muhammad ban san ko a Sakkwato kike da zama ba, da sai in ce maki ki nemi wanda ya san Wamakko sosai ki tambaye shi ya fada maki ko da gaske ne Alu din ya taba satar akuya? Za ki ji gamsasshen bayani daga gare su. A’a ba Gwamna bane shi, idan da karya ake masa ai da ya kai kotu ya ce an bata masa suna kamar yadda ya kai jaridar ALMIZAN kara a wata kotu a Zariya a shekarun baya yana neman ta biya shi Naira miliya 50 saboda wani labari da ta buga a kansa, wanda Lauyansa ya ce na batanci ne a gare shi. Ko kuma da ya shiga kafafen yada labarai ya ce sharri ake masa, ko dai wata hanyar da zai iya kare kansa, wanda duk ya mallaki hanyoyin yin hakan. Amma me ya sa bai yi ba? Ai ya kamata ki tambayi kanki ne. Amma in abin ki bincika ne, Alu ba dan goyo bane, ya wuce duk inda kike zato, kwallo ne shi na kin karawa. Ina ma dai za ki tsananta bincke.
Daga Abdurrahman M. Gulfegany 0808 677 1522
MACE MA’AIKACIYA
Manzon Allah (S) ya ce, “mafi alherin matanku ita ce mai haihuwa mai suturcewa, mai kamewa, madaukakiya a cikin danginta, mai kankantar da kai ga mijinta, mai tabarruji ga mijinta, mai katange kanta ga waninsa, wadda take jin maganar mijinta, take bin umurninsa, wadda idan mijinta ya kadaitu da ita, sai ta ba shi abin da ya bukata a gare ta. Wannan ma’aikaciya ce daga cikin ma’aikatan Allah wadda ba ta tabewa kuma ba ta nadama”.
Daga Ahmad Sulaiman Babura 0806 077 3772
WA YA CE WAMAKKO BAI SACI AKUYA BA?
Malama Ikilima kin fada cewa duk wanda ya ce Wamakko ya saci akuya Allah ya tsai da shi ranar shaida, to, shi kuma wanda ya ce bai sata ba Allah ya tsai da shi tare da Wamakko a ranar lahira.
Daga Maryam Dalhatu ’Yankara 0813 323 7374
YAUSHE AKE YIN AYYUKA?
Kamar yadda Salla take da lokacin da ake yin ta, haka ma karance-karancen addu’o’i biyan bukata suna da lokutan da ake yin su. Wato ba koyaushe ake yin addu’a a kan neman muhibba ba, ko addu’ar neman arziki, ko ta halaka azzalumai. Abin nufi a nan shi ne kowace addu’a akwai lokacin da ya dace a yi ta. Sanin haka shi ma wani ilimi ne na musamman mai zaman kansa.
Daga Malami Bello B/kebbi 0708 978 7377
ME YA SA BA ZA KU HADA KAI BA?
Ina masu cewa ba za su hada kai da ’yan uwansu Musulmi ba? Ga wani misali. Mu kaddara cewa ga wasu mutane ’yan uwa daya uba daya, sai suka samu kansu a wata sahara suna kokarin gano hanyar gida. Sai ya zama wasu a cikinsu sun gano hanyar, amma sai suka kawa gida abin su. Shin don Allah idan wadannan ’yan uwan nasu suka halaka laifin waye? Ko kuwa hakan zai faranta ran iyayensu. Haba ’yan uwa Musulmi mu yi wa kanmu hisabi mana.
Daga Sabi’u A. Mai Tsidau 0806 750 1161
MU DAINA KARYA ’YAN UWA!
In ba ka ji daga Malam ba, kar ka ce Malam ya ce don kaucewa hadarin duniya da lahira.
Daga Muhammad Sani A. A. Mai Magani Da Ikon Allah, Nasarawa, Kaduna.
KARA FARASHIN KAYA A WATAN RAMADAN
Watan Ramadan, watan ibada ne, watan neman gafara da ceto ne, watan da Allah yake amsar addu’ar bayinsa ne, watan da bayin Allah suke shiga wata sabuwar rayuwa, ba sa kaunar su ga watan ma ya kare. To, amma su wasu ’yan kasuwan namu alla-alla suke watan ya zo su karama kaya farashi. Da kamata ya yi ma idan kaya ya tashi, to su sai su sauke farashinsa saboda alfarmar watan Ramadan. To, su wasu suna ga lokacin arzikinsu ne ya zo, idan ba su kara farashin kayansu ba a watan Ramadan, suna ga makamar ba za su yi arzikin bane, idan ya wuce. Allah Ya ba mu albarkan da yake cikin wannan wata. Daga Aliyu Suleja 0803 225 0162
KIRA GA MALAMAN KASAR NAN
ALMIZAN, don Allah ku sanar da Malaman kasar nan da cewa, tafsirin Alkur’ani ba abin wasa bane. Don haka ina kira ga duk wanda zai yi tafsirin ya rinka fassara Alkur’ani ba da son ransa ba.
Daga Isma’il Kabir K/Kudu Malumfashi
GABA DAI-GABA DAI ALMIZAN
ALMIZAN makaranta, manazarta, matserar masu neman gaskiya. Fada gidan ban kashin azzalumai, garkuwa ga raunana, zuma ga zaki ga harbi, ‘A-L-M-I-Z-A-N’ (A). Allah ne madogararku. (L). Lillahi wa Rasulihi kuke yin aikinku. (M). Mizaninku (Ma’auninku) gaskiya. (I). Islam (zaman lafiya) ne manufarku. (Z). Zakzaky (H) ne Jagoranku. (A). Azzalumi ne makiyinku. (N). Nagarta ce tushen nasararku. Na kara da cewa jarida don kwatar hakkin raunana. Kuma “Allah zai cika haskensa ko da azzalumai sun ki.”
Daga Muhammad Saminu Hamza Kademi, Halkar Fagge Kano 0808 440 8509.
’YAN FUDIYYA MALUMFASHI, KUN CANCANCI YABO
’Yan Fudiyya Malumfashi, kun cancanci yabo, kun zamo farin cikin al’umma gun fareti, karatu, tarbiyya, sakafa, hazaka, gun Muzaharori ku ake bi da jinjina. Na taya ku murnar cin nasarorin da kuke samu musamman na baya-bayan nan; jinjina ga M.S.A Malumfashi hedimasta na Fudiyya..
Daga Sanusi Malumfashi, Mariga, jihar Neja.
GASKIYA ABIN DA KUKA YI BA KU KYAUTA BA
Wani ya turo maku sako kun buga yana tuhumar Shi’a karya ce, ya ce a zo a yi mukabala ko mubahala. Ni kuma na turo sako na yi mubahala da shi, amma kuka ki bugawa. Kuma duk ALMIZAN sai na duba, amma ban ga kun buga ko da na wanina ba kan tuhumar da ya yi. Shin abin da ya rubuta kuna nufin gaskiya ne kenan? Kuma sai da kuka turo man sako sau 2 kuna cewa in kara turo sakona, amma kawai kuka sa na bata kudina. Ni na yi sallama da ku.
Daga 0708 109 1238
DUK WANDA YA YI RUBUTU MAI MA’ANA ZA SU BUGA
Ban san me ya sa ’yan uwa mata ba sa yawan rubutu a jaridar ALMIZAN ba, duk da kuma suna da hikima da fasahar da in sun yi rubutu yakan yi tasiri. Misali na kusa shi ne rubutun Nusaiba Abubakar, ya yi ma’ana. Don haka Sistoci a kara motsawa a rinka gogayya da ku a fagen rubutu. Su ALMIZAN duk wanda ya yi rubutu mai ma’ana, za su buga.
Daga Akilu Zariya
TSUNTSIN DA YA JA RUWA....!
Allah Sarki! Ana Ramadan mai kisan kiyashi ba ya nan, mai tafsidin a gama da ’yan Shi’a ba ya nan, ba tafsidin. Tsuntsun da ya ja ruwa......!
Daga Umar Gaide Hadeja
SHAWARA GA MALAMAI
Malamai masu tafsirin cikin Ramadan, a yi tafsiri na gaskiya da zuwa ga bin dokokin Allah da Manzonsa da halaye masu kyau, kuma zuwa ga hadin kan Musulmi. Kar ku bari tafsirinku ya koma tafsidi da kuma sukan juna da yi wa juna sharri da hassada.
Daga Abdulhakim Assamawiy Ilorin, jihar Kwara.
KAI KUMA DA WACCE KA ZO?
Magajin Dakta Gumi, Shaikh Alhasan Hasan Jos, ko da me ka zo kai kuma? Muna sauraron ka.
Daga Idris M. Yunusa Garko 0708 276 1772
WAIWAYE ADON TAFIYA ALMIZAN
Allah ya kara kare ki daga makiyanki na zahiri da badini. Kuma ina taya ku murnar cikar ALMIZAN shekara 20 da kafuwa, kuma don Allah idan da hali ku buga hoton ALMIZAN ta daya da ta biyu da ta makon kama Malam, domin ya zama waiwaye adon tafiya.
Daga Sani Umar Garko
BAN DA SATAR AKUYA YA AIKATA WASU MIYAGUN HALAYEN
Ikilima, aikin da Alu ya yi na rashin arziki shi ne dalilin yin bincike a kan rayuwarsa. Har aka gano cewa kurciyarsa babu kyau. An kuma gano lalle ban da satar akuya, to akwai wasu halaye munana da ya aikata a rayuwarsa. Da fatan ke ma za ki bincika. Allah Ya taimaki mai gaskiya.
Daga Nasiru Bello Kaura Namoda.
MUN FAHIMCI HADISIN: “ADDIBUW AUALADIKUM” KUWA?
Anya ’yan uwa mun fahimci Hadisin: “Addibuw aualadikum” kuwa? Domin a gaskiya ba ma bai wa ilimin ’ya’yanmu muhimmanci! Shin mun shirya amsar da za mu gaya wa Allah da Manzonsa a kan umurnin da suka ba mu a kan mu yi wa ’ya’yanmu tarbiyyar son Manzo da son Iyalansa da kuma karatun Alkur’ani? Ashe ba Fudiyyoyi bane cibiyar addibuw aulaadikum ba? To, wallahi idan ba mu shiga taitayinmu ba, za mu yi shari’a da ’ya’yammu a gobe kiyama! Ko muna zaton za su koya a gari ne?
Daga Yakub Lawal Ingawa 0808 665 7330
IN DA GASKE NE ANA TAUSAYIN TALAKA…
Yana da mutukar muhimanci ’yan kasuwa su rangwanta farashi da Azumi musamman kayan masarufi. In da gaske ne ana tausayin talaka, to gwamnati ce za ta sayo kaya ta karya farashi yadda za a sayar a kasuwa, sannan ta ba ’yan kasuwa sari yadda su ma za su ci riba. Ta haka ne kowa zai amfana maimakon a yi ta surutun ’yan kasuwa sun ki su taimaka, bacin su ma ba wanda ya taimaka musu. Gwamnati ce da alhakin saukakawa talaka ta hanyar amfani da dukiyar da Allah Ya hore mana a wannan kasa.
Daga Muhamma M. M. Sa’id
HAPPY SHAHRU RAMADAN KAREEM
Barka da shiga watan rahma da kira ga liyafar Ubangiji. Imam Ali (AS) ya ce: “Ya Manzon Allah (S), meye mafi kyawun aiki a watan nan? Sai ya ce: “Tsoron Allah da barin haram.” Da fatan za a sa Maulanmu Sayyid Zakzaky (H) da ’yan uwa cikin addu’a. Happy Shahru Ramadan Kareem.
Daga Ibrahim Bello 0803 049 8698
Shafin Farko
|