Rahotanni

Iyalan Sayyid Zakzaky (H) sun ziyarci Marigayi Sarki Muhammad Sambo Hadeja

Daga Awwal Ashir

A ranar Lahadin da ta gabata 1 ga Agusta 2010, Sayyid Muhammad, Ahmad da Hammad, ’ya’yan Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) suka kai ziyara zuwa kabarin Marigayi Sarki Muhammad Sambo Hadeja, wanda ya yi shahada bayan arangamar sa da Turawan mulkin-mallaka, a makwancinsa da ke cikin kauyen Mairakumi a Karamar Hukumar Mallam Madori mai nisan kilomita 21 daga masauratar tasa da ke Hadeja.

An gabatar da addu’o’i na musamman ga Marigayin, yayin da Sayyid Muhammad ya yi fatan rahama gare shi, sannan ya roki Allah ya yi wa masu buya a bayan sunan Marigayin suna aikata fasadi jaza’i.

Baya ga wannan maziyartan da ma wasu al’ummar garin sun nuna matukar alhininsu dangane da makwancin Marigayin, na rashin kulawa da bai wa wajen muhimmanci a hukumance, ta yadda duk wanda ya ga wurin ba zai taba zaton cewa bil’adama ne a kwance a gun ba, balle a ce Sarkin Musulmi ne guda.

Da yawa sun shaida mana cewa sun sanar da hukumomi a kan a gine wajen a yi hanya wadda za ta kai maziyarci wajen ba tare da ya sha wahala ba, amma al’amarin ya ci tura.

Alaramma Malam Haladu shi ne wanda kabarin yake cikin gidansa, ya shaida mana cewa shi dai ya zo ya sami kabarin a wajen tun yana daji, shi ne ya gina gidansa a wurin ya ci gaba da kula da shi har zuwa yau. Mun tambaye shi ko akwai wata kulawa ta musamman da ya samu daga hukuma? “Ni nake kulawa da wurin, amma yanzu sun dauke ni aiki ne suna ba ni albashi. Ta fuskacin gurin kuwa sun yi masa rumfar kwano wannan da ka gani”

Da yake karin haske dangane da karamomin kabarin, ya nuna tun da can ana ganin wani haske yana tashi a wurin, amma yanzu ba a gani.

Ita dai wannan ziyara ta biyo bayan kaddamarwa da aka gabatar ne a garin na Mallam Madori a ranar Asabar, na kaset din fim din rayuwar Imam Khumain (KS) mai suna “Ruhullah”, wanda aka tarjama shi zuwa harshen Hausa, kuma Sayyid Zakzaky (H) ya kaddamar da shi a ranar mata ta duniya (Mauludin Zahra (AS)) na bana, yankin ’yan uwa na Mallam Madori su ma suka shirya suka gabatar, an kuma tara Nairori masu kauri duk da yanayin damina da ake ciki a yankin.

An yi taron baje kolin abubuwan da suka ta’allaka da Alkur’ani

Daga Shu’aibu Muhammad Qum, Iran

A ranar Asabar din da ta gabata 7/8/2010 aka bude kasuwar baje kolin abubuwan da suka ta’allaka da Alkur’ani mai girma karo na 18 a Iran.

Shi dai wannan taron baje kolin ana gabatar da shi ne duk shekara a cikin babban birnin Iran, wato Tehran a karshen Sha’aban zuwa karshen Ramadan, inda ake kawo abubuwa daban-daban da suka shafi Alkur’ani, kamar irin bugu daban-daban na Alkur’ani, Tafsirai da littafan da suke magana kan maudu’i daban-daban da ya shafi Alkur’ani na kowane bangare na Musulmi Sunnah da Shi’a.

Sai dai a wannan karon taron baje kolin ya samu ci gaba fiye da shekarun da suka gabata, inda kasashe da dama suka samu halarta, domin su ma sun nuna al’adunsu da yanayin irin ci gaban da suke da shi a kan Alkur’ani, cikinsu ko har da kasashen Afrika kamar Nijeriya, Senegal, Komor, Sahili’aji, Tanzaniya, Madagaskar da sauransu.

A cikin abubuwan da Nijeriya ta gabatar a wurin, kamar yadda muka samu labari daga wanda ya wakilci Nijeriya a taron, Shu’aibu Muhammad, ya hada da Alkur’ani bugun hannu, Allo na rubutu, Tawada, Alkalami, Tafsirin Shakh Nasiru Kabara: ‘Ihsanul Mannan’, Tafsirin Shakh Abubakar Mahmud Gumi: ‘Raddul Azhan Ila Ma’anil Kur’an’, Tafsirin Shaikh Abdullahi Gwandu, Hotunan makarantun Allo da sauransu.

Shi dai wannan taron zai dauki kamar tsawon kwana 25 ana gabatar da shi.

An gabatar da tarukan Nisfu Sha’aban a Da’irar Kaduna

Daga Wakilinmu

’Yan uwa na Kaduna sun bi sahun sauran na garuruwa wajen shiryawa da gabatar da tarukan tunawa da ranar da aka haifi Imamin wannan zamanin, Imam Mahdi (AS) da kuma Malam Ibraheem Zakzaky (H), inda aka shirya tarurruka domin taya juna murnar zagayowar wannan babbar rana ta 15 ga Sha’aban.

Da yake jawabi a wajen taron da Da’irar ta shirya a filin ’Yan Lilo da ke tsakiyar T/wada Kaduna, Malam Mukhtar Sahabi, ya tabbatar da cewa, an haifi Imam Mahdi (AS) a shekara ta 255 bayan hijirar Manzon Allah, kamar yadda ya zo a littafan tarihi na magabata, kuma ya shiga gaiba, zai dawo ya kawar da zalunci da azzalumai.

Malam Sahabi, wanda ya koka matuka game da bayanin da wasu mutane suke yi game da Imam Mahdi (AS) da nufin kawo saddu ga fahimtar tafarkinsa, ya ce al’ummar Mahdi bai zama ya boyu ga kowa ba, kuma al’amarinsa na Allah ne, don haka ba wani da zai iya kawowa al’amarinsa cikas. “Idan ba ku san Imam Mahdi ba, ku daina karambanin yin magana a kansa, ku tambayi ma’abota sani idan kun zamo ba ku sani ba”.

Ya yi cikakken bayani game da shubuhar da wasu suke cewa wai ba a haife shi ba. Ya ce batun haihuwarsa da kuma yin magana tun yana yaro ba wani bakon abu bane ga duk wanda ya san al’amarin Musulunci, “domin Annabi Isa, Annabi Idris, Annabi Iliyasu da Khidir (AS) duk suna nan ba su ba su mutu ba, duk kuma za su dawo domin su taimaki Imam Mahdi idan ya bayyana”, in ji shi.

Malam Mukhtar Sahabi, wanda ya bayyana cewa lamarin Imam Mahdi ya yi kama da na Annabi Isa, ya bayyana cewa Imam Mahdi zai zo ne ya gyara duniya, ya cika ta da adalci bayan ta cika da zalunci. Kuma akwai abubuwa da yawa wadanda ba za su samu ba sai idan Imam Mahdi ya bayyana. Ilimi zai karu, imani ma zai cika ya kai kololuwarsa.

Ya yi kira ga jama’a da su yi wa kansu kiyamullaili su nemi sanin waye Imam Mahdi, domin yana cikin jerin Khalifofin Annabi 12 kamar yadda Bukhari da Muslim suka ruwaito cewa shi ne cikon na 12, don haka shi ne Imamin wannan zamanin, kuma duk wanda bai san Imamin zamaninsa ba zai yi mutuwar jahiliyya kamar yadda Manzon Allah ya tabbatar a cikin Hadisin Huzaifa.

A gurgurje kuma ya tabo janibin Malam Ibraheem Zakzaky, wanda ya ce tun kafin wannan lokacin an yi ishara da bayyanarsa da kuma irin aikin da zai yi har ma da irin matsalolin da zai fuskata da ma wadanda za su kasance cikin masu taimaka masa wajen share wa Imam Mahdi fage ta hanyar kawar da zalunci da kafirci a wannan nahiyar.

Kazalika ya gabatar da irin wannan jawabin a harabar babban masallacin Juma’a na Rigasa Kaduna, inda ’yan uwa na Halkar Imam Mahdi suka shirya kayataccen taro domin wannan rana.

Masu koma wa munanan dabi’u bayan Ramadan, ba su amfana da shi ba

In ji Sayyid Ibraheem Zakzaky

Daga Muhammad Isa Ahmad

Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Kano, karkashin jagorancin Malam Muhammad Mahmud Turi suka ziyarci Sayyid Zakzaky (H) ranar Talata 23 ga Sha’aban 1431BH a FIC da ke Dan Magaji Zariya.

Yayin gabatarwa, Malam Muhammad Turi ya ambaci cewa kamar yadda aka saba ’yan uwa na yankin Kano kan ziyarci Sayyid (H) a watan Sha’aban wanda a wannan shekarar ma sun sami halarta.

Sayyid Zakzaky (H) yayin da yake jawabi ga mahalarta ya tunatar da karfafa ’yan uwa a wajen dagewa musamman ga shi Ramadan. Dama dai watanni masu alfarma na Rajab da Sha’aban an dage wanda zai hadu da Ramadan da ta kasance makaranta ce ta samun takawa, kuma wanda ya ci jarabawar samun takawa ya zamo muttaki kenan, ya fito shawal a watan Shawwal.

Sayyid (H) ya ambaci Azumi na koyar da takawa ne ta yadda idan mutum na Azumi idan ya ga dama zai iya boyewa ya ci abincinsa yana mai ambaton ai yana Azumi idan yana cikin mutane. Amma saboda tsoron Allah (T) sai ya ki yin haka, ka ga takawa shi ne ka ki sabawa Allah (T) ko da ko ba wanda ke ganin ka, kai kana jin tsoron Allah (T) ne.

Ya kuma kara da nusar da cewa kasantuwar Azumi na koyar da takawa, lalle ana son a ga takawa nan a dukkan sauran ayyuka. Misali, idan kai ma’aikacin gwamnati ne ba za ka murguda alkalumma ba domin kana jin tsoron Allah (T). Haka nan idan kai dan kasuwa ne ba za ka yi almundahana ba domin kana jin tsoron Allah (T).

Sayyid (H) ya yi tsokaci ga wadanda kan dauki Ramadan a matsayin watan takurawa, kuma su bar wasu daga cikin munana ayyuka, amma su komawa wannan munanan dabi’u da ba su amfana ba da Ramadan. Na’am, adatan ba akan samu ana iya dukkan ayyukan da akan gabatar a Ramadan ba, amma bai kamata ba a komawa munanan ayyuka da aka daina ba. Wato ana son da an fita Shawwal shawal an rabu da munana ko nakasun ayyuka da aka gabatar a da har abada.

Sayyid (H) ya kuma karfafa batun kyautatawa juna wajen buda baki ta hanyoyi da dama, da kuma tanadar wa iyali kayan Salla da kuma wadanda za a iya yiwa.

Sayyid dai ya gabatar da du’a’i, kuma maziyartan sun isa gidajensu lafiya.

Duniya ba matabbata bace

In ji Wakilin ’yan uwa na Bajoga

Daga Muhammad Adamu

Wakilin ’yan uwa na Bajoga a jihar Gombe, Malam Muhammad Mufti ya tunatar da al’ummar Musulmi hadarin da ke tattare da fifita duniya a kan komai. Ya ce, “ita duniya mun zo cin kasuwa ne, ko ka sayar, ko ba ka sayar ba, ba ruwan Allah idan lokacinka ya cika tafiya za ka yi ko ba shiri.”

Malam Muhammad, wanda ke jawabi a wajen wani taro da aka shirya a garin na Bajoga, ya tabbatar da cewa Sayyida Khadijah (AS) a budurwa Annabi (S) ya aure ta ba bazawara ba, kamar yadda gurbataccen tarihi ya zo wa wannan al’umma.

Kazalika ya shaida wa mahalarta taron ne cewa Nijeriya ta rube, don yanzu ta kai shekaru 107 daga lokacin da aka kirkiro ta aka dora ta birbishin tsarin da ba na Allah ba, saboda haka yanzu ana neman masu girbi ne kawai.


Shafin Farko