|
|
Juma'a 3 Ramadan, 1431 Bugu na 938 ISSN 1595-4474 |
|
|
|
Daga M. Umar Saye
A sakamakon taron gangamin da jam’iyyar PDP ta gabatar a garin Alkaleri domin karbar bakuncin Alhaji Bala Abdulkadir Kauran Bauchi, kuma Ministan Abuja zuwa cikin jam’iyyar, sai kuma daga baya aka fara samun tufka da warwara daga uwar jam’iyyar reshen jihar Bauci, inda suka bayyana cewa su ba su da labarin wannan hijira da aka aiwatar a ranar Litinin din da ta wuce.
Alhaji Sama’ila Adamu Burga mai rikon Sakataren jam’iyyar ta PDP a jihar Bauci shi ne ya kira taron manema labarai a hedikwatar PDP da ke Bauci a ranar Talatar da ta wuce, inda ya bayyana cewa, babu wani Shugaban PDP na Jiha da ya samu labarin cewa Minista Bala zai koma jam’iyyar, don haka bai bi dokar sauya sheka ba, ba su san da zamansa ba, saboda bai bi hanyoyin da suka dace ba. Tun cikin wata Yuni da ya rubuta musu takarda suka ba shi amsa bai sake cewa komai ba, sai suka ji ya koma.
Sama’ila Burga ya bayyana cewa har yanzu suna jiran sa don ya sa rana su karbe shi, idan kuma bai yi haka ba, to yana da niyyar raba jam’iyyar ne a jihar. Don haka ya ce komawarsa PDP babban lamari ne da yake da bukatar a shirya gangami daga jiha ba ya tara wanda yake so kurum ya koma ba.
Don haka ya kara da cewa matukar bai yi haka ba za su dauki komawarsa da wata manufa ta rashin gamsuwa da Gwamna Yuguda duk da cewa shi mai gidansa ne, don haka yanzu ya butulcewa Gwamna Yuguda.
Ya ce kasancewar mataimakin Shugaban PDP na shiyyar Arewa maso gabas Sanata Paul Wampana a wannan waje ba shi zai tabbatar da hijirarsa zuwa PDP ba, illa ya dawo a daidaita a karbi hijirarsa ta hakika.
Shi kuwa mai tallafa wa Ministan Abuja kan harkokin siyasa, Alhaji Danladi Abdullahi Mai Auduga ya kira taron manema labarai a daren Talatar, inda ya bayyana cewa yana son mayar da martani ga Sama’ila Burga da cewa lokacinsa ya kare na jagorancin jam’iyyar abin da ya fada sako ne na Gwamna kurum. Amma Sanata Bala Kaura ya dawo PDP tun wajen watanni biyu, kuma ya dawo da umurnin shugabanni, inda ya fara da gabatar da kansa a wajen shugabansa na gunduma ya ba shi kati, kuma ya dawo Karamar Hukuma ya gabatar da kansa, ya rubuta, ya kuma gabatar da kansa a bayyane, ya rubuta takarda ga shugaban jam’iyya tun daga gunduma har zuwa matakin kasa da Shugaban kasa da Gwamnan Bauci da jami’an tsaro na jiha da kasa baki daya, kuma har cikin jaridu ya buga.
Don haka ya ce yin waccan magana hassada ce, kuma wanda ya yarda, ko ya ki yarda ruwansa, don wannan magana ce ta jahilci da makirci da yaudara da neman raba kan jama’a. Don haka ya ce yanzu shiga jam’iyyar kurum ana sayen kati ne a shiga sakar sama, don haka yin biki ba wajibi bane, illa ana amfani da shugabannin jam’iyyar na jiha ne don a kawo cikas. Saboda haka ya bukaci jama’a su zo a tafi don a gina jam’iyyar PDP yadda ya dace, a dinke waje guda.
Alhaji Danladi Mai Auduga ya ce, wannan kalami na shugabannin ya nuna ba su yarda da shugabancin PDP na kasa ba, kuma suna barazana ne ga hadin kan jam’iyyar a jihar Bauci.
Sun baza komar 84 a Zamfara
Daga Husaini Baba
A sakamakon rikicin magoya bayan jam’iyyar ANPP da PDP a jihar Zamfara, Hukumar ’yan sanda sun kama mutum 54, kuma sun baza komar neman kamun mutum 84 a fadin jihar Zamfara.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar ta Zamfara, Abubakar Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau.
Kwamishinan ya bayyana cewa dukkan jam’iyya wacce ake wa rijista tana da ’yancin ta gudanar da dukkan harkokinta a cikin jihar Zamfara, kuma duk lokacin da hakan ya taso akan sanar da su, za su duba su gani idan babu wani baki a kasa, “za mu ba da dama kuma za mu tabbatar da jami’anmu na tsaro sun tabbatar an yi an tashi lafiya”.
Kwamishinan ya bayyana cewa yanzu haka sun kama mutum 54, “kuma muna neman mutum 84 ruwa a jalo, lalle muna da bukatar ganin su don yi masu wasu tambayoyi, kuma wadanda muka kama, da mun kammala bincike za mu kai su gaban Kuliya”.
Kuma Kwamishinan ya kara bayyana cewa sakamakon rikicin an rasa rai da dukiyoyi, don Larabar makon jiya wani daga ciki ya rasu, kuma an kona motoci da kayayyakin da aka fasa.
Da ya koma kan batun ’yan tauri a cikin jihar ta Zamfara, Kwamishinan ya bayyana cewa ya haramta sanya rigar ’yan tauri don dukkan wanda muka ci karo da shi lalle zai yaba wa aya zaki.
Abubakar Muhammad ya kara da cewa matakan da suka dauka a kan ’yan siyasa don ganin an samu kwanciyar hankali da zaman lumana a jihar ta Zamfara zai sa a samu sauki.
A karshe Kwamishinan ya tabbatar wa ’yan siyasa cewa duk ’yan siyasa suna da ikon gudanar da ayyukan siyasarsu, muddin suka sanar da su, kuma in sun bukaci su ba su jami’an tsaru a shirye suke su ba su.
Daga Alhusain Dakace
Kamar yadda makarantun kwana ta ’yan mata da ke jihar Kano suke samun kula daidai gwargwado daga hukumar ilimi ta jihar da kuma tallafin wasu masu hali da kuma kungiyoyi, kamar samar da tsaro, gyara da kula da dalibai da gyara azuzzuwa da samar da ruwa, amma abin ba haka yake ba a makarantar kwana ta ’yan mata da ke garin Kura a jihar Kano.
Wakilinmu ya jiwo cewa matukar gwamnatin jihar Kano ta Malam Ibrahim Shekarau da kuma mawadata ba su dau matakin gaggawa ba, to, babu shakka makarantar ka iya kai wa ga an daina karatu a cikinta kwata-kwata, sabili da tarin matsalolin da suka addabi makarantar mai dalibai mata sama da 1826.
Da take jawabi a gaban dimbin al’ummar da suka taru a bikin cikar makarantar 30 da tsofaffin daliban makarantar suka shirya, Shugabar makarantar, Malama A’isha Musa Abdullahi, ta fada a wurin cewa babbar matsalar da ta addabi makarantar a cikin shekaru da dama ita ce ta rashin kyakkyawan tsaro, wanda hakan ke kawo matukar fargaba ga daliban makarantar da kuma ita kanta da sauran Malamai da kuma duk mai kwana a cikin makarantar.
Malama A’isha ta kara da cewa abin bakin ciki da fargaba shi ne yadda makarantar a halin yanzu gaba dayanta ba a katange take ba, kuma wayar da ake sa wa don zagaye makarantar ta rushe, ga shi kuma makarantar tana cikin jeji ne, kuma akwai kauyaku da ke makwabtaka da makarantar da gonakin mutane, haka ya ba da dama ko ta ina mutum zai iya kutsa kansa cikin makarantar ko dare ko rana.
Sakamakon wannan rashin tsaro da makarantar take da shi ne ya bai wa wasu barayi da zauna-garin-banza shiga makarantar cikin dare, inda suka yi awon gaba da wasu na’urorin injin samar da ruwa mai amfani da hasken rana. Bayan wannan makarantar na fama da karancin masu gadi. A halin yanzu 14 kacal ne, bakwai su yi da daddare, bakwai su yi da rana, “wanda kuma kamata ya yi su nunka haka,” in ji ta.
Akwai kuma dakin shan magani da ke makarantar, a halin yanzu ya lalace ba ya aiki, sannan kuma babu ma’aikaciyar lafiya mai kwana a makarantar da za ta rika kula da lafiyar dalibai.
Malama A’isha ta kara da cewa makarantar na bukatar gyare-gyare, kamar tagogi da kofofi duk sun lalace. Akwai kuma bukatar karin kujeru da tebura da dakunanan kwanan dalibai da magewayi. Kuma yanzu haka babu dakunan gwaje-gwaje, baya ga rashin hasken wutar lantarki, hatta taron da aka gudanar kungiyar tsofaffin dalibai ne ta dauki dawainiyar gudanar da shi.
Don haka ta yi kira da wadanda abin ya shafa da cewa su gaggauta daukar mataki na ceto makarantar game da wannan hali na kai wa ga rugujewa.
Bayan an kammala bikin Wakilinmu ya zagaya cikin makarantar, inda ya ga cewa hakika makarantar tana fama da matsaloli masu tarin yawa, dakunan karatu wasu babu tagogi, wasu kuma babu kofofi, ga kuma tarin kazanta da ta dabaibaye makarantar, hatta dakunan gidajen Malamai wasu sun lalace, wasu kuma ciyawa sun rufe su, ga kuma rashin kyawon hanya na shiga makarantar; tun daga bakin get za ka fahimci haka.
Wani mai suna Isa da ya halarci bikin, shawartar Shugabar makarantar ya yi da cewa ya fa zama dole sai ta yi da gaske kafin a ce an dawo da martabar makarantar, domin ya fahimci cewa ana sako-sako da kuma nuna halin ko-in-kula da gyara makarantar. Kuma da yake makarantar ta mata ce, ’ya’yan jama’a na cikin barazanar bata gari.
Daga Shafi’u Saleh Yola
Majalisar dokokin jihar Adamawa ta zabi mamba mai wakiltar mazabar Guyuk Mr.Gibson Nathaniyal a Majalisar dokokin a matsayin sabon Shugaban Majalisar dokokin jihar, hakan kuwa ya faru ne sakamakon ajiye aiki da tsohon Shugaban Majalisar Hon. James S. Barka mai wakiltar mazabar Hong a Majalisar ya yi don radin kansa a ranar Litinin da ta gabata.
Shi dai tsohon Kakakin Majalisar Mista James Barka bai ba da wani dalili na sauka daga mukamin nasa ba ya dace ya yi hakan ne don radin kansa da kuma ba da dama ga mambobin Majalisar su kawo sauyi da kuma sabonta shugabanci a zauren Majalisar dokokin jihar.
Ya ce yana gode wa mambobin Majalisar bisa goyon baya da hadin kan da suka ba shi a yayin shugabancinsu da ya yi na tsawon shekara uku. Ya ce yana fatan za su bai wa sabon Shugaban hadin kai don ciyar da Majalisan da jihar Adamawa gaba.
Bayan gabatar da jawabinsa ne dan Majalisa mai wakiltar mazabar Gerei a Majalisar, Alhaji Abubakar Abdullahi ya ba da sanarwar sunan Mista Gibson Nathaniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, inda nan take tsohon Kakaki James da sauran mambobin Majalisan suka goya masa baya ya samu zama sabon Shugaban Majalisar dokokin jihar Adamawa.
Mambobin Majalisar sun tsige Hon. Aliyu Isa Amadu a mukaminsa ne na mataimakin tsohon Shugaban Majalisa da kuri’u 17 cikin 25 na mambobin Majalisar suka kuma zabi mamba mai wakiltar mazabar Maiha Hon. Alfa Umar Belel a matsayin sabon mataimakin Shugaban Majalisar dokokin jihar.
Tuni dai Akawun Majalisar Asma’u Salima ta rantsar da sabon Shugaban Majalisar dokokin jihar, inda shi ma ya rantsar da sabon mataimakinsa Alhaji Alfa Umar Belel.
A jawabinsa sabon Shugaban Majalisar dokokin jihar, Hon. Gibson Nathaniyal ya yi kira ne ga mambobin Majalisar da su ba shi hadin kai domin ci gaban Majalisar, inda kuma ya yi alkawarin rungumar mambobin Majalisar domin tafiya tare.
A zantawarsa da manema labarai, sabon Shugaban Majalisar dokokin jihar Mista Gibson ya bayyana shugabancin tsohon Shugaban na tsawon shekara uku da suka gabata da cewa zai dora ne daga inda tsohon Shugaban ya tsaya, zai kuma rinka dasawa da shi domin shi ma ya kai ga nasarorin da tsohon Shugaban ya samu a yayin shugabancinsa.
Ya ce kuma Majalisar za ta ci gaba da bai wa gwamnatin Murtala Nyako da Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Mijinyawa Kugama Guyun saboda kaucewa fadawa rudani a jihar.
A wata sanarwa da Sakataren yada labarai na ofishin Gwamna Nyako, Alhaji Maijama’a Adamu ya sanar da cewa Gwamnan da sabbin shugabannin Majalisan dokokin jihar sun yi alkawarin rungumar juna don ciyar da jihar gaba. Ya ce sun kuma amince da cewa a halin yanzu dimokradiyya tana kai ga dorewa a jihar Adamawa.
Daga Abdullahi Dambam
Maidakin Gwamnan Jihar Bauci, Alhaji Isa Yuguda, Hajiya Hawwa Abiodin (Gimbiyar Liman Katagun) ta ziyarci garin Dambam cibiyar Karamar Hukumar Dambam da ke jihar Bauchi domin ci gaba da shirinta na tallafawa miskinai da marasa karfi.
A ziyarar ta shiga dukkan masarautun Hakiman Karamar Hukumar uku, Dambam, Dagauda da Jalam, inda ta ba da taimakon kayan abinci ga miskinai da gajiyayyu na kamanin Naira 250,000.
Sai dai a cikin jawabinta ga daruruwan matasa a garin Dambam ta nemi matasan da su daina sha da mu’amala da kayan maye, “matasa ba shan kwayoyi ya kamace su ba. Ya kamata kowane matashi ya zama yana da aikin yi, mai zuwa makaranta ya ci gaba da zuwa, ya samu ilimi mai kyau, ba shaye-shaye, ba karya, ba sata. Don Allah a natsu”, in ji ta.
Bayan jawabin nata, Hajiya Hawwa Abiodin, ta kaddamar da wani kafaffen allunan karfe, riguna, takardu tana da hotuna masu dauke da sakon fadakarwa a kan shaye-shaye.
Bayan tashi a gun taron Wakilinmu ya same ta a masaukinta, inda kuma a cikin tattaunawarsu ta bayyana irin ci gaban da shirin nata ya samu. Ta kuma yi kira ga mata da su fito takarar a mukaman siyasa daban-daban, inda ta furta cewa ba wani abu da maza za su yi wanda mace ba za ta iya ba.
Ko da Wakilin namu ya tambaye ta ko tana sha’awar tsayawa takara a matakin jiha ko kasa? Sai ta kada baki ta ce, “mai gidana Gwamnana ina taimaka masa, amma nan gaba sai Allah ya nuna min in fito, to ban sani ba, amma yanzu komai Allah ne zai nuna mana”
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |