Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Masu Karatu

Makarkashiyar da ake shirya wa Nijeriya

Daga Buhari Daure (buharidaure@facebook.com)

Tunda aka fara fitinar nan ta Borno, wato tawayen harkar Boko Haram, kasar nan ta shiga cikin wani yanayi na rashin sanin tabbas. Inda a karo na farko, aka fara kunar-bakin-wake a kasar da ba a bincike. Ko sun ce sune, babu tabbas. Amma dole a zarge su, su suka ba da fuskar haka. Dole a hada kai tsakanin kowa da kowa, don ya yaki ta’addanci.

Wannan harka ta samo asali ne a bisa dalilai da dama. Baya ga cewa 'yan Arewa sun fi kowace kabila dadewa suna mulki a kasar nan, kuma ba su tsinana wa Arewar komai ba. Duk da cewa za su iya yin gyara da kudin da suka mallaka, a yi gaskiya, a yi adalci, a taimaki juna, amma rashin son juna ko kauna, musamman don mutane sun rarrarabu zuwa Dariku da kungiyoyi masu adawa da juna, kuma kowa ya kama nasa a jam'iyyance!

'Yan Boko Haram na nuna alakarsu da kungiyar Alka'ida da sunan samun taimako, horo da hadin kai daga Al-Shabab ta Somaliya. Sannan akwai makamai da dama a hannun jama'a, musamman bayan an yi yakin Libiya, yakin da ya kawo karshen shekarun da Gaddafi ya yi yana mulki.

Sarkakiyar ta sami jan hankalin wasu jahilan Musulmi wadanda suka fada tarkon da suka zama 'yan ta'adda, suka tabbatar da fahimtar da ake wa Musulmi na cewa 'yan ta'adda ne. Yayin da aka daure wasu a shekarun baya, sai wani tsohon Minista, kuma Farfesa ya sako su a sunan hakkin bil’adama. Wannan ne alakar da ta kullu tsakanin ‘CAN’ da 'yan Boko Haram, don bayanan Banki sun tabbatar da wannan hulda.

A gabar Neja-Delta, akwai kabilu da 'yan ta'adda wadanda su ma za su iya ta da kayar-baya ganin abin da ake wa Kirsitoci a kasar nan, musamman bayan hare-haren da aka kai coci-coci a Arewacin kasar ranar Kirsimati da na Kano, ba a kare ba, yanzu ma wani ya dana bam, yana jiran ya tashi! Ku kula da kanku. Tun lokacin da Shugaba Bush ya zo, duk da cewa ana yajin aiki a kasar, sai da ya zo don muhimmancin zuwan nasa! Ya shiga da 'yan leken asirin ‘CIA’, inda aka kulla alakar hulda don ciniki da daukaka addinin Kirista.

Duk wannan za su iya taimakawa wajen ganin an raba kasar, domin Turawa na da ra'ayin man Nijeriya. A kan haka da zarar 'yan Arewa sun matsa da a ba su mulki, wanda ake ganin nan gaba za su yi wannan yunkuri, sai kasar ta shiga yanayin rabuwa ko ta halin ko kaka. Kaurayen Neja-Delta na iya ta da kayar baya da zarar an sami sabani, wani zai kiyasta ashana a rijiyar man!

Irin wadannan dalilan suka sa 'yan Arewa suka zama a daure, ta yadda ba abin da Sarakunan, Malamai balle 'yan Majalisa za su iya cewa, ga kuma kwadayin abin da suke samu a hannun gwamnatin Tarayya.

A yau abin da fi muhimmanci shi ne kowa ya zama mai gaskiya, sai a sami mai gaskiya ya shugabance mu, amma kowa macuci; miji ya cuci matarsa, mata ta cuci ’ya’yanta da ’yan uwa, Malamai su yaudari dalibai, dalibai su cuci kwakwalwarsu, direba ya cuci kwandasta, shi ma karen mota ya cuci fasinja, a kasuwa a cuci kwastoma a boye kaya, a yi kimshe.

Yayin da Arewa sai kara tabarbarewa take yi da talauci, sannan jahilci ya sa mutane har yabawa barna ko tashin bam suke idan ba a garinsu ba ne; wasu su rika kabbarar Allahu Akbar! Suna jin dadi, wai ana Jihadi don jahilci. Za a dade ana fafatawa da 'yan Boko Haram, musamman don an tsokano su. Amma sun yi kuskuren nuna karfi, wato karfin da suka nuna ya rinjaye hankalin harkar, domin burinsu ba zai tabbata ba, ba su da shirin nasara!

Ba a iya bambanta bako da dan kasa, sannan ko yanzu wasu na shigowa kasar ta bayan gida, domin iyakokin kasar sun huje kamar rariya, da an shigo birnin babura sai a zarce har Abuja. Ba inda ba za su je ba! Kamar yadda a yau ba a jin duriyar Alka’ida, to nan da shekaru uku zuwa biyar sai an nemi dan Boko Haram an rasa, dukkansu za su shige karkashin kasa.

Don jahilci a Nijeriya ne ake sa wa yara sunayen Saddam da Gaddafi, yayin da bayan an kifar da su wasu suka sauya wa 'ya'yansu sunaye, sunayen da ba sunayen Annabawa (AS) ba, ba sunayen Sahabbai ba, ba sunayen ranaku ba, ko watanni, sunayen kabila, sunayen 'yan fashi, 'yan tawaye. Sai dai dan ta'addan nan Osama Bin Ladin, wanda ko a yau za ka ga mutane na lika hotonsa a jikin babura, motoci, a daidata sahu da buga fastarsa shago. Shi ba dan takara ba, shi ba Shehin Malami ba, amma karfi da yaji sun mayar da shi gwarzo. Ina aka ce Musulmi ya kashe mutane? Su kansu Gwamnonin da 'yan siyasar ba su tsira ba, inda wasu suke tunanin su fara garkuwa da 'ya'yansu, iyayensu ko matansu. Maganar shigowar soja, wata sabuwar matsala ce mai zaman kanta! Balle wani abu wai juyin juya-hali, wanda an masa nisa. Nijeriya dai tana kan bam. Ko Nijeriya za ta rabu, sai dai uku ko hudu, ba dai biyu ba. An raba Habasha, kuma yanzu an raba Sudan, wannan dalili ne na cewa ba a gama raba Afrika ba.

Akwai alamu da binciken da ya bayyana cewa, wasu abubuwan da Shugaba Jonathan yake yi ba da son ransa ba ne, don biyan bukatun wasu, musamman wadanda suka titida shi ya hau kan karagar mulki. Dole sai ya karkata wani abu don ya biya ranar da aka masa, shi ya sa ake kafewa da tsananin tsaro a kasafi ko janye tallafi, don a sallami wasu da biliyoyi!

An janye tallafin! Duk da haka za mu iya cewa gara Shugaba Jonathan ya janye tallafi ba tare da an rika ba shi wani abu daga ciki ba. Tunda an gaza daukar mataki, maimakon mu gwammace da gulma, gara mu taya wannan gwamnatin da addu'a da Allah ya sa a cika alkawarin da aka wa 'yan kasa na masu abubuwan more rayuwa, sannan mu yi fatan Allah ya hore mana na yau da gobe.

Tabbas Boko Haram matsala ce, ba mafita ba, don sun kara yawan matsalolin da suka shafi Musulmi, sun kara yawan marayu, zaurawa tare da karuwanci. Talaka na kashe talaka. Abin sai ‘Laa haula walaa kuwwata’.

Ra’ayoyin masu karatunmu a Facebook

Murtala Suleiman

Allah ya saka maku da alherinsa Almizan, da ma aikinku fadan gaskiya ne.

Dangane da labarinmu na: Zanga-zangar adawa da cire tallafi: Yadda aka yi wa Gwamnati bore a jihohi

Abdullahi Ibrahim

A duk zanga-zangar da aka yi ban ji wani a NLC, musulmi ko kirista wanda ya ce a koma a yi ta

Istigfari ko tuba ba, don Allah ya dube mu da idon rahamarsa ba, kowa sai tsine wa Shugaban kasa kawai yake yi. Allah ya fid da mu a halin da muke ciki. Amin

Sabi’u Pillars

Ya Allah duk wa su azzaluman Nijeriya in masu shiryuwa ne, Allah ka shirye su, in ba masu shiryuwa ba ne, Allah ka tona asirinsu.

Dangane da labarin mu na, An kashe Musulmi a Lamurde da Benni

Ibrahim Ismail Muhammad

Allah ya ba mu shahada, ya kuma kare mana wannan babbar jaridar Almizan.

Garba Muhammad

Allah ya kawo sauki, kuma muna rokon Allah ya kawo mana kwanciyar hankali, kuma mu zauna lafiya duk inda muke. Musulmanmu da suka rasu, Allah ya sa sun yi shahada.

Salim Muhammad

Wallahi akwai goyon bayan gwamnati a wadannan abubuwan da ke faruwa, a duba a yi gyara, idan ba haka ba duk muna shirye mu koma lahira baki daya don mun san makomarmu insha Allahu Aljanna ce.

Elcaleef Muhammad Idris

Abin da Goga Jonathan ya shirya ne, da abokanansa Amurkawa. Sai dai a zauna da shirin kariyar kai, da kuma du’a'i.

Dangane da filinmu na, Tarihin Imam Ali Dan Abi Talib (AS) a takaice (3)

Sagiru Saidu

Mun gode, Allah ya ganar da wadanda ba su gane ba.

Alhassan Loga Dunari

Allah ya kara tabbatar da mu bisa wilayancin Imam Ali (AS).

Umar Sule

Mun gode Allah ya tabbatar da mu a kan wasiccin Haidar har zuwa ranar kiyama.

Abdulmajeed Usman Hm, Hujjah takobin Shi'a. Allah ya kara wa Malam lafiya da ikon jaddada addinin Musulunci kamar yadda Allah ya yi mana alkawari. Lokaci ya zo mu yi damarar yaki ’yan uwa.

Dangane da labarinmu na, Dandalin Masana (AFIMN) Bauci sun yi taron daura

Daga Bala Ningi da Nasiru Yalwa

Allah ya taimake ku ’yan Bauchi, ya kuma bar mu da Malam Zakzaky, ameen.

Dangane da labarin mu na, Aya ta bayyana a Husainiyya Bakiyyatullah Zariya

Abdulrahman Gani

Allah ya kara mana soyayyar Ahlul bayt (AS) da Sayyeed Zakzaky (H)

Aliyu Muhammad

‘LABBAIKA YA AL-ZAKZAKY' Allah ya kara mana sabati da yakini, ya ba Malam nasarar tabbatar da Musulunci a Nijeriya, amin.

Yusuf Ibrahim Kudan

Masoya gidan Annabi mu kara gode wa Allah.

Sadiq Umar

Mun gode Allah da ya zabe mu a cikin jimlar mabiya wannan gida mai haske.

Umar Alhaji

Wannan ishara ce ga masu lura. Allah ya ba mu sabati.

Fatima Ummar

Wannan ma aya ce ga mutane, amma mai hankali zai gane.

DANGANE DA FILIN MU NA. UMURNIN ALLAH NA MUHAMMAD KABIR ALKNAWY

Tijjani Sulaiman Mal.Kabir Alkanawy muna godiya da wannan bayanin na Umurni "takwiny" da "Tashri'iy" Allah ya kara haske! Ni dai wallahi ina son ka!!!

Abdullahi Ladan

Allah ya biya ka namijin marubuta, ka ji mashaya ruwan Hussainiya, masu diba da yawun masu yawun. Muna barar du'a'inku, sabati, biyan bukatu, kariya da duk abin bukata ga Maulana (H).

Muhammad Dhiya'ulhak Adam Mun gamsu sosai, Allah ya saka da alheri, godiya ga wanda yake sanar da mu Imam Ali. Ya Allah don girman sanin da ka yi wa Imam Ali, ka kara wa Sayyeed (H) kusanci da Annabi da kuma Imam Ali. Allahumma ajib du'a’i bi Muhammadin wa Ali Muhammad

Yusuf Ubale

Malam Kabir, Allah Ya kara ilimi da ba ku ikon fahimtar da mu ma su saurare da kokarin bi. Allah ka fahimtar da masu ja, ka nuna musu gaskiyar gurguwar fahimtar da suka yi matsayin Imam. Allah ka sakawa su Malam da a ko’ina suke fito da gaskiyar al'amari.

DANGANE DA LABARINMU NA, TA’ADDANCI BA AIKIN MUSULMI BA NE -SULTAN SA’AD ABUBAKAR

Abu Muhammad

Kai amma Sultan Allah wadaranka. To ka sa ni mu ma a Sakkwato akwai jinin ‘yan uwanmu a wuyanka, amma ba ka nemi gafararmu ba. To, wallahii ka sani ba za mu yafe ba, kuma martaninmu ya fi dukkan martanin zafi.

Abdullahi Ladan To, ai ganawar an gaya masa abin da zai fada ne shi ya sa dole ne kuma ya fada. Kuma da ma shi ba addini ne ya dame shi ba, kuma da ma su ne suka sai da mu wa Yahudawa, don haka yanzu saura su zo su dauke mu kawai.

DANGANE DA LABARINMU NA, ABIN DA YA SA MUKA HAdE WAJE dAYA IN JI SHUGABAN KUNGIYAR IZALA

Aliyu Abdulkadir

Allah ya kara dunkule mu a waje daya. Allah ya taimaki Musulunci da musulmai baki daya. Wannan ba karamar nasara ba ce ga dukkan musulman duniya baki daya. Alhamdulillah.

Sammani Nasir

To, an gama karami saura babba, shi ne daina cin mutuncin duk wanda ba dan kungiya ba. Da kuma yarda da Musuluncinsa, ya zamo an hade waje daya karkashin jagorancin Shugaba guda daya ba tare da rarraba ba. Allah ya nuna mana ranar don Ahlil kisa'i (AS).

Muhammad Bello

Amin

Abal Fadal

Kamar yadda Mal. Nasir ya ce, Allah ya sa hadewar ta amfani Musulunci, ba ta zamo kwangilar yakar sa ba. Don ba mummunan hadari irin taimaka ma makiya wurin fada da addini da sunan addini. Allah ya taimaki addinin Baban Kasim (SAWA).

DANGANE DA LABARINMU NA, LABARIN WADANDA SUKA JE AIKIN HAJJI A KEKE

Abubakar Umar Ibraheem

To, amma ta yaya suka dawo gida?

Yusuf Ibrahim Kudan

Ko jirgi suka hau su ka dawo Mal. ABUBAKAR, da ma batun shi ne sun je Makka a keke, ba a ce sun je sun dawo ba. Wadannan matasa sun yi kokari, Allah ya sa sun sami hajji karbabbe.

ABUBAKAR UMAR IBRAHIM ka shirya mu je bana, mu sai mu yi zuwa da dawowa.

Umar Abdullahi Sakafa

Idan dan Nijeriya zai yi irin wannan tafiya ta ina zai bi ya fita? Ta wace kasa zai ratsa? Wace gabar ruwa mutum zai dumfara? Shin ko sai ya yi biza? Ina neman amsa da wuri-wuri saboda lallai a fara shiri.

Abal Fadal Mal. Umar Saqapha, in ka duba 'map' din Nijeriya za ka ga cewa muna da 'boder' da Chad, ita kuma tana da Sudan. Daga Sudan kuwa za a ketare bahar maliya ne zuwa Jidda. Amma a wani littafi (Hajj by road), marubucin ya nuna sai da suka shiga ta Nijar da Kamaru kafin Chad saboda wasu matsaloli da ya kawo a lokacin. Ina ganin zuwa da mashin zai fi komai sauki. In za a yi dogaro da 'experiance' din marubucin 'Hajj by road', tafiyar ta wuce mutum 1 ko 2. Tana bukatar ayarin da ya kunshi kanikawa, ma'aikatan lafiya, kayan abinci, magunguna, dss, gwargwadon girman ayarin. A dai ci gaba da neman sani kan al'amarin, na san ba za a rasa samun matafiya ba.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan