Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Rahotanni

Al’ummar Gusau sun yi mummunan gani

Daga Mustafa Garba

Al’ummar unguwar Samaru Low-Cost da ke cikin Gusau hedikwatar Jihar Zamfara sun wayi garin Talata 05/01/2012 da mummunan labari a cikin unguwarsu na tsintar gawar wani jinjiri sabuwar haihuwa a cikin kwata.

An tsinci wannan jinjirin ne a cikin kwata a daidai a lokaci da ake kokarin kwashe ruwan da ke cikin kwatar saboda an fahimci ramin ya cika da ruwa har yana zuba waje. Aliyu Ibrahim, shi ne yaron da babansa ya sa kwasar wannan kwatar, kuma ya yi wa Wakilinmu karin bayani a kan yadda al’amarin ya faru kamar haka; “Na fito tun da safe domin in cika umurnin da Mahaifina ya ba ni na kwashe wannan kwatar tunda sanyi safiya kafin jama’a su fara fitowa kada ruwan kwatar da wari ya ishe su. Farawa ke da wuya sai na ci karo da wani abu mai kamar kitse ko leda, da na ci gaba da jawowa sai na ga jariri. Take tsoro ya kama ni na ruga gida a guje na sanar da Mahaifana aka nemo makwabta domin tabbatar da gaskiyar abin da ke faruwa. Bayan an fito da jinjiri ne sai aka kira Mai Unguwa, shi kuma ya kira ’yan sanda domin su shaidi al’amarin”.

Kabiru Salihu Zamau dalibi ne a makarantar koyon jinya ta Jihar Zamfara yana daga cikin wadanda suka duba gawar jinjirin, ya bayyana mana cewa; “Jaririn ya isa haihuwa, kuma an haife shi cikin koshin lafiya”.

Almustafa Ibrahim na daga cikin wadanda suka halarci rufe gawar jinjiri a makabartar Samuru, ya tabbatar mana da cewa yana ganin wannan yaron daga wata unguwa ne aka kawo shi nan, amma a unguwarsu babu wata wadda suka san da cewa tana dauke da ciki alhali ba ta da aure, “Kuma da ma unguwar tamu unguwar ma’aikatan gwamnati ce, kuma bakin gari take, babu jama’a a cikinta da yawa. Don haka muke samun irin wadannan matsalolin domin ko a lokutan baya ma an taba tsintar wasu jinjirai guda biyu, amma su da ran su aka kawo su nan aka jefar, yanzu haka yaran na gidan marayu ana kulawa da su”, in ji shi.

Malam Akilu Shinkafi na daga cikin dattawan unguwar, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a kan batun, inda ya yi fatan Allah ya tona asirin wadanda suka yi wannan aiki, tare kuma da yin kira ga gwamnati da jama’a da su kara sa ido ga masu aikata irin wadannan miyagun ayyukan domin suna jawo fushin Allah. Ya kuma yi kira ga iyayen yara da su zage damtse wurin kulawa da tarbiyyar ’ya’yansu.

Madrasatul Hizbur Rahim Tsafe ta yi bikin yaye dalibai

Daga Mustafa Garba

Madrasatul Hizbur Rahim da ke Zawiyyar Malam Kasimu Unguwar Sabon Fegi a garin Tsafe cikin Jihar Zamfara ta gudanar da bikin yaye daliban da suka yi sauka a ranar 31/12/2012. Bikin saukar ya gudana ne a harabar makarantar, inda Malamai daga babbar Zawiyyar Hizbur Rahim da ke Gusau da kuma jama’a da dama daga cikin garin na Tsafe da kauyuka suka samu halarta.

Da yake jawabi a wajen taron, babban bako Malan Bello Wazifa Gusau, ya taya daliban murna bisa ga wannan matsayi da suka samu, kuma ya bukace su da su kara dagewa domin yanzu suka fara karatu. Ya yi kira ga al’umma da su kokarta su gina wa makarantar mazauni na din-din-din. Ya kuma kara kira ga iyayen yara da su kara kulawa da Malaman da suke karantar da ’ya’yansu domin ba kowane Malami ba ne ake bai wa koyar da yara.

Da yake tsokaci a kan halin da kasar ke ciki kuwa, Malam Mai Wazifa ya ce; “Yahudawa na ta yunkurin ganin sun wargaza kasar nan, amma hakan ba ta samu ba har yau din nan sakamakon addu’o’in da yaranmu ke yi da kuma Malamanmu”.

Daga karshe dai an yi ’yan ciye-ciye da lashe-lashe, kafin kowa ya wuce zuwa gida. Dalibai bakwai ne suka sauke Alkur’ani a wannan karon.

Gwamnatin Kwankwaso ta bullo da shirin ‘lafiya jari’

Daga Mustafa Ibrahim Kano

Mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan tsafta da kula da muhalli, Alhaji Shehu Usman Aliyu Yammedi ne ya bayyana aniyar gwamnati na bincike mai zurfi don tabbatar da cewa magungunan da matasan da aka horar a karkashin wani sabon shiri da suka kirkiro mai suna ‘lafiya jari’ ingantattu ne.

Alhaji Shehu Usman ya ba da wannan tabbacin ne jim kadan da kammala kaddamar da shirin bai wa matasa 200 kayan magani da suka kai na Naira dubu 100 da kuma kudin kama haya Naira dubu 50 da gwamnatin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ta aiwatar a wani shiri na samarwa matasa aikin yi mai suna ‘Lafiya Jari’, inda matasa 200 suka amfana.

Hon. Shehu Usman Aliyu Yammedi, wanda shi ne Babban Jami’in na ‘Lafiya Jari’ ya ce, duk wata hanya da za ta sa a samu magani mai kyau da sauki sun tsara ta, domin kaucewa matsala a wannan shirin na ‘Lafiya Jari’.

Ya ce, don haka ne ma aka shirya yadda za a tafi da abin ta hanyar sa ‘D.M.A’, wato ‘Drugs Management Agency’ a cikin lamarin, wacce take da ruwa-da- tsaki wajen tafi da hada-hadar maganin da wadannan matasa za su rika saye, suna sayarwa a kemis dinsu, da ma kulawar kungiyar masu sarrafa magunguna, da dai sauran masu ruwa-da-tsaki, domin kawar da matsalolin sayen magani maras kyau ko kuma wanda lokacin aikinsa ya kare a wannan jiha.

Ya ce, za su sa ido sosai na ganin wannan tsari na ‘Lafiya Jari’ ya tafi daidai da shirin gwamnatin. Shehu Yammedi ya ce, kodayake shi ba zai magana da yawun ‘D.M.A’ ba, amma ya san ba za su yi wasa a kan wannan aiki nasu ba.

Haka kuma ya ce, duk da kafin wannan horo da aka yi masu na ’yan kwanaki kuma duk da kasancewa dalibai ne da suka yi karatu a makarantun kiwon lafiya da na tsafta, da kuma makarantun Ungozoma, an gargade su da su tsaya a kan abin da suka sani kada su yi abin da ba su gane ba ko da kuwa rubutun Likita ne, to kada su yi wasa da wannan aiki, domin harkar lafiya abu ne na natsuwa da taka-tsantsan.

Murtala Shehu Rano da Hajiya Sabuwa na daga cikin wadanda suke cin gajiyar wannan shiri, sun yi kira ga matasa da kada su ba da kunya a wannan shiri. Alhaji Bala Muhammad Juji ya ce, makasudin wannan shiri shi ne samawa matasa aikin yi da kuma kawar da matsalolin da suka shafi lafiya. Ya ce, a matsayinsa na jagoran horar da matasan, an ba su horo mai kyau. Ya yi kira da Gwamnonin Nijeriya da su bullo da irin wannan tsari a jihohinsu.

Umar Tata ya raba wa matasa fom na ‘JAMB’ 400 a Funtuwa

Daga Husaini Baba

Ilimi shi ne ginshikin zaman duniya, kuma shi ne ke sa mutum ya zamo cikakken mutum, ya san kansa kuma ya amfani al’umma, kuma shi ne babban jarin da za a ba mutum ya amfana da shi, duniyarsa da lahirarsa.

Wannna ne ya sa matashin dan siyasa kuma mai kishin matasa da su zamo mutane nagari, Alhaji Umar T. Abdullahi (Tata) Dutsim-ma ya raba wa matasa fom na ‘JAMB’ na shiga Jami’o’i guda 400 a fadin Karamar Hukumar Funtuwa cikin jihar Katsina.

Nura Turaki Funtuwa, daya daga cikin wadanda suka wakilci Alhaji Umar Tata wajen raba fom din ya bayyana cewa, kishin da Tata ke yi na ganin matasa sun zamo mutane nagari, sun kauce wa bangar siyasa da zaman banza, shi ne ya sa Alhaji Umar Tata ya sawo wadannan fom na makudan kudi don tausayawa ga matasa, ya ba su kyauta tare da biyan kudin rijistar fom din.

Ya kara da cewa “A kullum shi burin Alhaji Umar Tata shi ne ya tallafa wa matashi ta bangaren karatu, kuma tun daga matakin firamare da sakandire da Jami’a. Ba a nan gudummuwarsa ta tsaya ba, hatta makarantun addini, Umar Tata na taimaka masu don yanzu haka ya sai wa makarantar Limamin Juma’a na cikin gari fili na miliyan daya da rabi, sai kuma ya sai fili don makabarta a BCJ na kimanin miliyan daya. Kuma ya gyara masallacin Juma’a da ke cikin Tudun Wada Funtuwa, da dai sauran ayyukan da ya yi”.

Da ya koma bangaren lafiya kuwa, Alhaji Nura Turaki ya bayyana cewa Alhaji Umar Tata ya samar da ruwa a asibitin Funtuwa, kuma ya kai gudummuwa a gidan yari na Funtuwa na tallafin hatsi, shinkafa buhu 25, sai gero buhu 10 da keken dinki da na saka, don tallafi ga wadanda ke tsare a kurkukun Funtuwa.

“Don haka, wannan tallafin da Alhaji Umar Tata ya kawo mana a Funtuwa, duk da shi ba dan Funtuwa ba ne dan Karamar Hukumar Dutsin-ma ne, ya nuna mana cewa lallai shi mai kishin garin Funtuwa ne. Muna fatan Allah ya saka masa da alheri, ya kare shi daga sharrin makiya da mahassada, kuma ya ci gaba da taimaka wa al’ummar wannan jihar tamu da kasa baki daya” a ta bakin Nura Turaki.

Wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Bello Abubakar da ke Funtuwa ya jinjina wa, Alhaji Umar Tata a kan yadda ya dau nauyin sai wa dalibai fom don shiga Jami’o’i, ya kuma bayyana cewa, da ana samun kamar sa a fadin kasar nan, da karatu bai gagari dan talaka ba. “Don yanzu haka wasu da dama lokacinmu rashin kudin fom ne ya hana su ci gaba da karatu, amma yau ga shi Allah ya kawo mana mai kishin talaka, mai son ci gaban matasa, ya sai fom ya raba kyauta, da yin rijista a intanet kyauta, wanda a yanzu ana sai da shi Naira dubu biyar da rijistarsa, kuma duk ya dau nauyi. Ina fatan matasan masu hali za su yi koyi da Alhaji Umar Tata wajen tallafa wa matasa ta janibin karatu”.

’Yan kasuwar da ba a bi bashi ne za su amfana da tallafi a Zamfara
Hon. Hasan Zurmi

Daga Husaini Baba

A kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi na ganin ta farfado da harkar kasuwanci a fadin jihar ta Zamfara, yanzu haka gwamnatin jihar karkashin Gwamna Abdul’aziz Yari, ta yunkuro don tallafa wa ’yan kasuwar jihar da bashin jari, kuma wadanda ba a bin su bashin ne kadai za su amfana da tallafin.

Kwamishinan kasuwanci da ma’sana’antu, Hon. Hasan Muhammad Zurmi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau.

Hon. Zurmi ya kara da cewa, wannan shirin tallafin don ganin bai samu nakasu ba, gwamnatin ta sanya shi a cikin kasafin kudi na wannan shekarar da muke ciki, kuma don haka ya sa gwamnatin ta yi hadin gwiwa da Bankin Masana’antu (Bank of Industries) don ganin hakarta-ta-cimma-ruwa, wajen farfadowa da harkar kasuwanci a fadin jihar ta Zamfara.

Hon. Hasan ya kara da cewa, bai wa ’yan kasuwa tallafi zai inganta tattalin arzikin jihar ta Zamfara, kuma matasa za su samu sana’o’in da za su yi.

Da ya koma kan batun wadanda suka ci bashi a baya kuma suka ki biya, Kwamishinan ya bayyana cewa babu makawa sai sun biya shi, don yanzu haka gwamnatin na bin wasu ’yan kasuwar bashin sama da miliyan talatin, don haka duk wanda ake bi bashi sai ya biya sannan a ba shi wani.

A karshe, Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da aka san su da kaunar juna da zaman lafiya da su kasance haka don babu abin da ke ci gaba ba tare da zaman lafiya ba. Kuma kada su yi gaggawa game da ayyukan da gwamnatin Gwamna Yari take yi, don shirye- shiryen gwamnatin na ganin ta bunkasa wannan jihar shi ne da shi Gwamna ke kwana kuma yake tashi. “Don haka nake kira ga al’ummar jihar Zamfara da su ci gaba da bai wa gwamnatinmu goyan baya da addu’a don ganin kudurinta ya hakkaku,” in ji shi.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan