Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Rahotanni

Kungiyar Kwadago sun ci amanarmu

In ji Malam Musa Gambo

Malam Musa Gambo, daya daga cikin matasan Zariya masu bayyana ra’ayinsu kan al’amuran yau da kullum ya bayyana matukar fusatarsa game da matakin da ’ya’yan kungiyar Kwadago ta kasa, NLC, ta dauka na amincewa da karin farashin mai daga Naira 65 zuwa 97 da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.

Malam Musa Gambo, wanda ya bayyana wannan damuwar tasa a lokacin da yake zantawa da Wakilinmu, ya ce; “Lallai Shugabanin Kungiyar Kwadago sun ci amanarmu, sun sayar da mutuncimu, sun ba mu kunya, sun nuna ba domin talakawa ko jama’ar kasa suke yin fafutikar da suke yi ba. Sun ce ba za su yarda da karin ko kwandala ba, amma sai ga shi sun mika wuya ga karin 33. Kawai sun yaudari jama’ar kasa sun fito sun nuna damuwarsu”.

Ya ci gaba da cewa mika wuya da suka yi ba tare da sun tuntubi jama’ar kasa ba, ya nuna dama bakinsu daya da gwamnatin, kawai ana amfani da su ne don a wawaitar da hankalin jama’a a ci gaba da bautar da su. Ya yi watsi da uzirin da suka bayar na cewa sun dauki wannan matakin ne don su ga ana neman a kashe mutane.

Malam Musa ya nuna damuwarsa a kan yadda gwamnatoci a kasar nan suke yin duk wani nau’in kuntata wa ga jama’a da sunan cire tallafi. Ya ce a sauran kasashen duniya masu arzikin man fetur kamar Nijeriya, duk abin da mutum zai saya akwai tallafin da gwamnati ke sawa don ya zama sun ci gajiyar abin arzikin da Allah ya hore masu. “Domin arziki na al’ummar kasa ne gaba daya, amma su mahukunta kasar nan sai suka karkatar da arzikin kasar nan cikin aljihunansu, su kadai suke amfana, daga su sai ’ya’yansu”.

Matashin ya kuma nuna matukar gamsuwarsa a kan irin tutsun da jama’ar kasar nan suka fara fitowa suna yi wajen nuna rashin amincewa da matakan kuntatawa da gwamnati ke fitowa da su. “Lallai na goyi bayan matakan da al’umma suka dauka na fitowa su nuna rashin amnincewarsu. Mutum ya fito ya nemi hakkinsa lallai bai zama aibi ba. In har ba a kyautata maka ba, ba za a ce abin da ke hannunka za a kwace ba”.

Malam Musa Gambo ya luma yi jinjina ta musamman ga wasu al’umma da suka fito Kirsitoci da Musulmi suka hada hannu waje guda don yakar irin zaluncin da ake yi masu. “Hada kai waje daya shi ne zai kawar mana da zalunci da azzalumai. Kullum suna so ne ya zama muna fada da juna don ya zama sun ci gaba da zaluntarmu. Mulki yana tabbata da adalci ko da ba Musulunci, amma ba ya tabbata da zalunci ko da Musulunci. Abin da ya faru a Masar na hada kai tsakanin Musulmi da Kirista suka kori azzalumai”.

Da yake tsokaci game da hare-hare da tashin bama-bamai da ake kai wa kuwa, Malam Musa Gambo, ya nuna matukar damuwarsa a kan yadda aka jefa al’umma cikin dimuwa ana gwara kansu. “Gaskiya yanzu kasar nan ta shiga rudami, ana kai hare-hare da sunan Boko Haram, wannan dai wata kirkira ce da aka kirkiro don cimma bukatunsu na kashin kansu da kuma na kasashen Yamma”, in ji shi.

Yan fashi sun yi wa Zamfara kofar raggo

Daga Mustafa Garba da Bello Tudu

Kusan duk wayewar gari sai an samu labarin da ’yan fashi da makami suka auka wa bayin Allah a wani yanki daga cikin yankunan Jihar Zamfara suka kwashe dukiyarsu, wani zubin ma har su kashe su.

’Yan kasuwa da ke fatauci zuwa gari-gari su suka fi fadawa cikin tarkon da ’yan fashin ke yi. Wani abin takaici ma shi ne, yadda hatta ’yan sanda suka fara nuna alamar kamar abin ya gallabe su. Domin suna jin tsoron jefa kansu cikin lamarin sakamakon yadda ’yan fashin ke fuskantarsu da makaman da suka fi nasu kuzari.

Ko a wannan makon sai da ’yan fashin suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a garuruwan Tsafe da kuma Birnin Magaji, inda kuma wasu ke kwance a Asibiti suna karbar magani a sakamakon raunukan da suka samu.

A garin Tsafe, a ranar Litinin 23/1/2012 da safe ’yan fashin sun tare hanyar Gusau zuwa Zariya a wani kauye da ake kira Magazu gab da shiga garin Tsafe, inda suka bude wuta ga wata motar fasinja wadda ta nemi ta juya bayan da suka yi kecibis da gungun barayin, inda a nan take suka bindige wani soja wanda dan garin ’Yandoton Daji ne a kan hanyarsa ta komawa wurin aiki bayan ya kammala hutu.

Wadanda al’amari ya faru a gabansu sun shaida wa ALMIZAN cewa sojan da ya rasu ba ya cikin kayan aiki, amma barayin sun so harbin Direban ne a lokaci da ya nemi ya juya, sai harsashin ya fada wa sojan, domin yana cikin fasinjan da ke gaban motar, kuma akwai wadanda suka samu raunuka da dama.

Wasu daga cikin wadanda suke zaune kusa da wurin da al’amarin ya faru sun shaida wa Wakilinmu cewa duk da ’yan sandan da ke zama wurin kusan ko yaushe, ana samun matsala a wannan wurin, don haka sun yi kira ga Hukumar ’yan sanda ta Jihar Zamfara da ta binciki jami’anta a kan yawan fashi da ake yi a kai a kai a tsakanin Tsafe da Magazu.

Ya zuwa lokacin da muke hada wannan rahotun tuni aka turo jami’an soja a wannan hanyar domin ci gaba da kulawa da ita saboda lamarin hanyar ya fara shan karfin ’yan sanda.

Ana cikin juyayin wannan al’amari ne, kuma a ranar Talata 24/1/2012, wasu gungun ’yan fashin wadanda ake zaton Fulani ne suka kai wani mumunan hari a garin ’Yanwarin Daji duk a cikin yankin Tsafe, inda suka kashe Shugaban ’yan banga na garin, Alhaji Abubakar Cika a gaban iyalinsa bayan da suka harbe shi da bindiga har sau shida.

Wakilinmu ya kutsa kai gidan mamacin bayan faruwar al’amarin inda ya ci karo da gawar Marigayin kwace cikin jini. Matarsa ta bayyana wa wakilin namu yadda al’amarin ya faru; ta ce, “Da misalin karfe 4:00 na asuba wadannan barayi suka shigo nan gidan suna neman, Alhaji daki-daki, bayan da suka fahimci yana cikin dakina sai suka kutso kai ba tare da sun nemi kudi ko wani abu ba, kai tsaye suka fada masa cewa ‘mun zo ne mu kashe ka’. Ko da ya ji haka sai ya rungume ni yana kalmar shahada. A hakan suka dinga harbin sa, wanda haka ya sa wasu harsasan suka same ni a bayana, suka raunata ni, kamar yadda kuke iya gani”.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa ALMIZAN cewa kafin wannan ranar, an ji Marigayin yana ba da labarin cewa barayi sun aiko masa da sakon takarda, inda a ciki suka yi masa bayanin cewa suna nan tafe za su kashe shi.

Jama’a da dama ne suka raka wannan mutum zuwa makwancinsa tare da nuna alhini a kan wannan kisan. Kuma sun yi kira ga gwamnatin Jihar da ta gaggauta kawo masu dauki a kan wannan barazana da ’yan fashin ke yi masu duk shekara.

An kashe Alhaji Cika yana da mata uku da ’ya’ya 18. Kafin rasuwarsa, shi ne Sarkin fawar ’Yanwari, kuma Shugaban ’yan banga, haka kuma ma’aikaci ne a Hukumar ba da ilimin furamari ta Tsafe.

Kafin barayin su kashe Alhaji Cika sai da suka shiga wasu gidaje guda uku, inda suka amshi kudi kusan dubu 300, kamar yadda daya daga cikin wadanda aka amsar wa kudaden ya shaida wa Wakilinmu.

Idan za a iya tunawa shekara uku zuwa hudu ’yan fashi sun kashe Alhaji Ma’azu Zurawa, wani babban dan kasuwa a garin na ’Yanware.

A wata sabuwa kuma a ranar Alhamis 26/1/2012 da misalin karfe 9:00 na safe wasu gungun ’yan fashi suka bude wa ’yan kasuwa wuta wadanda suka taso daga Birnin Magaji, inda suka kashe mutune 15, ’yan kasuwar suna kan hanyarsu ta zuwa Batsari ta Jihar Katsina.

Wata mata da ta tsira a cikin hatsarin ta shaida wa Wakilinmu cewa; “Ko da barayin suka tsaida motarmu ba su tambaye mu kudi ba, sai kawai suka bude mana wuta, bayan sun gama ruwan harsasai sai suka banka wa motar wuta”.

Ita dai wannan mota ta dauko hatsi ne da jama’a. Matar ta ci gaba da cewa; “Na ji lokacin da ’yan fashin ke cewa mazajanku ne suka ja maku wannan matsalar, domin a kwanakin baya sun yi hadin gwiwa da jami’an tsaro inda suka kashe mana jama’a, don haka wannan abin da muka yi daukar fansa ne.

Jama’a da dama sun nuna fargabarsu a kan wannan mataki da barayin suka dauka, inda suka bukaci gwamnatin Jiha da hada hannu da Jihar Katsina domin a fatatttaki wadannan barayi wadanda suke fakewa a cikin dajin da ke tsakanin Jihohin biyu.

Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin babu wanda aka kama a cikin wadannan barayen da suka yi wannan aika-aikar. Majiyar watsa labarai ta Jihar Zamfara ta sanar da faruwar wadannan hatsuran a gidan rediyon Jihar.

Hare-haren bama-bamai: Mutanen Dambam cikinsu ya duri ruwa

Tun lokacin da Arewacin Nijeriya ya rincabe da harbe-harben bindigogi, kai harin bama-bamai, ruguza masallatai da cocina, duk wani gari da ya kai a kira shi gari a Arewacin kasar nan, to mutanen garin Musulmai da Kiristocinsu suna kwana da tashi ne a cikin zullumin faruwar hari.

Lalatawa da ruguza garin Maiduguri ta Jihar Borno da wasu Kananan Hukumomin Jihar shi ne farko, ya gangara zuwa cikin garin Kano. Har ya zuwa hada wannan rahoton al’amarin ya ja tunga da birki a garin Postiskum ta Jihar Yobe, kilomita 40 kafin garin na Dambam.

A ta daya bangaren, tun lokacin da aka samu musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ’ya’yan kungiyar Jama’atul Ahlul Sunna Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a garin Wudil ta Jihar Kano, abin ya gangara shi kuma ya nufi gabas, inda masu hasashe ke tunanin sai ya hada da jihar Borno, amma yana zuwa garin Azare sai ya ja birki, kilomita 60 kafin garin na Dambam.

Wannan hali na tsaka mai wuya da garin na Dambam ya samu kansa a ciki, ya kara kidima da sa shakku a cikin zukatan mazauna garin, ganin cewa shi ne gari daya tilo da ya rage a matsayin tudun mun-tsira a wannan tsakanin.

Wani abu da ya kara jefa rashin tabbas a zukatan al’ummar Dambam da kewaye shi ne, ba wani gari wanda yake ya kai Karamar Hukumar da suka hada iyaka da wanda bama-bamai ba su auka mata ba. Misali an kai hare-hare a banki da ofishin ’yan sanda da ke Misau kudu masu yamma da Dambam. An fasa na Azare da Bulkachuwa da ke mukwaftaka da Dambam ta bangaren yamma. Sai kuma Gamawa ta jihar Bauchi da ke Arewa da Dambam din, inda watanni da suka gabata ’yan bindigar suka ziyarce ta, sai Potiskum ta jihar Yobe daga Gabas, sai kuma Darazo wadda suke jingine da juna da Damban din ta bangaren Kudu.

Jibge sojoji da aka yi da kayan fada, ya sake sanya zukatan jama’ar cikin tsoro da fargaba, sai dai ba sun kakkafa shingayen binciken kwakwaf ba ne, amma dai zamansu a cikin garin da kuma shingen da suka sa kimanin kilomita biyar kafin shiga garin, ya sa mutane na tambayar cewa in ba rami, to me ya kawo zancensa?

A jawabin da Limamin Masallacin Juma’a na garin Dambam, Malam Baffah Yaya ya yi bayan kammala Sallar Juma’ar da ta gabata, ya dan kwantar da hankulan jama’a cewa mutane su ci gaba da addu’ar zaman lafiya da neman kariya daga Allah.

Wakilinmu ya dauko mana ra’ayi da hangen jama’ar garin, inda wani ma’aikacin lafiya da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa; “Ka don albarkacin zaman lafiya da al’ummar garin Dambam suea da shi, Allah zai ba mu kariya”.

Umar Tata ya raba wa matasa fom na ‘JAMB’ 400 a Funtuwa

Daga Husaini Baba

Ilimi shi ne ginshikin zaman duniya, kuma shi ne ke sa mutum ya zamo cikakken mutum, ya san kansa kuma ya amfani al’umma, kuma shi ne babban jarin da za a ba mutum ya amfana da shi, duniyarsa da lahirarsa.

Wannna ne ya sa matashin dan siyasa kuma mai kishin matasa da su zamo mutane nagari, Alhaji Umar T. Abdullahi (Tata) Dutsim-ma ya raba wa matasa fom na ‘JAMB’ na shiga Jami’o’i guda 400 a fadin Karamar Hukumar Funtuwa cikin jihar Katsina.

Nura Turaki Funtuwa, daya daga cikin wadanda suka wakilci Alhaji Umar Tata wajen raba fom din ya bayyana cewa, kishin da Tata ke yi na ganin matasa sun zamo mutane nagari, sun kauce wa bangar siyasa da zaman banza, shi ne ya sa Alhaji Umar Tata ya sawo wadannan fom na makudan kudi don tausayawa ga matasa, ya ba su kyauta tare da biyan kudin rijistar fom din.

Ya kara da cewa “A kullum shi burin Alhaji Umar Tata shi ne ya tallafa wa matashi ta bangaren karatu, kuma tun daga matakin firamare da sakandire da Jami’a. Ba a nan gudummuwarsa ta tsaya ba, hatta makarantun addini, Umar Tata na taimaka masu don yanzu haka ya sai wa makarantar Limamin Juma’a na cikin gari fili na miliyan daya da rabi, sai kuma ya sai fili don makabarta a BCJ na kimanin miliyan daya. Kuma ya gyara masallacin Juma’a da ke cikin Tudun Wada Funtuwa, da dai sauran ayyukan da ya yi”.

Da ya koma bangaren lafiya kuwa, Alhaji Nura Turaki ya bayyana cewa Alhaji Umar Tata ya samar da ruwa a asibitin Funtuwa, kuma ya kai gudummuwa a gidan yari na Funtuwa na tallafin hatsi, shinkafa buhu 25, sai gero buhu 10 da keken dinki da na saka, don tallafi ga wadanda ke tsare a kurkukun Funtuwa.

“Don haka, wannan tallafin da Alhaji Umar Tata ya kawo mana a Funtuwa, duk da shi ba dan Funtuwa ba ne dan Karamar Hukumar Dutsin-ma ne, ya nuna mana cewa lallai shi mai kishin garin Funtuwa ne. Muna fatan Allah ya saka masa da alheri, ya kare shi daga sharrin makiya da mahassada, kuma ya ci gaba da taimaka wa al’ummar wannan jihar tamu da kasa baki daya” a ta bakin Nura Turaki.

Wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Bello Abubakar da ke Funtuwa ya jinjina wa, Alhaji Umar Tata a kan yadda ya dau nauyin sai wa dalibai fom don shiga Jami’o’i, ya kuma bayyana cewa, da ana samun kamar sa a fadin kasar nan, da karatu bai gagari dan talaka ba. “Don yanzu haka wasu da dama lokacinmu rashin kudin fom ne ya hana su ci gaba da karatu, amma yau ga shi Allah ya kawo mana mai kishin talaka, mai son ci gaban matasa, ya sai fom ya raba kyauta, da yin rijista a intanet kyauta, wanda a yanzu ana sai da shi Naira dubu biyar da rijistarsa, kuma duk ya dau nauyi. Ina fatan matasan masu hali za su yi koyi da Alhaji Umar Tata wajen tallafa wa matasa ta janibin karatu”.

’Yan kasuwar da ba a bi bashi ne za su amfana da tallafi a Zamfara
Hon. Hasan Zurmi

Daga Husaini Baba

A kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi na ganin ta farfado da harkar kasuwanci a fadin jihar ta Zamfara, yanzu haka gwamnatin jihar karkashin Gwamna Abdul’aziz Yari, ta yunkuro don tallafa wa ’yan kasuwar jihar da bashin jari, kuma wadanda ba a bin su bashin ne kadai za su amfana da tallafin.

Kwamishinan kasuwanci da ma’sana’antu, Hon. Hasan Muhammad Zurmi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau.

Hon. Zurmi ya kara da cewa, wannan shirin tallafin don ganin bai samu nakasu ba, gwamnatin ta sanya shi a cikin kasafin kudi na wannan shekarar da muke ciki, kuma don haka ya sa gwamnatin ta yi hadin gwiwa da Bankin Masana’antu (Bank of Industries) don ganin hakarta-ta-cimma-ruwa, wajen farfadowa da harkar kasuwanci a fadin jihar ta Zamfara.

Hon. Hasan ya kara da cewa, bai wa ’yan kasuwa tallafi zai inganta tattalin arzikin jihar ta Zamfara, kuma matasa za su samu sana’o’in da za su yi.

Da ya koma kan batun wadanda suka ci bashi a baya kuma suka ki biya, Kwamishinan ya bayyana cewa babu makawa sai sun biya shi, don yanzu haka gwamnatin na bin wasu ’yan kasuwar bashin sama da miliyan talatin, don haka duk wanda ake bi bashi sai ya biya sannan a ba shi wani.

A karshe, Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da aka san su da kaunar juna da zaman lafiya da su kasance haka don babu abin da ke ci gaba ba tare da zaman lafiya ba. Kuma kada su yi gaggawa game da ayyukan da gwamnatin Gwamna Yari take yi, don shirye- shiryen gwamnatin na ganin ta bunkasa wannan jihar shi ne da shi Gwamna ke kwana kuma yake tashi. “Don haka nake kira ga al’ummar jihar Zamfara da su ci gaba da bai wa gwamnatinmu goyan baya da addu’a don ganin kudurinta ya hakkaku,” in ji shi.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan