Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



DANDALIN SISTERS

Ran maigida ya dade!

Daga Sakina I. Gwadabe (Mrs. Husaini Bala Alkurba) 0809 299 3786

‘Our Execellencies’, masu girma mazajen aurenmu, ababen alfaharinmu,wadanda muke taka rawa mu matan aurenku da bazarku. Yaya al’amura? Ya kasuwa ko aiki? Ya gajiyar tafiye-tafiye ko fatauci? Leburanci ko dillanci? Kananikanci ko dukanci? Muna rokon alherin Allah (T) da albarkarsa su kara karuwa gare ku, da gurbin sana’arku, komai girma ko kankantarsa.

Ya masu girma! Masu girma mazajenmu, ababen kaunarmu, kawukanmu bisa wuyayanmu! (Mu matan aurenku), mun zo da kokon bara, muna rokon a duba, a yi gyare-gyare a kan kurakuren yau da kullum da muke fuskanta daga gare ku; wadanda a zahiri suke ci-mana-tuwo-a-kwarya; a halin zamamtakewarmu da ku.

Ran maigida ya dade! A gaskiya, ranar wanka ba a boyon cibi, korafe- korafen da muke tafe da su, da tuhumomin da muke maku suna da yawan da ba za mu iya zayyana su duka ba, amma in har kuka yi gyara na hakika a kan matsalolin da ke tafe, lallai za mu hakura mu kau da kai a kan sauran.

Yallabai! Mu matanku, za mu zama masu matukar alfahari, idan mazajenmu suka zama masu tsantseni da gudun sabon Allah. Domin halin mutum naso yake yi, zai iya naso mu, mu raunanan makusanta da zuri’ar da Allah ya albarkace mu.

Ya maigirma! A matsayinka na matafiyi kuma jagora, mai manufa da sanin inda aka dosa, mu ababen kiwonka, muna matukar kishin ruwan ganin cewa kun ja mu zuwa ga hanya mai bullewa, tare da kyakkyawar guzurin da zai kai mu ga samun yardar Allah (T).

Yallabai! Dole fa sai ka gyaru, sannan za ka iya gyarawa! Ya mai girma, rashin damuwa da al’amuran da suka dame mu, yana bakanta mana matuka, musamman in muna cikin wani hali da muke bukatar lallashi, da ban baki, ba za mu so a yi shakulatin bangaro da al’amarinmu ba. Duk da cewa sannu ba ta maganin ciwo, amma fa yallabai tana da dadi.

Yallabai! Zan buga misali da al’amarin da wasu mazan suka fi rawar-kai da doki a kai, shi ne kara aure. Lamarin kishiya ko in ce mata Amarya, yana da radadi a zuciyar duk wata ’ya mace (uwargida), duk imaninta kuwa. Amma mun sani cewa, ba mu da ikon hanawa tunda Allah (T) ne ya ba da damar yi, kuma ya halasta ga ma’abocin adalci. A irin wannan yanayi, babban abin da muka fi bukata daga gare ku shi ne adalci, da lallashi da ban baki, da rashin nuna fifiko. Ko da kuwa an sami wani canji ko ci gaba na jin dadi da annashuwa daga Amarya, bai kamata muraran ka nuna fifikon da uwargida za ta gane ba. Wannan wani sirri ne da ya kamata ka bar shi a zuciyarka, domin dukkansu suna karkashin kulawarka ce. Ka auna ya maigirma! Da a ce Allah ya halasta wa matarka auren namiji fiye da daya, don Allah ya za ka ji a ranka? Ranar da matarka ta bar ka, suka kebe da sabon Ango kuma kana cikin gidan!

Ya maigirma! Alakarmu da iyaye, ’yan uwa da danginka ya ta’allaka ne kamar yadda kai ka dauke su, rashin ba su muhimmanci da kulawa da su gwargwardon iko, yana iya raunana dangantakarmu, mu matanku da su. Za mu so a dinga karfafar mu, a tallafa mana wajen kulla kyakkyawar alaka mai dorewa da iyayenka da sauran danginka.

Yallabai! Sau tari muna fuskantar matsaloli da abokan zama da makwabta! Wannan abin takaici ne matuka; wanda kuma yawanci hakan na faruwa ne sakamakon raunin alaka ko danganta tsakaninsu da mazajenmu!

Yallabai! Kyautata alaka da makwabta, umarni ne na Manzonmu (S), kamar yadda nakan ji daga Malamai.

Ran maigida ya dade! Abin bakin ciki ne matuka gaya a gare mu, rashin daukar iyayenmu (mu matanku) da ’yan uwanmu da kimar da ta dace! Wannan lamari yana ci mana tuwo-a-kwarya! Kuma hakan yana raunana kimarku a zuciyarmu mutuka, domin akwai kuna da zafi, kuma gagarumar matsala ce da kan kawo raini da rashin girmamawa! Na sani Yallabai, da akwai da yawa mazan da ba su cikin wannan layi, suna kamantawa. Amma dai muna fatan ma’abota wannan hali, za su duba kuma su gyara.

Ya maigirma! Alhakin tarbiyyar ’ya’yanmu fa ya rataya ne a wuyanmu duka! Na san ka san wannan. Ba kankanin kuskure ba ne, sakarwa mace ragamar tarbiyyar ’ya’ya, komai karancin adadinsu kuwa. Na’am, mune kashin bayan tarbiyyar al’umma, amma muna takaicin ganin cewa uba bai damu da binciken al’amarin da suka shafi tarbiyyar ’ya’yansa ba!

Ya maigirma! Tarbiyya a yau gagarumar aiki ne da ya fi karfin rai guda, matukar ana bukatar samar da al’umma mai inganci da nagartar da za a iya alfahari da haihuwarsu, ko da bayan ran iyayensu ne.

Yallabai! Gawurtaccen sirri maigirma na tattare da kyautatawa da farantawa iyali. Sahabin Manzon (S), Sa’ad Ibn Mu’az, yana daya daga cikin Sahabban da ake girmamawa; lokacin da ya mutu, Annabi (S) ya jagoramci jana’izarsa babu takalmi, kuma ba tare da alkyabbarsa ba, don nuna damuwarsa. Annabi (S) da kansa ya sanya Sa’ad cikin kabari ya yi masa addu’a, kuma ya ce Mala’ika Jibril (AS) tare da wasu Mala’iku (AS) sun halarci jana’izarsa. Amma lokacin da mahaifiyarsa ta ce: “Ya Sa’ad hakika ka ci sa’a, don Annabi ya yi tafiya ba takalmi zuwa jana’izarka, kuma har ya sanya ka cikin kabarinka…sai Manzo (S) ya umarce ta da ta yi shiru kuma ya ce: ‘Ba za ki iya kare shi daga wahalar azabar kabari ba’. Sa’ad bai yi kyakkyawar mu’amala da iyalansa ba. Saboda haka yanzu yana nan yana shan wahalar matsewa na kabari.”

Hakika mu matanku da Allah ya danka amanarmu a hannunku, mukan tsinci kawukanmu cikin damuwa da takaici, in aka yi rashin sa’a matsolanci da rowa suka addabi zukatan mazajenmu, wanda hakan kan haifar da gurbacewar zama! Kyautatawar da muke bukata ta hada da: Kokarin ciyarwa mai kyau, irin cimakar da kake yi, tufafi gwargwadon iko, tamkar yadda za ka yi taka, sauyin abinci mai dadi idan hakan ta taso, misali; idan aka sami wani budi ko kasuwa ta yi kyau, lokacin zuwan wadansu muhimman ranakun a Musulunci (kamar ranar Idil Ghadir, Ranar Idil Fitri da Kabir, ranar 17 ga Rabi’ul Awwal, Yaumu Zahra (AS), ranar Juma’a, da sauransu). Akwai kuma bukatar bayar da isasshen kudin cefane, daukar iyali zuwa wurin shakatawa akalla sau daya a shekara, kyauta ta kudi ko kuma wani abin sha’awa lokaci zuwa lokaci, dinkawa iyali cikakken Hijabi na Shari’a, musamman a lokuta na musamman kamar: ‘Idil Fitr, Idil Kabir da Ghadir, ranar Ashura, da Maulidin Manzo (S).

Sauran sun hada da Maulidin Nana Zahra (AS), sai Nisfu Sha’aban da sauransu. Na karshe kuma, sai kamar ba da kyautar katin waya a lokaci zuwa lokaci. Gudummuwa iyakar ikonka idan wani sha’ani ya shafi matarka, misali: ‘Bikin aure, taron zaman makoki, bikin radin suna da kuma rashin lafiyar uwa, uba, ko ’yan uwanta.

Ran mazajenmu ya dade! Kuna kara shiga ranmu ne, tare da kara kima da martaba a zukatanmu yayin da kuka zama ma’abota sirranta aibobinmu idan muna da su, tare da boye dukkanin sirrikanmu da ke tsakaninmu ga ko waye. Bai kamata tsananin abota ko ’yan uwantaka ya sanya ka zama ma’abocin yada sirrikan iyalanka ba, kuma wannan dabi’a tana da kyau a kiyaye ta a lokacin da ake tare da iyali ko bayan an rabu, wanda ba ma fatan rabuwa.

Yallabai! Abin girmamawa a gare mu, na san ka sane cewa a kowace irin zamantakewa a kan sami sabani a tsakani (lokaci zuwa lokaci), balle kuma zama da mu mata raunana, masu gajeren tunani, ajizai, ma’abota kasala da mantuwa; muna bukatar tallafin hakuri da mu da halayenmu, muna bukatar saiti, nuni, hani, umurni, gargadi da kuma kyakkyawan jagoranci daga gare ku, ya ku mazajenmu, ababen kaunarmu, wadanda Allah (T) ya sanya mu a karkashin kulawarku.

Ya maigirma! Yallabi ran gida!! A duk lokacin da muka aikata wauta, kuskure, ta’asa, saunanci ko barna, kuma muka cancanci a yi mana fada ko a tsawatar, ya maigirma, muna son a rinka fakon idon yaranmu sannan a yi mana, ba mu san ko kadan yara su ji su fahimci wani sabani, ko rashin jituwa a tsakaninmu; domin kuwa hakan baraka ce babba! Duk inda rai ya kai ga baci, mu daure mu boye sabanin da ke tsakaninmu ga yaran da Allah ya azurta mu da su, komai karancin shekarunsu, ko adadinsu kuwa.

Na taba cin karo da hoton wani yaro dan shekara 10, a kan irin wannan matsalar a wani filin amsa koke da warware matsaloli mai suna: ‘GRANDPA’S GOLDEN KEY’, a mujallar Zamzam English Magazine da ake bugawa a birnin Tehran na Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Yaron ya rubuto matsalarsa ne ga ‘GRANDPA’S’ (shi mai gudanar da filin). Ga abin da yake cewa: “Zuwa ga ‘Grandpa’s’, na sami labarin kana amsa tambayoyi, tare da warware matsalolin masu karanta ka. Babbar matsalar da ta dame ni a rayuwata, kuma take haddasa min damuwa da rashin walwala ita ce, yadda iyayena suke yawan yin fada da junansu a gabana. Kullum sai sun yi fada, wannan ya shafi al’amarin karatuna, ka taimake ni ‘Grandpa’s’.”

Wannan lamari na wannan yaro, ya dade yana bakanta min rai; kodayake ‘Grandpa’ ya yi kokari gaya wajen kwantar da hankalin yaron, tare da jan hankalin iyayen nasa, amma na sani cewa wadannan iyaye sun sami barakar da ba su da telan da zai iya dinke ta.

Ran maigida ya dade! Muna bukatar a duk lokacin da aka bukace mu, wajen aikata Sunna, a dinga mutunta mu, tare da kimanta mu a matsayinmu na ’ya’yan Adam sabanin dabbobi. Mataye da yawa na fuskantar irin wannan matsala kasantuwar ana kokarin aikata Sunnar Manzo (S) ne tare da kyakkyawar fatan samar da zuri’a mai inganci da tsoron Allah, ya kamata a irin wannan yanayi a dinga yawaita amfani da hanyoyi na jan hankali tare da aikawa da ’yan sakwanni, sabanin masu aikata laifi ko sabon Allah.

Yallabai! Wani abin takaici da wasunmu da wasu mata ke fuskanta daga mazajensu, shi ne rashin tsafta ta kowane bangare! Musamman tsaftar jiki, hakora da sauran wuraren da ake kira (private parts). Kamar yadda muke ta shan korafe-korafe a kan rashin tsaftacewar mazajenmu jikinmu, to a gaskiya mu ma muna bukatar hakan daga mazajenmu. Babu dadi ko kadan namiji ya zama kazami a tsakanin iyalinsa. Wata mace ta taba gaya min a hira cewa: “Ita mijinta a gaskiya ya dauke mata komai na bukatar rayuwa, amma tana fuskantar matsalar kazanta matuka gaya da shi.” Ta ce; “Sau tari zai dawo gida da dare yana karni da wari, don saboda yanayin sana’arsa, amma a haka zai ci abinci kuma ya yi kokarin kwanciya. Sai na yi da gasken-gaske zai wanka. Shi kuma rashin fahimta ya sa yake zargina a kan ina kyankyaminsa da sana’arsa”.

Ya masu girma! Muna fatan daga matakan da za a dauka na gyara, gaskiya muna so a dabbaka bangaren gyaran jiki, yankan farata, gyaran hakora da yawan wanke su, aske suma da gyaran fuska, da aske duk wani gashi da barinsa a jiki yake alamta kazanta.

Ran maigida ya dade! Akwai wata matsala da take ci-mana-tuwo-a-kwarya, mu matanku, a halin zamantakewarmu. Zan so Yallabai ya tuna da cewa, kamar yadda muke bukatar nusarwa da zaran mun yi wani kuskure, to haka muke bukatar da zaran mun faranta muku, muna son a nuna mana a fili a aikace cewa mun burge! A gwarzanta mu. Wannan ne zai kara mana kaimi da karfin gwiwar ci gaba da faranta muku.

Ya masu girma! Yallabai ababen girmamawa a gare mu!! Muna masu kara jaddada biyayya da ban girma a gare ku; a zahiri ku ne mafiya kusanci a gare mu fiye da kowa namu, ku ne muka mika wa dukkan lamurranmu, ku ne uwa da ubanmu, ku ne abokan shawararmu, ku ne muke taka rawa da bazarku, muke farin ciki da walwala da farin cikinku, muke bakin ciki da damuwarku, muke alfahari da arzikinku. Hakika muna matukar bukatar kulawarku, taimakonku da tallafinku a kodayaushe.

A karshe, ya masu girma mazajenmu! Karfafa mana gwiwa da tallafa mana a kan yin karatu (na boko da na addini), da fita aiki; ba gazawa ba ce, ko ba komai za mu iya zama ababen alfaharinku a nan gaba, ko da kuwa amfanin karatun namu zai takaita ne ga ’ya’yanmu kawai. Ku tuna ba a taka kowane irin mataki a rayuwa, sai da ilimi, kuma ana neman ilimin ne daga ranar haihuwa zuwa ranar mutuwa, (kamar yadda ya zo daga A’imma Alaihimus Salam).

Ya ku mazajen aurenmu! Ababen kaunarmu!! Muna fatan daga yau za mu ga canji, kuma muna rokonku gwiwowinmu a kas, a kan ku kawar da wadannan abubuwa masu zuwa daga zukatanku:

1. Zargi.

2. Huce haushin wani a kan mace

3. Rashin tausayawa da tausasawa.

4. Rashin hakuri da mu.

5. Rashin fahimtar mu.

6. Rashin ilimi.

7. Rashin sanin kima da darajar aure.

8. Rashin kishinmu.

9. Daukar munanan shawarwari daga munanan abokai.

10. Rashin biya wa iyali bukatu.

11. Adalci tsakanin mataye.

Kada ku manta ya ku mazajenmu! Kauna ce ta hada mu, don haka komai tsufa da dadewa bai kamata a manta da mutunta juna da bai wa juna hakkokin da suka dace ba.

Yallabai! Na bar ka lafiya da fatan alheri, karuwar arziki, ingantacciyar lafiya, samun kusanci madawwami da Mahalicci, Manzo (S), A’imma (AS), da kuma samun mafi kololuwar daraja da sa’ada a yayin mutuwa (Shahada). Sai mun hadu a kashi na biyu da za mu bankado matsalolin uwargida ran gida, da nufin ta ji ta gyara.

Ni ce taku har kullum, Sakina I. Gwadabe.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan