Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



DANDALIN SISTERS

Matsalarmu mu mata a yau

Daga Jamila Isyaku

Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarkin da ya ba ni ikon tunatar da mu matsalolinmu mu mata a yau. Allah ya yi dadin tsira ga Manzon Allah (S) da Alayensa da sauran al’umma mabiya.

Nasihata gare mu mu mata ita ce, halayen wasunmu na zuwa gidan bokaye da asirce mazajen aurenmu, ko yi wa kishiyoyinmu sihiri don shiga wani hali na daban don son zuciya.

Ya ’yar uwata! Ina mai tunatar da mu abin da yake dole ne a gare mu shi ne mutuwa. Ko mutum yana so ko ba ya so, mutuwa wajiba ce a gare shi. Haka kuma dole in za ki yi rayuwa ta banza ce, matsawar ba mu bi rayuwarmu bisa tafarkin Allah (T) ba. In har mun bar duniya ta rude mu, to hakika komai dadewa za mu tafi mu bar ta. Abin kuma da muka shuka shi za mu girba, daidai da abin da muka aikata. Shi ya sa nake mana tuni da mantuwar da dan Adam ke da shi.

Ina mai tunatar da mu a kan matan da ke jefa ’yan uwansu mata cikin tsaka-mai-wuya, tana rayuwa sakamakon kokarin ganin bayanta da za ta yi, sakamakon hada miji daya saboda kishi da ya yi mata yawa.

Alal misali, ya ke ’yar uwata! Menene jin dadin mace da za ta raba ’yar uwarta mace da mijin aurenta ta hanyar sihiri? Abin da ke faruwa wata mijin korar ta yake yi ba cikin hankalinsa ba, wani kuma kauracewa matar yake yi, ba-shi-ba-ta. Wani kuma ga ta a matsayin matarsa, amma ba ruwansa da ita. Wani ma har da ’ya’yanta ko da kuwa ta haifi gari guda ne, sai dai ya dubi waccen, ita wannan babu ruwansa da ita. Wata kuma sai a dora mata lalurai ko ta rashin lafiya ko ta zubar jini ko ta haukatarwa, ko kuma a neme ta a rasa, ta shiga duniya. Wata kuma sai ki ji an mata sihirin da za ta shiga yawon banza, sai ta je ta yi yawon, sannan ta dawo tana kuka. Kai mata mu ji tsoron Allah, ta yiwu shi ya sa Annabin Rahama (S) ya ce, ya gan mu mu mata mun yawaita a wuta.

To, hakika wannan hali namu yana da nasaba da abin da zai sada mu da fushin Ubangiji Madaukakin Sarki, wanda in ba mu yi wa kawunanmu fada ba, hakika za mu shiga tabewa a cikin wannan rayuwar wadda ba ta da tabbas.

Ya ke ’yar uwata! Ki ji tsoron Allah, ba komai a duniya sai rudu da aikin da-na-sani. Ina mai tunatar da mu mu ji tsoron Allah mu kyautata halayenmu, wanda ta aikata daya daga abin da na fadi a baya, ta yi saurin tuba ga Allah da wannan baiwar Allah da ta cutar. In auren ya rabu ta yi saurin tona gaskiyar abin da ta aikata, don tsira ranar kiyama. Domin kunyar kiyama ita ce babbar kunya, ba ta duniya ba.

Ya ke ’yar uwa! Aure dai ba abin wasa ba ne, domin Annabin Rahama (S) ya ce a yi aure a hayyayafa ranar kiyama zai yi alfahari da mu. Ya ke ’yar uwata! Yaya za ki zama mai adawa da Sunnar Annabi (S) saboda son zuciya, domin mafi akasari a cikinmu ba wai jahilci ko rashin sanin illar bin bokaye ba ne yake sa suna zuwa don aikata sharri ga abokan zamansu ba. A’a, suna zuwa ne kawai don son zuciya da zalunci da ya yi musu kaka-gida a cikin zukatansu, amma ba don rashin sani haramcin abin ba.

Haka zalika, ina gargadi ga yara matan da ke bin bokaye don neman mazajen aure alhali wata ga mijin Allah ya kawo mata, amma sai ka ji ta ce; “Ina da kishiya gara a mallake min ita, in na shiga sai abin da na ce za a yi a gidan”. Wata ma sai ka ji tana furucin; “Wallahi in na aure shi sai ta bar gidan ko da zan rasa komai nawa, in dai har Malam ya tsaya ya yi min aiki, kamar ta bar gidan ta gama”. Wata in ta tashi yin mugun abin, har da yaran matar za ta hada.

To, tsakani da Allah, ya ke ’yar uwata! Kun yi gaskiya ke nan? Kuma za ki kira kanki mace tagari ke nan? Kin ce kina son shi, kin aure shi, kin zo kin raba shi da matarsa da ’ya’yansa. Ta yiwu kuma kafin ki zo gidan, matar ta dade tana wahala tare da shi. Amma ya samu budi lokaci guda, ke kuma kin shiga kin tarwatsa su. To, ke ’yar uwa yanzu sai ki ce Allah zai bar ki. Kin ga komai daren dadewa sai kin hadu da sakayya, sai kin ga mijin ya yi miki saki, kin zama bazawara. Alhali halinki ya jawo miki. Wani kuma sai a kwashe dogon zamani suna tare ba tare da ta samun matsalar komai ba, saboda kin nemo duniya kin kuma samu. Allah ya tsare mu da mace mai wannan halin, amin.

Haka zalika, wata saboda rashin imani ta zo ta sami uwargida da mijinta suna zaune lafiya, amma zuwan Amarya ta sihirce mijin sakamakon baki dayansu ba a gida daya suke da uwargidan ba. Duk lokacin da kwanan uwargidan ya zo, sai makuwa ta sami mijin ya kasa gane gidan ita uwargidan. Sai dai ya gaji da yawonsa na neman gidan, ya dawo gare ta ita Amaryar tunda daman sihirin don haka ta yi shi. Kai jama’a! Karshe ma kodayaushe yana gidan Amaryar, ya kuma kyale uwargidan ba ruwansa da ita, ga shi kuma bai sake ta ba, ya bar ta da ’ya’ya.

Ya ke ’yar uwa! Me kike nema a duniya? Ba kya tunanin mutuwa zuwa take ba tare da sanarwa ba? Shin in ta riske ki a kan wannan bata da kike shigar wa kanki, me za ki ce wa Allah? Shi ke nan ko rayuwarki kin yi ta a banza, kin cutar da mijinki, kin cutar da ’yar uwarki?

Kai mata ’yan uwana! Halayenmu munana sun tsananta sakamakon mafi yawa daga cikinmu na aikata mugayen kaba’irai a kan mazajen aurenmu da kuma abokan zamanmu. Mafi akasarin wasu matan sai su hana mazajensu aure, amma su sun yarda da su je su nemi mata a titi da a kawo masu matar Sunna. Su gara mijinsu ya yi hulda da matar banza. Wa’iyazubillahi.

’Yar uwata! Ba ki yin tunanin sauyin zamani da irin halin da rayuwarmu take ciki yanzu? A tunanina, inda an wajabta auren mata dubu zan amince da kara aure a kan in ga mijin aurena na bin matan banza. Amma sai ki ga wasu matan na cewa; “In dai zai ba ni abin da nake so, to ya nemi dubu mana. Ina ruwana, ai shi ya ga zai iya”. Ke ba kya tunanin ke ce mutum ta farko da zai cutar ya kuma bar miki gori a doron kasa, kuma ya bar abin fadi a cikin zuriyarsa? ’Yan uwana ku kiyaye abin da zai zama gori ga tsakanin zuriyarku.

Wani namijin ma yana da suriki, to in mijin ’yarki na aikata irin halinka, ya za a yi ta yi masa nasiha ya saurare ta, bayan ubanta na yi? Mafi akasarin iyaye maza na cusa wa ’ya’yansu mata bakin ciki a gidajen aurensu. Wata ubanta matan banza yake bi. Wata rana sai su hadu da surkinsa a can inda suke daukar mata. Kai iyayenmu! Yaya za a yi mazajenmu su darajta mu? Yaya za a yi su saurari nasihar da za mu yi masu? Don haka, ina rokon ku masu wannan halin, don Allah don Annabi su nema mana mutunci a gidajen aurenmu.

Haka zalika wasu matan bokaye suke bi da Malamai kan a rufa masu bakunan mazajensu, saboda su rika fita suna neman mazan da ba nasu ba, suna kuma cin amanar mazajen aurensu, saboda zalunci da cin amana irin nasu. A halin yanzu mu mata mun shiga halaka ta hanyar kuntata wa mazajen auremu ta hanyar asirce su, da sihirin da za mu aiwatar da komai ba tare da sun dubi abin da muke yi ba.

Wasu matan duk yadda suka kai ga musgunawa mazajensu ba za su taba duban abin da suke yi ba, saboda sun san abin da suke yi masu ba tare da sanin su ba. A zamanin da muke ciki yanzu, wadannan al’amurra suna faruwa ga dukkan kabilun da ke rayuwa a wannan duniya tamu, sakamakon hakan ba a kabilunmu na nan kawai abin ya tsaya ba. Don haka, ina mai jan kunne a gare mu mu mata, mu kiyaye aikata wadannan mugayen halaye namu, wanda mafi akasarinmu shi zai kai mu wuta. Kuma duk matar da ta yi sanadin zuwan mijinta wuta sakamakon jagorancin da ta yi masa har makomarsa ta kai su can, to hakika kin cuci rayuwarku, kuma duk shekarun da kika yi a doron kasa, hakika kin tabe. Wanda rashin zuwanki duniya ya fi zuwanki amfani. Kaico! Allah ka yi mana tsari da irin wadannan mataye, amin.

Haka zalika, a irin wannan halayen namu yakan sa ’ya’yanmu su taso su lakanci irin abin da muke yi, su ma sai ki ga sun tashi da mummunar tarbiyya. Alal misali, kamar yadda wasu iyayen ke tura yaransu gidan Malamai don karbo masu sako, in mai gidansu bai bari sun fita a ranar ba. Ga shi kuma Malamin ya tabbatar mata ta zo a ranar, za ki ga ta aiki yaransu masu karancin shekaru. Ki ga yaro ko yarinya tun tana karama ta san gidan Malamai, in namiji ne tun yana yaro zai taso da sanin muhimmancin Malamai. A haka rayuwarsu za ta tashi, duk wani abu da za su yi sai sun fuskanci gidan Malamai, kafin su mai da hankalinsu a kan duk abin da suka sa a gabansu. Wa’iyazubillahi. Allah ka shiryatar da mu a bisa halayenmu baki daya.

Sakamakon wannan, halin namu kan sa mu manta Ubangijin da ya kage mu, ga shi kuma muna Salla, muna Azumi, muna Zakka, kuma duk wanda Allah ya kira cikinmu mukan ziyarci Dakinsa. Amma dukkanin al’amuran duniya mukan manta da shi, mu mai da tunaninmu a kan duk wani kalami da bokayenmu ke sanar da mu. Shi ya sa muke fadawa masifa kala-kala, a tsakaninmu, domin Allah (T) ya ce: “Duk bawan da ya kasance da ni, ni ma zan kasance da shi, duk wanda ya manta da ni, ni ma zan manta da shi.” Amma kuma yana ganin mu. To, wannan halin namu shi ya tarwatsa rayuwar mataye da dama, har wasu daga cikinmu kan fadawa rayuwar hatsari irin na wannan zamani, wanda duk cikakken mai tunani da ya san abin da yake yi, addu’a ce kawai za ta yi mana tsari ga wannan zamani da muke cikinsa. Allah ka shirye mu shiriyar addinin Musulunci, amin.

Haka kuma, ina kira ga iyayenmu maza da mata da suke bar ma ’ya’yansu abin kunya. Ya ku iyayena maza da mata! Ku tsare mana mutuncinmu mu ’ya’yanku, ku yi kokarin barin alheri a tsakaninmu, ku tsare mutuncin zuriyarku, a duk inda kuke. Wanda hakan zai sa babu wani mahalukin da zai goranta mana mu ’ya’yanku. Misali, akwai wasu iyaye daga cikinmu masu fita yawon bin matayen banza a gidajen banza da ke jihohi da dama. Hakika wannan na zama mana bakin ciki a gidajen aurenmu ga masu aure, in kuma samari ne yakan zama masu abin gori a gidajen surukansu.

Ga misali, wannan mahaifinki ya kasance mai irin wannan halin, sai kuma Allah ya jarabce ki da mijin aure mai irin wannan hali. To, a zahirin gaskiya ba zai dauka ba in ba Allah ya shirye shi ba. Wannan matsala na yawan bata wa mata tunani ta yi masa nasiha, sai ka ji ya ce “Can muke haduwa da mahaifinki, har kin isa ki sa ni in daina? In kuwa kina so in daina, ki je ki sanar da ubanki ya daina, ni ma sai na daina. Tunda guri daya muke haduwa, in ya daina sai in bari, in bai bari ba, ni ma ina nan a hanya”. Haka na faruwa sosai, domin isharorin Ubangiji da yake sauka a tsakaninmu mu mata ne, domin Allah shi ke fid da mai rai a cikin matacce, ya fitar da matacce a cikin mai rai. Domin ikonsa ne kuma yadda ya so hakan zai yi. Shi ya sa wasu iyayen kan haifi yaran da suka fi karfinsu, sakamakon ba su gina wa kansu rayuwa ta-gari ba.

Wasu kuma halayen kwarai gare su, amma sai Allah ya jarabbe su da fitinannun ’ya’ya a tsakaninsu. Shi ya sa duk mutumin da Allah ya yi wa baiwa da Musulunci (ma’ana ya fito a tsarin Musulunci), to ya gode wa Allah, ya kuma tsaya daidai karfinsa ya bauta masa, ba tare da ya hada shi da wani ba, ko ya bar duniya ta rude shi. Hakika sai mun yi yaki da zuciyarmu, sannan za mu nisanta da aikata miyagun ayyuka. Allah ka shiryatar da duk al’ummar Musulmi baki daya ta hanyar tafarki madaidaici, amin.

Sayyida Zainabul Kubrah: Babbar abar koyi ga mata Musulmi

Daga Bilkisu Yusif Maitaya Kano

Da sunan Allah, Mai Girma da Daukaka. Sarkin da ya aiko Manzo da shiriya da addinin gaskiya. Amincin Allah da Rahamarsa su kara lullube Manzon Allah (S) da Ahlul Baiti Tsarkaka (AS), musamman Sayyidah Zainabul Kubrah, wadda nake wannan rubutu a kanta.

WACECE ZAINABUL KUBRAH?

Sayyida Zainabul Kubrah ’Yar Fatimah (AS), ’Yar Manzon Allah (S), ’Yar Imam Ali Bin Abi Talib (AS).

Sunanta na hakika Zainab, ana yi mata Alkunya da Ummu Kulthum, ko Ummul Hasan.

Ana yi mata lakabi da Akilata Bani Hashim’, wato abar girmamawa, mai cikar hankali, mai girma madaukakiya a gidanta.

An sami ruwayoyi mabambanta game da shekarar da aka haife ta, wasu na cewa an haife ta ne a shekara ta 5 bayan Hijira, a watan Jimala Ula. Ita ce ruwaya mafi rinjaye. Ruwaya ta biyu, an haife ta shekara ta 6 bayan Hijira.

Sayyidah Zainab ta taso a Gidan Annabta, gidan da wahayi yake sauka. Ta sami kyakkyawar kulawa da tarbiyya daga Babarta, Sayyidah Fatimah, ’Yar Manzon Allah (S). Tana da kyawawan halaye da ladabi. Tun tana karama ta haddace Alkur’ani mai tsarki. Ta sami ilimi mai zurfi a wajen Babarta, Sayyidah Fatimah (AS), kamar yadda ta ma shawo daga Babanta, Manzon Allah (S).

Sayyidah Zainab ta haddace Hadisan Manzan Allah (S) masu yawa. Ta san hukunce- hukuncen addini, ilimin tarbiyya, tarihi, dss. Allah ya azurta Sayyidah Zainab da siffofi kyawawa daga cikinsu akwai:-

1. Imani tabbatacce: Tana da matukar imani na kololuwa, in ana maganar imani, Sayyidah karshe ce a imani.

2. Allah Ya azurta ta da hakuri matuka, wanda Kakanta, Manzan Allah (S) ya ladabtar da ita. Sayyidah Zainab ta kasance mai yarda da abin da Allah ya dora mata, kuma mai hakurin

bala’o’in da ta gani a rayuwarta. Allah (T) ya yabi wadanda suke da wannan siffa ta hakuri a Ayoyi masu yawa: “Ku yi wa masu hakuri bushara, wadanda in wata masifa ta same su za su ce ga Allah muke, kuma gare shi za mu koma.”

3. Al-Izzah wal karama: Allah ya azurta ta da girma da daukaka.

4. Zuhdu: Wato taka-tsantsan cikin sha’anin duniya da barin kawace-kawacenta. Wannan tarbiyya ta gudun duniya ta samo ta ne daga Mahaifanta, Imam Ali (AS) da Sayyidah Zahra (AS). Imam Ali (AS) ya yi wa duniya sakin da ba a komawa. Mahaifiyarta duk da

kasancewarta ’Yar Manzon Allah (S) ba ta mallaki komai ba, daga tabarmar Salla sai akushi

na abinci da bargo (kisa’i).

Rayuwar Sayyidah Zainab ta zama babbar abar koyi ga mata Musulmi, domin gidanta ya zama wani waje ne da ake Tilawar Littafin Allah mai girma, da koyar da ilimin addini da hukunce-hukunce da tarbiyya, da sauran ilmummuka.

AURENTA: Mijin Sayyidah Zainab shi ne Awn Bin Ja’afar At-Tayyar.

WAFATINTA: Sayyidah ta yi wafati a shekara ta 62, wata shida bayan dawowarsu Madina.

INDA AKA BINNE TA: Babu takamaiman wajen da aka binne ta, wasu sun ce tana Damashk (Siriya).

Tarihin Sayyidah Zainab ba zai kammala ba, sai mun dan tabo abin da ya faru a Karbala. Bayan su Imam Husaini (AS) sun yi shahada, ta je inda jikkunansu masu tsarki tana cike da imani da kadaita Allah, ta ce: “Allah ka karba mana.” A daren 11, Sayyidah ta yi Sallar godiya ga Allah a bisa abin da ya dora mata na ganin masifu. Babu wata mace a cikin al’ummar Manzo (S) da ta ga bala’in da Zainab ta gani.

ABUBUWAN DA SAYYIDAH ZAINAB TA KOYA MANA:

*Muhimmanci hakuri a rayuwa da mai da komai ga Allah.

*Muhimmancin Sallar dare, domin ita ce sirrin bayin Allah.

*Muhimmancin isar da sako (TABLIG). A kan hanyarsu ta koma Madina, ta ci gaba da yi wa mutane bayanin gaskiyar abin da ya faru a Karbala, wanda hakan ne ya sa da dama daga cikin mutane suka dawo cikin hayyacinsu har suka fahimci hakikanin gaskiyar abin da ya faru.

*Muhimmancin neman ilimi, koyar da shi, da aiki da shi.

*Muhimmancin dauriya a tafarkin Allah. Duk abin da zai same mu, in dai a tafarkin Allah ne,

mai kyau ne. Rayuwarta gaba daya ta kare ne cikin ibada, kuka, da bakin cikin abin da ya same su.

Amincin Allah da Rahamarsa, su kara lullube ki ya Zainab!!!




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan