|
|
Juma'a 10 Ramadan, 1431 Bugu na 939 ISSN 1595-4474 |
|
|
|
Kungiyar Dalibai Musulmi ta kasa (MSSN) reshen ‘Government Day Junior Secondary School Dorawa-Potiskum’ (GDJSS) sun yi gagarumar walimar kammala karatunsu na matakin aji uku a harabar makarantar da ke unguwar Tandari a cikin garin Potiskum.
Ita dai wannan walima, wadda aka saba yinta duk lokacin da dalibai suka kammala karatu, ta samu halartar jama’a da dama daga ciki da wajen garin na Potiskum.
Babban bako mai jawabi a wajen shi ne Malam Ibrahim Lawal, Head Master na Madrasatul Fudiyya Potiskum.
Malam Ibrahim Lawan ya yi jawabai masu gamsarwa da ratsa jiki. A cikin jawabin nasa, ya yi nasihohi a kan su dage da karatu, su kasance masu biyayya ga iyaye da kyawawan dabi’u a ko’ina suke. Sannan ya gargadi yaran a kan su guji bangar siyasa, wanda ba komai bane a cikinta sai halaka.
Wakilinmu ya zanta da Shugaban MSSN na makarantar (patron), Malam Musa Kawu, inda ya shaida masa cewa, shekaru uku kenan da fara yin wannan walima, kuma muna samun hadin kai daga wajen Shugaban makarantar, Malaman makarantar da kuma su kansu daliban makarantar.
Ya ci gaba da cewa, “a shekaru uku da muka yi muna yin wannan walima daliban wannan shekara sun fi na kowace shekara kokari da kula da lamarin MSSN na wannan makaranta, domin kuwa sun sayawa wannan makaranta manya-manyan taburmai na Salla na Naira dubu 10”.
Sannan ya ce: “A cikin irin namijin kokarin da wadannan dalibai suka yi shi ne akwai wata daliba da ta yi sanadiyyar Musuluntar wata kirista a wannan makaranta.”
Sannan ya yi musu addu’ar Allah Ya ba su nasara a makarantun da za su jona a gaba, wadanda kuma za su yi aure, Allah Ya ba su mazaje nagari. “Tarbiyyar kuma da muka koya musu, Allah Ya sa su dore a kai har karshen rayuwarsu,” in ji Malam Musa Kawu.
Daga M. Umar Saye
Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Bauci, Alhaji Mukhtar Ahmad a nasa jawabin yayin wannan zama na sa’o’i biyu, ya roki wasu Limaman unguwanni kan su sanya ido a kan Ladanai da suke lalata Azumin jama’a ta hanyar kiran Sallar ‘assalatu’ na karshe da suke yi a lokaci da alfijir ya gama fita, alhali su wadannan mutane sun dogara ne da kiran Sallar su na karshe kafin su daina cin abinci.
Ya ce wannan lamari mutane suna kallon sa kamar karamin al’amari, amma babba ne a lokacin Azumi, saboda wasu Ladanai ba sa kiyaye lokacin daina cin abinci da kuma lokacin da ya kamata su kira assalatu, wanda zai dakatar da mutane daga cin abinci, saboda suna kira ne daga karshe kuma a lokacin da za a shiga Salla, alhali wasu masallatai har sun idar da Salla, amma wasu a lokacin suke daina cin abinci. Don haka ya bukaci mutane da su gyara wannan kuskure don a samu gyaran ibada.
Mukhtar Ahmad ya kara da jawo hankalin masu hannu da shuni da su rika fitar da Zakka daga dukiyarsu, kuma su raba ta ga jama’ar da suka dace da hanyar da ta dace kamar yadda Allah ya yi umurni. “Saboda akwai mutane da dama da suka dace su bayar da Zakka amma ba sa bayarwa, sun kuma sani wannan hakki ne na Allah da ya dace su sauke nauyinsa daga kansu”, in ji shi.
Ya ce a baya har Marigayi Sarkin Bauci sai da ya kira masu kudin da suka dace su fitar da Zakka fadarsa ya ba su takarda daga Hukumar Shari’a da hannunsa, amma mutum daya ne tak ya dauki wannan umurni yake bayar da Zakkar, shi ma akwai kura-kurai cikin yadda yake raba ta.
Don haka Shugaban hukumar Shari’a, ya shawarci masu hannu da shuni su tausayawa masu karamin karfi, su rika fitar da Zakka suna ba su don su fita daga cikin wasu wahalhalun; hakan zai taimaka su fita daga cikin fushin Allah da kare dukiyarsu daga bala’in rashin fitar da Zakka.
Daga Husaini Baba
Yanzu haka dai gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Mamuda Aliyu Shinkafi, ta ware Naira miliyan 107 don ciyarwa a cikin wannan watan na Ramadan.
Gwamna Shinkafi ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da manema labarai a makon da ya gabata a ofishinsa da ke Gusau.
Kuma ya kara da cewa, “wannan wata mai daraja wanda Allah ke ruwan rahama ga bayinsa, yake nunka ladan ayyukan alheri a cikinsa, ya kamata mu mike tsaye don ganin mun ci moriyar wannan watan mai dimbin falaloli”.
Gwamna Shinkafi ya bayyana cewa kamar yadda aka saba, gwamnati na iyaka kokarinta wajen ganin an taimaka wa al’umma wajen ciyarwa a wannnan wata mai rahama. “Wannan shekarar ma gwamnati ta yi shiri na musamman a kan hakan”.
Kazalika Gwamnan ya yi kira ga Musulmi da su rinka taimakon makwabtansu da na kusa da su, “lalle da kowa a ce zai taimaki makwabtansa da na kusa da shi ya fi ya kai gudummuwa wani wuri don nan ta fi dacewa”, in ji Gwamna Shinkafi.
A karshe Gwamna Shinkafi ya yi kira ga al’umma da su dage da ninninka ibadu a cikin wannan watan da neman gafara ga Allah, su kuma masu hannu da shuni da su taimaka wa mabukata da neman addu’a neman zaman lafiya a jihar Zamfara da ma kasa baki daya.
A wani labarin kuma, Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar Zamfara ta ba marayu kayan Azumi da na Salla 2500, da raunana da mata zawarawa da ke fadin jihar ta Zamfara.
Shugaban Hukumar, Alhaji Sarkin Fawa Malami ya bayyana cewa kamar yadda Hukumar ta saba duk farkon watan Azumi tana ba da tallafi ga marayu da musakai da zawarawa, wannan shekarar ma Hukumar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ba da wannan tallafin.
Sarkin Fawa ya bayyana cewa daga cikin abin da muke amsa na zakka ne da Wakafi muke amfani da su wajen aiwatar da wadannan shirye-shiryen na wannan Hukumar.
Shi ma babban Sakataren Hukumar Malam Sani Atiku Maradun ya yi karin haske a kan ayyukan Hukumar kamar haka: “A wannan lokacin Hukumar ta gina asibitoci 17 a fadin yankunan masarautun jihar ta Zamfara. Sai kuma Islamiyya nizamiyya wanda yanzu haka al’umma ke amfana da su”.
Sakataren Hukumar Zakka da Wakafi, wanda kuma shi ne Sa’in Zamfara, ya bayyana cewa abubuwan da marayu da musakai za su amfana da su sun hada da gero da shinkafa, shaddoji da atamfofi, da kuma kudin dinki Naira 500.
Daga M. Umar Saye
An shawarci ’yan kasuwa kan su ji tsoron Allah su daina sayar da bindigar ‘Nock-out’ da yara suke wasa da ita suna fasawa suna firgita jama’a, musamman a wannan lokaci na watan Ramadana da ya kamata mutane su dage wajen taimakon jama’a kan aikata aikin kwarai da tsoron Allah.
Shugaban shirin Gyara Kayanka, kuma mai ba Gwamnan Jihar Bauci shawara kan harkar ilmi da inganta tarbiyyar al’umma, Dakta Salisu Shehu, shi ne ya yi wannan kira ga ’yan kasuwar kan su sani cewa wannan ba al’adar Musulmin kwarai bane ya rika tsoratar da jama’a a yayin da suke kokarin ibada don neman yardar Allah.
Ya kara da cewa, maimakon mutum ya rika wannan kasuwanci, gara ya koma sayar da lemo da sauran kayan marmari a wannan wata mai alfarma saboda yadda suke ciniki, da haka ne zai kare kansa daga shiga cikin fushin Allah ta hanyar daukar alhakin bayinsa.
Dakta Salisu Shehu ya shawarci iyaye da masu unguwanni da Malamai da Limamai da ’yan kasuwa kan su bayar da hadin kai, su kuma ji tsoron Allah su taimaka don a kawo karshen wannan cutarwa da yaran ke yi wa jama’a, domin wannan abu zalunci ne, kuma haramun ne aikata shi, kuma Hukuma za ta shigo don shawo kan lamarin matukar ba a samu sauyi ba.
Ya roki kafafen watsa labarai su taimaka wajen shawo kan wannan lamari kamar yadda suka saba taimakawa wannan shiri na Gyara Kayanka ko da kudi, ko ba kudi, don a gudu tare a tsira tare. Haka su ma hukumomi ya ja hankalinsu da su taimaka wajen ganin an dakatar da wannan mummunan aikin da yaran ke yi, musamman a cikin wannan wata na Ramadan.
Wajibi ne Musulmi su hada kansu
In ji Shaikh Musal Kasiyuni
Daga Muhammad Isa Ahmad
“Ramadan watan Alkur’ani”. Wani ya ambata haka yayin da ya doso Darul Kadiriyyah da ke yamma da masallacin Juma’a na cikin garin Kano ranar Lahadi 28 ga Sha’aban 1431, inda aka fara karanta littafin Ashafa da Shaikh Musal Kasiyuni Shaikh Nasiru Kabara ya saba a duk wata Ramadan tsakanin Sallar Zuhr da kuma Asr.
Mai gabatarwa ya ambaci wannan shi ne shekara na 20 kenan da Shaikh Nasiru Kabara (RA) ya khalifantar da Shaikh Musal Kasiyuni wajen karantar da littafin Ashafa a duk watan Ramadan, wanda a bara dai aka yi saukar kashin farko na littafin Ashafa.
Kadan daga cikin Malamai da bakin da suka samu halartar bude karatun na wannan shekara sun hada da Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na cikin gari, Shaikh Nazifi, Shaikh Bala Makwarari, Shaikh Malam Baita, Malam Muhammad Turi, Wakilin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na Kano, Shaikh Ibrahim Khalil, Wakilin Sarkin Kano, Barista Abdullahi Ado Bayero, Alhaji Bashir Tofa, Shaikh Malam Umar Dan Sani, Malam Ahidu Mukaddamin Funtuwa, Wakilin Shaikh Harazimi, Mukaddaman garin Gano, Rogo, Ringim, Sumaila dss.
Shaikh Nazifi ya fara bude karatun da addu’a, aka gabatar da karatun Alkur’ani kuma Malam Abubakar Ci-gari ya yi gabatawar gaisuwa da maraba da baki.
Shaikh Musal Kasiyuni Shaikh Nasiru Kabara yayin fara karatun Ashafa na bana ya kasa jawabin nasa zuwa kashi biyu, na farko ta’aziyya, tsokaci da nasiha, sannan a bangare na biyu karatun Ashafa.
Malamin ya mika ta’aziyyarsa a madadin Darul Kadirriyyah bisa rasuwar wasu daga cikin mabiya da suka rasu daga shekarar bara zuwa bana, kamar su Shaikh Mukhtari Atamma, Hajiya, matar Shaikh Nasiru Kabara babar su Shaikh Bazallahi Shaikh Nasiru Kabara dss.
Malamin ya kuma yi tsokaci a kan halin da kasar nan take ciki, yana mai tattabo sassa daban-daban kamar halin rayuwa, siyasar kasar da dirkaniyar da ake fama da ita, yana mai kira ga karatun-ta-natsu a dukkan al’amura.
A batun halin da Masallacin Kudus, alkibilar farko ta Musulmi ke ciki kuwa, Malamin ya yi tsokaci tare da jajantawa a kan halin da masallacin ke ciki a hannun Yahudawa tare da kira ga hadin kan Musulmi da azamar ’yanto masallacin Baitul Mukaddis da yake wajibin dukkan Musulmi.
Malamin ya kara nuna rashin alfanun rarraba tsakanin Musulmi, wanda ba kowa ke amfana da shi ba face Shaidan da makiya Musulunci da Musulmi.
Shaikh Musal Kasiyuni ya yi kuma tsokaci, nasiha tare da kiran Musulmi su nisantar da kansu wajen taimakawa kafirci a kowane hali, yana mai ba da misalai daban-daban. Halin da kasashen Musulmai na Iraki, Afghanistan, Pakistan, Gazza, dss, wanda a kullum suke fuskantar hare-hare da tashin bama-bamai ya ishe mu abin tunani da daukar matakin da ya dace.
Haka nan Malamin ya nuna takaicin yadda a wani lokaci hatta Musulmi sukan taimakawa kafircin duniya wajen kuntata wa Musulmi ’yan uwansu, yana mai ba da misalin hanyoyin taimakawa da kasar Masar ke bai wa Yahudawa wajen azabtar da Musulmin Gazza na Palastinu kamar gindaya shinge da takunkumi.
Shaikh Musal Kasiyuni ya karkare wannan jawabinsa na kashin farko yana mai rokon Allah (T) ya hada zukata da kan Musulmi, tare da yi mana rangwame ga dukkan musiba.
Yayin fara jawabin kashi na biyu wato karatun Ashafa, Malamin ya rairayo salsalar yadda ya karanta littafin Ashafa, tun daga mahaifinsa Shaikh Nasiru Kabara (RA), har zuwa ga Shehu Muhammad Tunusi (Wali Mai Kalgo), wanda ya zo ya karantar da Ashafa a wannan nahiyar lokacin zamanin Sarkin Kano, Muhammad a karnin na 11, wato shekaru 400 da suka wuce kenan.
Malamin ya tunatar da cewa Littafin Ashafa kisimi biyu ne, na farko bayani a kan wanene Shugaba? Wato wanene Manzon Muhammad (S) wanda mafiya yawan masu karatun sa kan ta bahasinsa, da kuma kashi na biyu da ya kunshi hakkoki na Shugaba a wannan Ramadan da aka fara karatun ranar Lahadi an shiga kisimi na biyu ne.
Bayan gabatar da Sallar Asr, an yi addu’o’i aka kuma dakata sai rana ta gaba. Karatun dai ana gabatar da shi ne a kowane rana a Darul Kadiriyya tsakanin Zuhr da Asr.
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |