ALMIZAN ta cika shekaru 20 cikin nasara (1)

Daga Aliyu Muhammad Mahi Dawakin Kudu, Kano 0703 923 7441, 0819 133 2425

GABATARWA

Da sunan Allah Mai afuwa da jinkai, Mai kaddara abin da ya so cikin lokacin da ya yi niyya. Tsira da amincinsa su karu ga babban Jarumi uban jarumai, Masani uban masana, Annabi Muhammad (S) da iyalan gidansa tsarkaka.

Dan uwa mai karatu, ina sanar da kai cewa na yi wannan rubutun ne don in taya al’ummar Musulmin duniya, musamman Hausawa da masu iya karanta rubutun Hausa murnar cika shekaru 20 cif da wannan jarida mai farin jini, mai tasiri ga masoya da makiya, kainuwa dashen Allah, ALMIZAN ta yi. Da fatan Allah (T) ya nuna wa wannan jarida wasu shekaru 20 sau 20 tana juyawa.

MA’ANAR ALMIZAN

ALMIZAN kalma ce ta Larabci, wadda take nufin ma’auni, wato abin da ake amfani da shi wajen gano nauyin wani abu ko darajar wani abu. Amma a yau, a gwagwarmayance a cikin da’awar Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) idan ka ji an ce ALMIZAN, tana nufin jarida don karuwar Musulmi. Wasu mutane ne ’yan kishin addini suka tsaya suke samar da ita duk ranar Juma’a ta inda take auna maganganun da suka shafi al’ummar Musulmin duniya gaba daya, ta fadakar da su, a karshe ta fitar da sakamako mai kyau.

SAMUWAR TA CIKIN SHEKARU 20

A cikin watan Rajab mai albarka 28 ga shi a shekara ta 1411, wanda ya yi daidai da 1990 aka samar da wannan jarida ta “ALMIZAN” ranar Juma’a. A cikin wadannan shekaru 20, daga farko an fara sayar da wannan jarida a kan Naira uku, daga baya ta koma Naira hudu, ta tafi biyar, daga nan har ta kai Naira 10, ta kai 15, 20, 30, 40, 50, wanda daga baya har ta kai Naira 80, wato Murtala hudu.

Dan uwa mai karatu kada ka yi mamakin wannan sauyin farashi da aka dinga samu, domin na san kana sane da halin da kasar nan take ciki game da tashin farashin kayan sana’o’i, musamman wanda suka shafi kamfani.

Kamar yadda aka kira ta jarida don karuwar Musulmi, tabbas haka yake, domin tunda aka samar da wannan jarida, aka samar da wasu filaye na fadakarwa da suka shafi Musulunci, da Musulmi, kuma aka samar da wasu don sanar da al’ummar Musulmi halin da ’yan uwansu na duniya ke ciki.

Sannan duk duniya a cikin jaridun Hausa, ALMIZAN ce kawai take da tsari don fadakar da Musulmi a kan riko da yanayi mai kyau irin na Musulunci. Misali, za ka ga suna rubuta; GASKIYA DA RIKON AMANA ADO NE GA MA’ABOCIN ADDINI. HIZIFI NAWA A ALKUR’ANI KAKE KARANTAWA A KULLUM? KADA KA BARI SALLOLIN DARE SU DINGA WUCE KA, da dai sauran maganganu masu amfani ga rayuwarmu ta duniya da lahira.

Kamar yadda yake a tsare, an samar da jaridar ALMIZAN ne domin yada addinin Musulunci da kuma fadakar da mutane game da da’awar da Sharafuddeen Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ke yi, wannan ya sa ALMIZAN ta fuskanci barazanar karyawa da dannewa daga gwamnatocin jihohi da na kasa gaba daya, amma da yake ta zama kainuwa dashen Allah, ga ta nan daram dakau, fes, tas, sumul, babu abin da ya same ta sai gaba take cikin yardar Allah Ta’ala.

Ba zan manta ba daga cikin jaridun da aka samar da su don su yi fada da da’awar Sayyid (H) akwai irin su ATTAJDEED ta ’yan J.T.I, wadda ta yi dogon suman da in sun yi sa’a su fito sau biyu a shekara, wato ranar karamar Salla da babbar Salla. Sannan akwai irin su ASSUNNAH, ita kuma don ta zama kishiya ga ALMIZAN ga kayan aiki ga kudi, wai an samar da ita ne don ta karantar da Sunnah tunda ALMIZAN Shi’a take karantarwa, amma kafin tafiya ta yi nisa sai ga Assunnah ta rabu gida biyu, saboda rigingimun cikin gida da suka yi musu yawa. Wannan ya sa suka koma “Assunnah shudiya” ragowar kuma suka koma “Assunnah koriya”. Ba a dade ba suka yi mutuwar kasko, kowa ya kama gabansa, amma har yau ga ALMIZAN nan fes, tas, sai gaba take.

A lokacin da ALMIZAN ta fara fita, ta tarar da wasu jaridu na Hausa amma yau babu su, amma ita ga ta nan har yau ta yi nisan kwana. Daga cikin wadannan jaridu akwai irin su NASIHA, ALBISHIR da AMANA a garin Zariya ga ’YANCIN DAN ADAM a Jos, ga irin su RANA a Kaduna ga su ZUMA da dai sauran jaridun Hausa da na Turanci wadanda suka zama tarihi, amma ALMIZAN kuwa ga ta nan kullum sai gaba take.

A cikin wadannan shekarun ALMIZAN ta sami ci gaba da fasahohi wadda babu wata jaridar Hausa da ta sami irin su, kamar samun kwararrun ma’aikata masana aiki masu kishi, ba kishin Naira ba, ga kuma shiga sakar sama don zaga duniya su isar da sakon Musulunci.

AYYUKANTA DON KARE HARKA ISLAMIYYA

Jaridar ALMIZAN cikin wadannan shekaru ta zama kakakin isar da sakon gwagwarmayar Musulunci ta hanyoyi da dama, wanda dama shi ne dalilin kafa ta. Ka ga dai a Harka Islamiyya ba mu da wani muhimmin sako da ya wuce jawaban Sayyid (H). To, tsawon wadannan shekarun wannan jarida ba makon da zai zo ba ta fito da jawabin Sayyid (H), ko da kuwa yana tsare ne, domin jawabansa ba sa karewa.

Sannan a wadannan shekaru da ALMIZAN ta samu ma’aikatanta gaba daya tun daga M.D zuwa Edita da mai aiko da rahotanni sun tsaya sosai wajen haskawa duniya hakikannin yadda wannan da’awa take da manufofinta ga al’umma. Sannan Edita da ma’aikatansa sun tsaya sosai wajen mai da martini na ilimi, na hankali, na hikima da fasaha ga duk wani fajiri ko azzalumi da ya yi gigin daura fada da wannan da’awa mai albarka. Da wannan muke addu’a ga M.D Alhaji Danlami da sauran ma’aikata, Allah ya kara lafiya.

AYYUKA DA KOKARIN MA’AIKATANTA

Babu wata jarida a kasar nan kakaf da take da ma’aikata masu kokari wajen aiki ba don Naira ba irin jaridar ALMIZAN. Na sami tabbas a kan haka ne a lokacin da Janar Sani Abacha ya zo kama Sayyid (H), wanda bayan kamun suka je suka tafi da dukkan kwafin wannan jarida da ake shirin rabawa ranar Alhamis. Amma abin da zai ba ka mamaki shi ne yadda wadannan ma’aikata a wannan rana, gari bai waye ba, wato ba su yi barci ba, sai da suka buga wadda za a raba a fadin kasar nan kakaf kuma dauke da labarin kama Malam da aka yi. Kuma bisa taimakon Allah ta isa wurare masu yawa, musamman a nan Arewa a wannan rana ta Juma’a. Akwai sauran kokari da ayyuka masu amfani wadanda babu lokacin kawo su da wadannan ma’aikata suke yi. Muna fatan Allah ya kara musu karfin gwiwa.

SHAWARA GA DILLALAI

A matsayina na dillalin ALMIZAN, ka sani aikinka yana da matukar muhimmanci a wannan jarida, domin ta hannunka ake isar da ita ga dukkan al’umma. Da wannan nake ba ka shawara da ka yi kokari ka siffantu da sifofi na addini, kamar gaskiya da kiyaye amanar kudin wannan kamfani. Juriya da hakuri wajen karbo jarida da sai da ita. Shawara ta gaba ita ce ka sani wannan aiki naka aiki ne na sadaukarwa wajen taimaka wa Harka Islamiyya don tabbatar da addinin Allah a wannan kasa. Bisa wannan dalili nake fatan za ka ci gaba da hakuri da abin da kamfani yake ba ka na ladan talla, ba biyanka ake ba, sai don ka yi maganin kananan matsaloli na rayuwa.

SHAWARA GA MASU KARATU DA RUBUTU

Shawarata ga masu karatu da rubutu maza da mata ita ce, ku sani wannan jarida kodayaushe kofarta a bude take. Ma’ana kuna da dama ta yin rubutu a kan wani abu mai amfani ga al’umma. Ka da ku yi zaton cewa ku ba ’yan kaza bane, ko ba za a karba ba, a’a, ba haka bane, kada ku manta taken wannan jarida shi ne “JARIDA DON KARUWAR MUSULMI”. Wato in dai mutum Musulmi ne ya yarda da Allah da Annabinsa (S) wannan jarida ta shafe shi. Da wannan dalili nake shawartar duk wani mai karanta wannan jarida ko rubuce-rubucen Hausa ga dama ta samu, idan kana da wani abu na fadakarwa ga Musulmi ko matsalar wani fajirin azzalumin Shugaba kake tunani, inda za ka kai a buga a sanar da al’umma halin da ake ciki game da zaluncin wannan azzalumi, to na tabbata wannan jarida a shirye take ta buga don sanar da al’umma komai.

SHAWARA GA MASU KARATU DA RUBUTU ’YAN HARKA ISLAMIYYA

Shawarata a gare ku ita ce ya kamata ku fadada rubuce-rubucenku a kan wasu abubuwa da suka shafi addini musamman wadanda wasu makiyanmu suke yadawa mutanen su a kan sharri, ku dinga aikawa wannan jarida na tabbata za su buga don wayar da kan mutane yadda gaskiya take babu son rai a ciki domin tsawon shekarun nan aikinsu kenan.

SHAWARA GA MAWAKAN HARKA ISLAMIYYA

Gaskiyar lamari tsawon shekarun nan 20, ana dadewa sosai kafin ka ji ko ka ga wani abu daga mawakan Harka Islamiyya a cikin wannan jaridar. Ko me ya sa? Ban sani ba. Amma ya kamata ku motsa ku samar da muhimman kasidu masu gamsarwa a wannan jarida, musamman a lokacin Maulidin Annabi (S) da na Imam Ali (AS) da sauran A’immatul Huda (AS) da kuma sauran munasabobi wadanda ake gabatarwa kamar Ashura da Shuhada. Na tabbata in dai kun aika wa wannan jarida ba za su ki bugawa ba, domin har fili suka ware wa Ittihadis Shu’ara mai suna Dandalin Mawaka.

Za mu ci gaba insha Allah.


Shafin Farko