|
|
Juma'a 10 Ramadan, 1431 Bugu na 939 ISSN 1595-4474 |
|
Malam Ibraheem Yaqoub
Zakzaky (H) |
Mai karatu dai har yanzu muna nan a wannan fili naku mai farin jini da ilimantarwa na tambaya da amsa daga bakin Malam Ibraheem Zakzaky (H) kai tsaye. Kuma muna maraba da tambayoyi masu ma’ana zuwa ga Malam don a kori jahilci a wasu abubuwan da suka shige maku duhu. Sai dai kamar kullum muna kira da a rinka aiko mana da tambayoyi masu ma’ana. Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto muku wannan shafi. Allah ya kara fahimtar da mu, amin.
TAMBAYA: Akramakallahu, musulmi mai sana’ar hannu kamar gini, gyaran wuta, kafinta da sauransu, ko zai iya halatta a gare shi ya yi aiki a coci in an kira shi?
SHAIKH ZAKZAKY: Eh, ba laifi. Sai dai idan zai kawo zilla ga shi musulmi din. In ya ga cewa zai kawo masa kaskanci, to bai halatta gare shi ya dauki wulakanci ba. Amma idan ya zama akwai izza tare da shi, akwai girma, su suna ganin shi gwanin aikin wuta ne, in ba shi ya hada ba ma abu ba zai yi kyau ba, har ma sun zo sun lallashe shi ne, kuma ya gindaya masu wasu sharudda ma, duk suka yarda, to ka ga ya kiyaye mutuncinsa. Babu damuwa, yana iya yi.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne ya tashi a salla domin ya biya bashin da aka tsere masa daga Liman. Shin wani zai iya bin sa, wato shi ya zama Liman kenan?
SHAIKH ZAKZAKY: A’a, lallai masabuki ba ya zama Liman. Ko ka ga wani yana salla sai ka bi shi kana tsammanin sallarsa yake yi, sai ka gano ashe ya bi Liman ne, to binka da shi ya rushe.
TAMBAYA: Akramakallah, an ce sallar Juma’a ba ta wajaba a mazhabar Jafariyya. Ina neman karin haske. Kuma in haka ne, to zan iya yin azahar dina kafin masu sallar Juma’a su yi tasu?
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ba a ce Juma’a ba ta wajaba a Mazhabar Jafariyya ba, lallai Juma’a wajiba ce a Jafariyya. Abin da aka ce sharadin wajibcinta ne sai tare da Imam (AS). In ba tare da Imam (AS) ba, to ko an yi ta dole kuma sai an yi Azuhur. Shi ne aka ce, amma ba an ce wai bat a zama wajiba bane.
Sannan kuma idan ka yi sallar Juma’a ba tare da Imam (AS) ba, to za ka yi sallar Azuhur. Saboda haka idan mu kaddara kai matafiyi ne, wanda ko Juma’ar ma ba ta a kanka, kana matafiyi ne, to in lokacin salla ya yi ka samu ka yi Azuhur dinka. Lallai ba a ce Juma’a ba ta wajaba ba, tana da sharadin wajibci. Saboda haka idan tafiya ko wani uzuri da ta sarayar da wajibcin Juma’a a kansa ta same shi, to ba lalai sai ya jira masu Juma’a sun yi ba kafin ya yi Azuhur dinsa. Amma dai ya fahimci maganar farko, cewa lallai ba haka bane cewa wai ba wajiba bace a Imamiyya, wajiba ce amma da sharadi. In ba ta cika sharadinta bane ba za ta wajaba ba.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne yana doguwar tafiya sai ya ya da zango a wani gari ya kwana. Shin ya da zangon da ya yi ma kasaru zai yi? Daga Iliya Bashir Mile 12 Legos
SHAIKH ZAKZAKY: Eh mana in yana cikin tafiya din ne. Matukar mutum yana tafiya, har ma in da ya je, matukar yana cikin tafiya din ne. Akwai ka’ida na zama wanda yake iya maishe shi ya zama ya daina kasaru. Kamar inda ya ya da zangon nan sai ya yi niyyar zai kwana goma, to a lolkacin ne sai kasaru ta kau. Amma matukar a zangon nnan nasa bai niyyar zai kwana goma ba, zai ci gaba da kasaru ne.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne ya yi tafiya sai salla ta riske shi a hanya, amma bai samu ya tsaya ya yi ba, kuma lokacin da ya isa gida mukhtarin sallar bai wuce ba, shin zai yi ta a kasaru ne ko kuwa zai cika?
SHAIKH ZAKZAKY: Zai yi duk biyu ne. Zai yi kasaru kuma ya cika. Saboda tunda ta same shi a tafiya bai yi ba, to wajibinsa ne ya yi ta a kasaru din. Sannan kuma tunda ya zo gida lokacinta na nan, to sai ya yi duk biyu. Amma wannan ana cewa yin kasaru a nan ‘ihtiyadi’ ne tunda yana gida. Kamar yadda in salla ta same shi a gida, sai ya tashi ya yi tafiya, ta riske shi a hanya, shi ma ana cewa zai yi duk biyu ne. Zai yi cikakkiya, ya kuma yi kasaru. Amma a nan yinsa shi ma zai zama ‘ihtiyadi’ ne. Amma shi na fita ya fi karfi, ‘ihtiyadin’ ya fi karfi, cewa duk biyu zai yi, fiye da mai dawowa. Wato ‘ihtiyadin mai fita a lokacin salla bai yi ba, ya fita ya je ya yi kasaru, to shi lazim ne ya yi cikakkiya “ihtiyadan’ ya yi kasaru. Amma ‘ihtiyadan’ ya fi karfi. Wanda ya dawo shi ma bai yi salla a tafiya ba, ya dawo gida, shi ma zai yi kasaru kuma ya cika. Amma shi ‘ihtiyadan’ da dan sauki a kan wancan.
TAMBAYA: Allah gafarta Malam, idan na yi raka’ar farko na yi ‘jalsatul istiraha,’ shin zan yi kabbara in zan mike?
SHAIKH ZAKZAKY: Idan mutum ya yi raka’a ta farko, ya yi zaman da ake ce masa zaman istiraha, to in zai mike zai ce ‘bi haulillahi wa kuwwatihi akumu wa ak’ud.’ Haka zalika ma in ya zauna ya yi tashahhud bayan raka’a biyu. In zai mike shi ma zai iya cewa ‘bi haulillahi wa kuwwatihi a kumu wa ak’ud’ tunda ba muhallin takbir bane.
| Ana shiryawa da bugawa a I. M. Publications, P. O. Box 686,Babban Dodo, Zariya, Kaduna Nijeriya. Edita Ibrahim Musa Tar: 069-335148. I-mel almizan80@hotmail.com ko almizanzariya@yahoo.com GSM: 08037023343 |