Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Zanga-zangar cire tallafin mai

Na Malam Muhammad Suleiman 08029493717

Daga Shehu Janbulo

Tabbatar da karin kudaden albarkatun man fetur da cire tallafin gwamnati, wani rashin imani ne gami da kokarin aiwatar da muradun Amurka da sauran kasashen Turai.

Babu wata kasa mai hankali da za ta aiwatar da irin wannan danyen hukunci, musamman a irin wannan mummuna kuma mawuyacin hali na lalacewar tattalin arziki, rashin ayyukan yi da tsadar rayuwa, gami da tabarbarewar dukkan fannonin ayyuka kama daga tsaro, ilimi, lafiya har yanayin dabi'u da zamantakewar al'umma.

Kamar yadda mutane da dama suka sani, masu mulkin kasar nan ba ko shakka ba su da tsari balle sanin ya kamata, domin idan ba a ragewa talaka tsanani ba, bai kuma dace a kara masa ba. Hakika ba su da tausayi sam, ko da kuwa irin na ’yan’adamtaka ne. Haka ba su da kunya ko shakkar al'ummar da suke jagoranta, ba kuma sa jin kunyar yaudara da shirga wa jama'a karya.

Kodayake ba zabar su ake yi ba, suna nadi da kwace ne da karfi, balle su ji tsoron kada idan an zo zabe na gaba a ki zabar su. Amma duk da haka, ya kamata a matsayinsu na bangaren ita kanta al'ummar, a ce suna da kishi ko tunanin jama'ar da suka fito ciki, wadanda suka hada da iyaye, ’yan uwa, abokanai da masu yi musu aikace-aikace.

A yanzu dai, babu wata madafa ko sauran dabara dangane da samun sauki a kasar nan, wacce ta wuce ta fito-na-fito da azzalumai, tunda an shaida yadda makomar masu fafutuka da kuri'a ta kare.

A bisa alamu da yanayin da ake ciki, akwai yiwuwar faruwar wasu abubuwa biyu: Na farko, fantsama cikin wani mummuna kuma mawuyacin halin tsadar rayuwa, da babu wanda ya san adadin illar da zai haifar. Na biyu, yiwuwar barkewar rikici, wanda watakila ta sanadin zanga-zangar da ake kira ko kokarin shiryawa.

Sai dai a zahirance, akwai hadari kwarai shiga duk wani fito-na-fito ko rikici da zai kai mutum ga halaka ko samun lahani a bisa duk wani dalili ko hujja da ba ta Allah ba.

Ina so a fahimta cewa, kwatar ’yanci wajibi ne, amma ga Musulmi babu illa da sharri gami da rashin ’yancin da ya fi rayuwa karkashin wani tsari da ba na Allah ba, kuma babu hujjar kan gado da mutum zai bari ya wahala balle lahanta ko rasa rai, idan ba a gwagwarmayar tabbatar da gwamnatin Musulunci ba. Illa iyaka.

Tsarin Allah, wato gwamnatin Musulunci ita ce magani kuma hanyar kau da duk wasu matsalolin rayuwa tare da kulen da ke gaban dan Adam tun daga tushe. Amma duk wata fafutuka sabanin ta Musulunci nadama ce, domin haka ba zai cimma ruwa ba. Tamkar an gudu ba a tsira ba ne ko an kashe maciji ba a cire kansa ba.

An gudanar da zanga-zanga a Kano dai a ranar Litinin din makon jiya kamar yadda kungiyar kwadago ta kira. Sai dai an samu tashin hankali tsakanin wasu masu zanga-zangar da suka harzuka da ’yan sanda, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wadansu masu zanga-zangar tare da jikkata wasu.

Jama'a da dama sun fito fiye da yadda aka tsammata a baya. A ra'ayin wani mai suna Garba Ibrahim ya min cewa haka ta faru ne saboda mawuyacin halin da jama'a suke ciki na tsadar rayuwa.

Wani Dakta, wanda ya bukaci a saya sunansa ya ce, zanga-zangar ta samu karbuwa ne saboda jama'a sun gaji da halin ko-in-kula da gwamnati ke yi wa al’umma. Ya kara da cewa, jama’a tuni suka daina yarda da gwamnati sam saboda karya da yaudarar da suke yi kullum.

A wuraren da dama da na ziyarta babu kowa a cikin gari a rana ta farko wato Litinin, amma a rana ta biyu wato Talata an samu zirga-zirga kadan a kan ababen hawa. Na fahimci cewa mutane na cike da gwamnati a kan wannan karin kudin mai din. Har na ga wasu matasa biyu da suka tube riga suna nuna wa ’yan sanda cikinsu cewa idan za su harba su harba din. Haka zalika, mun ga yadda masu zanga-zangar suke bin bayan jami'an kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU, maimakon bin bayan ’yan kungiyar kwadago NLC. A karshe dai na fahimci cewa jama'a sun rasa jagoranci a lokacin zanga-zangar.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan