Shafin farko           

Hantsi                     

Tataunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Nasiha ga iyaye game da tarbiyyar yara

Na Malam Muhammad Suleiman 08029493717

Daga Shehu Janbulo

Hannunka mai sanda ya lura cewa wasu iyaye na halin ko oho da dora wa yara nauyin da ya fi karfinsu, wanda hakan kan sa yaran rayuwa a wahalce. Yara, kiwo ne da Allah Ta'ala ya damka wa iyaye, kuma zai tambaye su a kan yadda suka tafiyar da kiwon, kamar yadda su din ma za a tambayi nasu iyayen a kan yadda suka lura da su lokacin suna kanana.

Babu abu mai ciwo da bakanta rai ga masu hankali fiye da ganin yara a cikin wani hali marar kyau. Ko da ta wacce fuska, abin da ya shafi yara ya fi jan hankali, domin su mutane ne masu rauni da ba sa iya yi wa kansu komai. Shi ya sa kulawa da su ya zama wajibi.

Hakan ne ya sa addinin Musulunci ya zama babban gata da kare wa kowa hakki da 'yanci, musamman ma yara. Duniya ta ga yadda Manzon Rahama (S) ya nuna kulawa da daukar nauyi gami da abokantakar yara kanana tare da tausaya masu a duk inda ya same su. Hakika, rayuwar Manzo (S) abar koyi ce ga iyaye da mutane masu hankali a kan fahimtar muhinmancin lura da yara.

Ko zaluncin da Isra'ila take yi wa Palasdinawa da sauran mutane, babu abu mai bakanta rai da takaici fiye da gallazawa da kashe-kashen yara kanana. Ba shakka, yara sune manyan gobe. Idan har ba su samu kulawar da ta dace ba, a goben ba za a samu manya nagari masu ingantacciyar lafiya da karko ba.

Akwai wadansu halaye da wasu iyayen ba sa ganin su a bakin komai, amma kuma suna da tasiri ga rayuwar yara a gaba. Misali, yawan barin yaro ba wando, babu abin da hakan zai koyar fiye da cire kunya da rashin girmama al'aura. Irin su ne ko da sun girma ke kware wando a titi suna fitsari. Haka zalika, barin yaro hanci da majina dagaja-dagaja, ko ba wanka kaya dakal-dakal. Idan ba a yi sa’a ba, rayuwar irin su ce ke kasancewa ba tsari ga kuma kazanta.

Ita ko yunwa ga yara, ba karamar illa ba ce, domin ba za su taba zama lafiyayyu ba, balle har kwakwalensu su ginu ta iya fahimtar karatu ko wadansu abubuwa da ya kamata su rinka sani. Duk da akwai matsaloli a kasar nan, amma ya kamata a rinka kokarin taimakawa yara da abinci isasshe. Bai dace halayyar wasu iyaye ba masu fita waje su ci su koshi dam, amma yara a gida suna ci ba koshi koma ba su samu ba sam. Ko kuma iyaye mata masu kasala da ba sa yin abinci a kan lokaci har sai an wahala, yunwa ta ci ta cinye tukunna.

Wasu kuma akwai yawan aike. A maimakon a aiki yaro ya sayo abubuwan da ake bukata zuwa daya, amma sai a yi ta tura shi, duk ko da cewa zai iya zuwa aike lokaci daya. Haka zai ta sintiri a titi, duk ko da rashin kyawun hanyoyinmu ta fuskar gangancin ababen hawa. Wadansu ma har da dare ba sa barin yaran su huta.

Ko masu aza wa yara kayan nauyin da ya fi karfinsu, kamar wurin debo ruwa, ko wasu ayyuka da yara suke yi wa iyayen nasu. Ba laifi ba ne yaro ya yi wa mahaifansa aiki ko aike, amma adalci ne a rinka yin la'akari da raunin da suke da shi.

Ko ga masu yin talla, ya kamata iyaye su rinka rangwanta masu. Akwai rashin adalci zahiran, tura yara talla da safe, talla da rana, wasu ma har da dare. Zai fi zama adalci, komai za a yi a yi da rana, idan dare ya yi kuma a huta.

Wasu kuma iyayen a kokarin bai wa ’ya’yansu ilimi suke wahalar da yaran fiye da kima, kamar akwai wacce ta taba fada min cewa, lokacin suna kanana suna zuwa makarantar Allo da zarar sun yi Salla da Asuba. Karfe 7:00 kuma su dawo su shirya zuwa makarantar boko. Suna tashi daga boko karfe 1:30 da zarar karfe 2:00 ta yi su kara komawa makarantar Allo. Karfe 4:00 saura su tashi, su kuma wuce makarantar Islamiyya zuwa karfe 6:00 na yamma. Haka, bayan Sallar Isha za su kara komawa makarantar Allo zuwa 10:00 na dare.

Ba shakka, karatu yana daga hakkin da ya zama wajibi a bai wa yara, amma ba tare da wuce kima ba. Yawan takurawa ko tsanani ba ya samar da abu mai inganci. Wadansu kuma da na gani, idan sun tashi daga makaranta za su zauna su ci gaba da yin 'extra lesson' har zuwa yamma, da zarar kuma sun koma gida da daddare su tafi makarantar Islamiyya zuwa 10:00 na dare.

Abin fata dai shi ne, a rinka tausaya wa yara a koyaushe a ko'ina. Iyaye su rinka la'akari da raunin yaran, kuma su rinka tunawa idan su ne, yaya za su ji? A cikin yaran ma, marasa baki wadanda ba su iya magana sun fi zama abin tausayi.

Kada a rinka yawaita sa masu nafkin (diaper) ba dare ba rana. Ya kamata a rinka bari suna hutawa, ko dura masu abinci da karfi ko tilasta masu ci da yawa ko da sun koshi, wasu har ma sai sun yi amai tukun za a kyale su. Ko yawan ba su magani, da an ji jikin yaro ya yi dan dumi saboda watakila ko canjin yanayi ko kayan da aka sa masa. Ko barin yaran su yi ta kuka ba tare da an duba a ga dalilin kukan ba, ko yawan yi wa jarirai mata kitso. Ba kwalliya ba ne haka, domin yana cutar da su, tunda jijiyoyin kansu na da laushi matuka.

Yawan jibga wa yara kaya alhalin ana zafi bai dace ba, ko kuma saka masu kaya marasa nauyi a lokacin sanyi. Fakam da yawa, idan kaya suka yi wa yaro yawa ban da kuka babu abin da zai rinka yi. Komai za a yi wa yara a rinka yi daidai wadaida. Shi yaro ba ya son tsanani, domin kwakwalwarsa da jikinsa ba daidai suke da na manya ba. Muddin aka fahimci haka, insha Allah za a rinka la'akari da irin aiki ko nauyin da za a rinka dora masu. Ba tsanani ba, ba kuma wofintarwa ba.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan