Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Siyasa  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

Wasu Shafuka           



Tattaunawa

Zalunci da ta’addancin da aka yi a Karbala (2)

Daga Haruna Shelleng

Ci gaba daga bugu na 1012

Aka tattara su aka sa masu mari (chain), aka sa su a gaba a matsayin ribatattun yaki ko Hijabi babu a jikinsu. Ga kuma kan Imam Husaini (AS) da Iyalan Gidansa da sauran Sahabbansa a tsire a jikin mashi an daga, ana kora su ana kuma shela a gari cewa an gama da makiyan Sarki. A haka aka zo da su garin Kufa a kasa, aka je da su fadar Ibn Ziyad, daga nan aka nufi Sham da su bisa abubuwan hawa wadanda babu siradda. Duk garin da aka bi sai an yi shela jama’a su fito su ga wadanda suka yi wa Sarki tawaye, sai jam’a su fito suna kallo suna al’ajabi. Ita kuma Sayyidah Zainab na yin bayanin ko su su waye.

A hanya wani Banasare mai bauta, da sojojin Yazidu suka yada zango a kusa da rumfarsa, sai ya ga yadda kan Imam Husaini (AS) yake haske kamar rana. Ya roke su ya ba su wasu kudade su ba shi kan ya kwana tare da shi. Hakan ko suka yi, ya ba su kudin suka ba shi kan Imam Husaini (AS) ya kwana a wurinsa, da safe suka zo suka amshi kan suka ci gaba da tafiya zuwa Sham. Banasaren ya ce, ya tabbata wannan kan na Waliyyin Allah ne. Ka kwatanta aikin wannan Kirista mai bauta da aikin wadannan da ke kiran kan su Musulmi. Ibn Ziyad ya ce, idan ya ga dama zai halaka dukkan mutanen Hijaz a kan su bi Yazid dan Mu’awiyyah.

Shi ma Yazidu ya fito wajen gari domin ya tarbi kan Imam Husaini (AS) da na saura, da kuma fursononin yaki, wato Iyalan Imam Husaini (AS). Da ya hango su sai ya yi baitocin Ibn Zuba’ara. Yazidu ya ce: “Da ya hango ‘shumusu’ (jam’in rana), wato kawukansu suke haske kamar rana, sai hankaka ya yi kuka (kuma dama suna shu’umce da kukan hankaka), ko ka yi kuka ko ba ka yi ba, ni na biya bashin da nake bin Muhammadu.”

A wani wuri cewa ya yi, ya dau fansar Badar ne, ya biya bashin da yake bin Annabi (S). An yi daidai. Ina ma da iyayensa suna da rai su gani abin da suka kasa ga shi shi ya yi, duk wannan in ji Yazidu da aka kawo kan Imam Husaini (AS).

Shi Yazidu a wurinsa abin da ya yi wa Imam Husaini (AS) a Karbala daukar fansa ne ya yi a kan Manzon Allah (S), ramuwar gayya ce. Manzon Allah (S) dai ya zo da Musulunci ne, sannan kuma a Badar mushirikai aka rafke da Abu Sufyan, wanda shi ne Shugaban fatakai da suka fito daga Yamen, wanda Manzon Allah (S) ya rutsa da su, sai kuma Utba Ibn Rabi’a, wanda kuma shi ne Shugaban rundunar Badar. Dukkaninsu kakannin Yazidu ne ta wurin uwa da uba. Da Irr da Nafir duk sune, a Badar an kashe Utba baban Hindu (uwar Yazid), sai Shaibah (kawunsa), sai dan Utba, duk an rafke su a ranar Badar, duk kuma Imam Ali (AS) ne ya rafke su. Su Yazidu dai sun koma gabarsu ne ta jahiliyyar Larabawa.

Da aka zo da su fadan Yazidu aka dora kan Imam Husaini (AS) a tire, aka mika masa ya dauki sanda yana zungurin wishiryar Imam Husaini (AS) yana izgili, sai wani Sahabi da ke gurin ya la’anci Yazidu ya ce na ga Manzon Allah (S) yana sumbantar bakin Husaini (AS). Wani Jakadan Rum a fadar Yazidu kuma Kirista ya ce: “Wannan dan ’Yar Manzonku ne kuka yi wa haka? Ni kuwa mutane na girmama ni don ina da dangantaka ta nesa da Annabi Isa, kuma cocin kofato (kanisa) da kuke ji, akwai kofaton jakin Annabinmu ne, yadda muke girmama kofaton jakin Annabi Isa, amma kuma ku kuka yi wa dan ’yar Annabinku haka?.” Nan take ya amshi Musulunci, Yazidu ya sa aka kashe shi da wannan Sahabin.

Imam Ali Ibn Husaini (AS) ya yi jawabi a fadar Yazidu mai ratsa jiki, wanda ya sa masu sauraren sa suka dinga sakin tambulan (glass cup) na giya. To, saboda tasirin jawabin Imam Ali Ibn Husaini (AS) nan da nan Yazidu ya yi umurni a kira Salla domin ya daina jawabi, ya ji tsoron kada a yi masa tawaye. Da mai kiran Salla ya ce: ‘Ashhadu Alla Ilaha Illallah’, sai Imam Ali Ibn Husaini (AS) ya ce: “Hakika na shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma duk gabobina su ma sun shaida da Haka.” ‘Ashhadu Anna Muhammadar Rasulullah’. Sai Imam Ali Ibn Husaini (AS) ya ce wa Yazid: “Manzon Allah din nan Kakanka ne ko Kakana ne? Idan ka ce Kakanka ne ka kafirta, idan ka ce Kakana ne, to me ya sa ka kashe Babana?”

Haka ma wani cikin mutanen da ke fadar Yazidu ya ce wai a ba shi Sukaina ’Yar Imam Husaini (AS) ya yi sadaka da ita. Sai Sayyidah Zainab ta ce; “Ko mai gidanka Yazidu ba ta halasta masa ba balle kai”. “Har ni?” In ji Yazidu. Ta ce; “Kwarai, sai dai ka fita addinin Kakana”, in ji Zainab (AS). Da ya taso, amma da ya ji abin da Sayyidah Zainab ta ce, sai kuma ya yi turus. Yazidu ya aje su a wani kangon gini ne ko rufi babu a Sham, a nan ’Yar Imam Husaini (AS) Sakina ta rasu saboda bakin ciki, aka kuma bizne ta a nan cikin kangon ginin. Yau duba inda kabarin Sukaina ya zama babban Hubbare, wanda dubun-dubatar Musulmi suke ziyarta dare da rana. Shi kuma Yazidu ina fadarsa take a yau? Shi kansa, ina yake? Ina kabarinsa? Ba ma Sakina ba har Muhsin shi ma dan Imam Husaini (AS), wanda barinsa Mamansa ta yi da tafiya ta yi mata tsanani, har shi an yi katafaren Hubbare a inda aka bizne shi a Ba’alabak a kasar Labanon, shi ma ana ziyarar sa. Ka ga har abin da aka yi barin sa ba a manta da shi ba, tarihi ya kiyaye shi. Su kuma wadancan fa? Suna ina? Ina aka bizne su? Ayar da ke cewa: “Fasadi ya bayyana a tudu (kasa) da ruwa saboda abin da hannuwan mutane suka aikata”, ai tana magana ne a kan kashe Imam Husaini (AS). Kuma fasadin farko da aka yi a bayan kasa shi ne na kashe dan Annabi Adam (AS) da dan uwansa ya yi, sai kuma na Imam Husaini (AS) wanda a tarihin bil’adam ba taba yin haka ba, kuma nan gaba ba za taba yin irin haka ba. Wane fasadi ya kai kashe Dan Annabi (SAWA)?

Akwai wani Malami mai suna Shahid Mutahhari, wanda ya zayyana abubuwa guda daya bayan daya har 25 da aka aikata a filin Karbala ga Imam Husaini (AS) da Iyalansa da Sahabbansa, wanda ko a jahiliyyar Larabawa ba a aikatawa, amma an yi wa Imam Husaini (AS). Kuma wai wadanda suka yi aikin wai Musulmi ne? Abin tambaya a nan shi ne, yaya aka yi Musulmi ya yi abin da ba a yi a jahiliyya ba? Anya kuwa Musulmi ne, ko dai…? Wani Banasare ya fada a fadar Yazidu cewa, ya tabbata cewa; “Ku a kan bata kuke tunda kuka kashe Dan ’Yar Annabinku”. Banasare ma ya gane cewa sun yi nisa da barin addini.

Bari na yi magana a kan Gwarzuwar Karbala, wato Sayyidah Zainab Kubra ’Yar Imam Aliy (AS), ’Yar Fatimah (AS), Kanwar Imam Husaini (AS). Hakika ta ba da muhimmiyar gudummuwa a juyin juya-hali (revolution) na Imam Husaini (AS), tun daga Karbala har abin da ya biyo baya. Kuma idan akwai abin da ya fi jinjina, to shi za a yi wa Sayyidah Zainab (AS), domin abin da ya faru a Karbala da bayan Karbala, ko labari aka bai wa mutum ya isa ya sa shi ya mutu saboda bakin ciki da takaici, saboda abin da aka yi a Karbala a rubuce a tarihin dan Adama ba a taba yi wa Iyalan Gidan wani mutum ba ko wani gida abin da aka yi wa Imam Husaini (AS) da Iyalansa da Sahabbansa a Karbala ba. Kuma a gaban Sayyidah Zainab (AS), a ma kan idonta bayan Shahadar Imam Husaini (AS) ma, duk da mata da yara duk sun koma gare ta ne, duk da akwai Imam Ali Bin Husaini (AS), amma yana fama da rashin lafiya. Saboda haka, Sayyidah Zainab (AS) din ce dai ke nan.

Kuma dai ‘she handled the situation perfectly more than anybody could think or immagine’, kuma asirin wannan shi ne asalinta, wato gidan da ta fito, shi ne gidan Imam Ali da Fatima (AS) ’yar Manzon Allah (S) sune mahaifanta ta gaje gidansu, domin manyan mata a tarihi kamar su Maryam Mahaifiyar Annabi Isa da aka yi masu jarabawa yaya suka yi? Maryam da ta haifi Annabi Isa ba Uba da aka yi ca a kanta me ta ce; “Ta yi burin ta mutu kafin ran nan, an manta da ita mantawa”. Ka ji kuma ita Sayyada Zainab cewa ta yi a duk abin da ya faru a Karbala ba ta ga wani abu ba face hukuncin Allah, kuma ta yarda da hukuncin Allah. Ya Allah! ‘This is Sayyada Zainab for you!’ Don Allah ka kwatanta maganar nan guda biyu, sai ka yi wa kanka hukunci. Akwai Iyalan da suka kai Iyalan Gidan Annabi?

Da aka je da su Kufa daga Karbala, mutane da dama suna murna da abin da ya faru a Karbala. Da Sayyidah Zainab (AS) ta same su ta dira kansu da jawabi, ta yi masu tas. Sai da suka raina kansu suka shiga kuka. Ta kuma yi masu addu’a a kan su. Da kuma suka shiga fadar Ibn Ziyad ma sai ta yi jawabi mai ratsa zukata. Da ya ce zai kashe Ali Bin Husaini (AS), sai Sayyidah Zainab (AS) ta ce sai dai ya kashe su tare. Sai ya ce, da fa gaske take, lalle zumunci na da karfi. Imam Ali Bin Husaini (AS) ya ce masa: “Kana yi mini barazana da kisa ne, ba ka san cewa kisa a wurinmu al’ada ce ba, kuma Shahada karama ba?” Duk A’imma gaba dayansu Shahidai ne.

Shi din banza! Ko maigidansa ma yaya ya kare da Sayyidah Zainab (AS)? Da aka kai su fadar Yazidu, ta yi wannan shahararren jawabin nata a fadar Yazidu. Zance mai isa, kaulan baliga ta yi masa. Shi kansa Yazidu sai da ya ce, kowace kalma ya ji ta kamar walkiya, kai ya ma fi walkiya, kamar tsawa ko aradu (thunder), in ji shi. Duk abin da ta gani bai karya zuciyarta ba. A gaban babban azzalumi ta wanke shi tas, sai ya yi borin-kunya a kan zai kashe Ali Bin Husaini (AS). A nan ma ta ce: “Ina gwarzantakar wanda yake fada da mace?” Sai ya yi turus.

Duk inda aka bi da su yayin da za a dawo da Madina, sai Sayyidah Zainab (AS) ta fadi abin da ya faru. Ita ta ci gaba da sakon juyin-juya-hali na Imam Husaini (AS), bayan shahadarsa.

Ali Shari’ati na cewa, ko dai ka zama Imam Husaini (AS) azzulumai su kashe ka, ko kuma ka zama Zainab wadda da ta ci gaba da sakon Imam Husaini (AS). Babu na uku, sai dai ka zama cikin su Yazidu (LA) azzalumai, su ne na uku. Tarihin Sayyidah Zainab (AS) na raya zuciya, ya karfafa gwiwa, ya kuma shirya batacce da matacce. Babu sassauci (compromise) a magana ko sassauci ga azzalumai. A duk fadin duniyar nan a yau, babu mace da ake ziyarar kabarinta kamar Sayyidah Zainab (AS). Ka ji daukaka ba Malam. A gaskiyar magana, mutanen da suka aukar da waki’ar Karbala, ko da Manzon Allah (S) suka samu dama abin da za su yi masa ke nan. Ba Yazidu ya fada ba cewa, ya biya bashin da yake bin Manzon Allah (S) ba. Allah ya ki. Babu wanda zai yi galaba a kan Manzon Allah (S), shi ya sa suka rama a kan ’ya’yansa. Allah yana cewa: “Wa hammuw bimaa lam yanaaluw” (kuma sun himmatu ga abin da ba su samu ba).” (9/47). Duk masu Tafsirin Sunna da Shi’a sun fassara wannan Aya da cewa, sun yi burin kashe Manzon Allah (S). Su waye? Ya kamata a gaya mana mutanen da suka so kashe Annabi (S), ya kamata mu san su. Tarihi ya yi shiru a kansu, ta yiwu manya ne shi ya sa aka sakaye sunayensu. Allah ya ga dama, babu wani da zai salladu a kan Manzonsa (S). Shi ya sa hamiyyar Larabawa ta jahiliyya wanda suka yi shi cikin Musulunci, ‘manifestation’ din shi ne a Karbala. Bai iya yiwuwa a kansa ba, sai ’ya’yansa (S). Amma don shi ne ‘target’ din, babu shakka Manzon Allah (S) ne suka so kashewa.

Me aka je a Badar, Uhud, Khaibar, Handak? Duk don a kashe Manzon Allah (S) a kuma kawo karshen Musulunci. Iyayen Yazidu suka yi burin haka, amma ta Allah ba tasu ba, sun kasa. Sai suka yi ramuwar gayya a kan ’ya’yansa. Da wane ido za su kalli Manzon Allah (S) a gobe kiyama, idan ya ce don me kuka kashe mini Iyalan Gidana? Wace amsa za ku ba da?

Kuma mutum na iya tambayar, me ya sa hakan ta faru? Domin Allah na nufin daukaka Imam Husaini (AS) da Iyalansa da Sahabbansa, ya kuma kaskanta su Yazidu da mataimakansa. Kowa ya samu sakamakon aikinsa. Kuma Allah ya bar su, suka fito da duk kullin da ke zuciyarsu.

Da ai Annabi Ibrahim (AS) aka bai wa wannan darajar ta yanka Isma’il (AS), amma sai Allah ya ce: “Muka fanshe shi da abin yanka babba”. Ma’ana Imam Husaini (AS). Wannan darajar Allah ya ga dama a gidan Annabi (S) ya sa. Shi ya sa ma da Allah ya sanar da Manzonsa (S) abin da za a yi wa Imam Husaini (AS), sai Manzo (S) ya yi kuka, sai Allah ya ce domin zubar da hawayen da Annabi ya yi, ya bar shugabanci a zuriyar Husaini (AS) har zuwa ranar kiyama. Manzon Allah (S) ya yi kuka, Imam Ali (AS) ya yi kuka, Sayyidah Fatimah (AS) ta yi kuka, Ummu Salma (matar Annabi ta yi kuka). Da sammai da kassai da abin da ke cikinsu duk sun koka, sama sai da ta canza kamanni har na wata shida. Saboda meye haka ba zai kasance ba, alhali Allah ya halaka al’ummar Annabi Salihu (AS) saboda sun halaka taguwarsa, sai duk aka halaka su. Taguwar Annabi Salihu (AS) ta kai darajar Imam Husaini (AS) ne? Ko darajar dokin da ya hau (Zuljanan) ba ta kai ba. Allah yana nan a madakata.

Imam Ali Bin Husaini (AS) ya ce: “Da Annabi cewa ya yi a kashe Iyalin Gidansa bayan rasuwarsa, da ba za a yi masu fiye da abin da aka yi masu a Karbala ba”. Wato, ko da cewa ya yi a kashe su, to ba za a yi fiye da abin da aka yi masu a Karbala ba. Wato ma’ana, an kure iyakar ta’addanci a Karbala. Balle kuma cewa ya yi, a so su, a kuma bi su. To, wannan ita ce soyayyar? Manzon Allah (S) ya gaya wa Imam Husaini (AS) cewa, yana da wani matsayi na musamman a wurin Allah, amma ba zai same shi ba sai da Shahada. Shahadarsa ta zama fansa ga wannan addini.

Za mu ci gaba insha Allah.




Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba?
Babu damuwa.
Kana iya duba nan