Al’amarin Imam Husain ya ma zama mahadan ‘Insaniyya’ (11) Tare da Sayyid Zakzaky
GYARA A MAKON JIYA
Mai karatu ka yi mana afuwa don kuwa a makon jiya akwai tsallake a wannan shadara din saboda rashin fitar abin da Sayyid Zakzaky ya fada a faifen da muke amfani da shi. Yanzu ga gyaran: “Su sun dauka Karl Max ne da Lenin da Angel, ashe Amiril muminin shi kadai ya ba adala ‘definition’.
Haka kuma a nan ma akwai tsallake, amma ga gyaran: “Ana ganin irin wannan kyakkyawan misali, amma in aka kwatanta da Amiril muminin, Ghandi miliyan ma ina ya kai Amiril muminin, wanda a duniyar nan dimraini da kursaini (mayafi biyu da busassun gurasa biyu) suka wadatar da shi.”
ARBA’IN NA DA WANI ASIRI
To, Arba’in na da ma’ana daban-daban. Wala’alla wasu ma’anonin arba’in wadansu asirai ne dangane da arba’in wanda Allah ya bar wa kansa sani. Za mu ga an kawo batun arba’in a Alkur’ani daban-daban. Za kuma mu ga hadisi ya zo da arba’in daban-daban. Wala’alla akwai wani asiri a wannan adadi arba’in.
Alal misali, shi wannan Manzon (S) ba a yi masa wahayi ba sai da ya cika shekara 40. Kuma a cikin Alkur’ani Allha (T) ya bayyana mana cewa Annabi Musa (AS) shi ma ya je mikatin Allah kwana 40. Farko an yi masa alkawari 30 ne “wawa’adna Musa Thalasina lailatan wa atmamnaha bi asharin fa tamma mikati Rabbihi arba’ina laila.” Kwana 40 sannan aka ba shi Attaura.
Sannan ma a cikin Linjila, wanda yanzu yake hannun Kirista, Bible, an nuna cewa Isah (AS) shi ma ya yi Azumin kwana 40 kafin ya shigo birnin Kudus, wanda ya shigo a kan jaki, wanda wasu kiristoci ma su kan rinka yin wannan azumi din na kwana 40. Ga shi ma aka ce “wa balaga arba’ina sanatan kala Rabbi auzi’iniy an ashkura ni’imatikallatiy an’amta alayya.’ Kuma aka ce har yayin da ya kai karfinsa, ya kai shekara 40. Ga shi nan arba’in, arba’in a cikin Alkur’ani. Hadisi kuma ya zo da arba’in bila adadin.
Alal misali akwai hadisin da ya nuna halittar tayi a cikin uwa, ya kasance ‘nudfa’ kwana 40, sannan ya zama ‘alaka’ kwana 40, sannan ya zama ‘mudga’ kwana 40, sannan a umurci Mala’ika ya hura masa rai bayan arba’in uku. Maganar 40 dai ya fi a kirga. Akwai ma riwayar cewa idan da mutum zai kiyaye kansa, mutum ya gwada wannan, ya kiyaye kansa, kar ya aikata zunubi, hatta ko dan karami ne, la’alla na magana da baki ne ko na kallo ne, kar ya ci haram, kar ya aikata haram, kar ya yi zunubi kwana 40, to Allah zai kinsa hikima a bakinsa, zai koma ‘aja’ib’ in ya kiyaye wannan.
To arba’in, arba’in na da wani asiri. To arba’in din bayan rasuwa fa? To ita ma akwai wani asiri dangane da ita. Wala’alla, me ake yi ma mamaci bayan ya kwana 40? Don an ruwaito ma, an ce tsohon tarihin Misirawa suna wani biki na bizne gawa, akwai wani hallu’i da suke yi in ya cika 40. Su harhada wadannan abubuwan su sa a cikin wani akwati mai kama da mutun-mutumi, su sa. To shi ma suna jira sai ya kwana 40. Sukan kiyaye a lokacin za a shiga ma mamaci hisabi dangane da abin da ya aikata. Duk da lokacin su imaninsu da iyayengijinsu, wadansu irin kamar kwankwamai ne. Kowane Ubangiji ya tambaye shi dangane da bin da ya aikata. To su ma suna da wannan al’adar, wala’alla asalin abin kila wani addini ne na wani Annabi daga baya ya sukurkuce ya koma ya zama al’ada.
Kuma mukan kafa hujja da arba’in din Imam Husaini da riwaya shaharriya ta Imam Hasan Al-askari (SA), wanda yake cewa alamar mumini biyar ne, salla raka’a 51 a kwana da yini, da kuma ziyarar arba’in, da sa zobe a dama, da kofa goshi a kasa, da bayyana “Bimillahir rahmanir raheem.” Ka ga sai ya sa ziyaratul arba’in daga cikin alamomin mumini. Kuma wala’alla abin nufi da ziyaratul arba’in, arba’in din Imam Husaini. Don wannan ya yi ihtisasi da muminai. Don haka ne ma nake cewa idan har ka hangi irin wannan hushud da irin wannan tafiya, ka duba ka ce magoya bayan Husaini ne, to kai kuma ka yi imani da la’ilaha illallah Muhammadur Rasulullha, kuma ka san Husainin nan Sayyidu Shababu Ahlil Janna ne, to ya kamata ka bincika kai menene? Imanin naka in an auna asikeli ko zai yi nauyin mene? Ka ga wannan babu mamaki da ka ga ziyaratul arba’in na cikin alamatul mumini.
To, sai mu ce ziyaratu arba’in wala’alla yana nufin zuwa kabarin Abu Abdillah a ranar arba’in, wanda kum akwai riwayar ziyarar arba’in na kusa da na nesa. Mu nan da ba mu sami zuwa ba, sai mu ce ma wadanda suke can “ya laitana kunna ma’akum fana fuza fauzan azima.” Kuma mu roki Allah mu ce “Allahummar Zukna fiddunya ziyaratul Husaini wa fil akhirati shafa’atah, wahashurna fi zumratihi.” Da fatan Allah (T) ya azurta mu da ziyarar Imam Husaini a nan duniya, a Ashura ko Arba’in, ko duka biyu, ya maimmaita mana. Yanzu haka ma wannan ziyarar akwai ba’adin ’yan uwa wadanda suke karatu a Iran, wadanda sun shiga cikin gungun al’ummar da suka tafi zuwa Karbala din.
HAR YANZU YAZIDU NA NAN DA RAI, HUSAINI MA NA NAN DA RAI
To, kuma abin da ke aukuwa a wannan lokaci mai ban al’ajabi dangane da ziyarar Ashura da ziyarar Arba’in musamman ma, yana nuna mana cewa har yanzu Yazidu yana nan da rai, kamar yadda kuma har yanzu Husaini ma yana nan da rai. Domin har yanzu Yazidawa ba su daina kisan kai ba.
Zan sha mamakin a ce mutum yana da imani, shi sunansa musulmi ne, amma ya je ya dasa bom, ko ya harba gurneti ko wani abu mai kama da haka nan a dandanzon mutane da suke tafiya Ashura, duk da kuma ya san wannan taron nan mutane ne daban-daban. Ko da yaki ne ba tsakanin soja da soja ake yi ba? To, wadannan mutane ne daban-daban maza da mata, tsofaffi da yara har da jarirai nan gungura su a ‘pusher’, da ma marasa lafiya wadanda suke fatan Allah ya sa wannan ya zama sanadiyyar su sami lafiya, amma ya wurga bom. Ko dazun na gani a talabijin wani dan sanda ya dauko wani jariri cikin wadanda aka harba suka mutu a Basra a dandazon masu tafiya da kafa. Amma mutanen nan suna tafiya ba su san mai zai tashi ba, ko a mutu ko a yi rai. Suna tafiyan a ce can wani ya tashi, can mutum goma, can mutum tara, can mutum ashirin, haka nan.
Wannan anya zai zama aikin wani mumini ko ma meye i’itikadinsa? Wanda yake karanta Alkur’ani, wanda ya karanta cewa, “man katala mu’uminan muta’ammidan fajaza’uhu jahannama khalidan fiha wa gadiballahu alaihi wa la’anahu wa a’adda lahu azaban aziyma.” Anya? Wannan sai dai aikin Yahudu da sauran ‘mulhidin’. Wanda zai ga dandazon mutane irin wannan, har da marasa lafiya da tsofaffi da jarirai ya wurga masu bom, wanda zai mutu ya mutu, wanda zai yi rai ya yi rai, wanda zai kassara ya kassara; amma mutanen nan ba su fasa ba.
To, har walayau kamar yadda yake akwai Yazidawa, to akwai kuma Husainawa, wadanda su kuma ashirye suke, kamar yadda sahabban Imam Husaini suka ba da ransu, da iyalan gidansu da shi kansa, su ma shirye suke su yi wannan. Wanda ya mayar da wannan waki’a ta Karbala ba ta zama tarihi ba, tana nan da ranta.
JABIR BN ABDULLAH MASOYIN AHLUL BAITI NE
Har wala yau dangane da Arba’in, akwai cewa shi arba’in din Imam Husaini (SA) ya dace da daidai lokacin da Jabir Bn Abdullah Al-ansariy (RA) ya ziyarci Imam Husaini. Na san Jabir Bn Abdullah shahararre ne cikin Sahabban Manzon Allah (S). Na’am Mabiyin Manzon Allah ne, Masoyin Amirul Muminina ne, Masoyin Fatima ne, Masoyin Hasan da Husaini ne, Masoyin Ahlil Baiti ne. Amma kuma sauran makarantu, har ma Sarakai, makarantun Sarakai, suna da ruwayoyi dangane da shi kuma suna girmama shi. Saboda haka masu cewa abin da Annabi bai yi ba, Sahabbai ba su yi ba, to ba za a yi ba, ya zama bidi’a, ‘lau kana khairan lasabakuna ilaih’. To ‘fakad sabkuuna ilaih! Fa huwa kahair!’ Don Jabir Bn Abdullah Ansariy shi ne farkon wanda ya ziyarci Imam Husaini daga Madina ya tafi. Kafin ya isa, a daidai kabarin ya cire takalmi ya tafi da kafarsa. Ya je ya dumbuji kasar kabarin ya muttsuka a fuskarsa ya yi kuka, ya yi kira, ya yi kira, yake cewa kiran masoyi, amma kuma ina za ka iya amsa mani alhali an gutsuttsure jiki.” Sannan shi ma ya je ya dibi ruwan Furat kashar-kashar, ya kai baki ya kasa sha, yana tunanin kishin Imam Husaini.
Lokacin yana kabarin Imam Husaini sai aka hango duhun gungun mutane na zuwa. Ya ce ma yaronsa ‘maza duba ka ga wanene, su wanene wadancan?’ Idan dakarun Yazidu ne mu kauce, in kuma Maulaya ne. Haka ya ce, Maulaya, Sayyidi Imami Zainul Abidin, ka isar mani da gaisuwa gare shi kafin in iso. Ya zo ya ce ai ‘fahuwa Maulaka, wa Sayyuduka, Imam Zainul Abidina ne’. Sai ga Imam Zainul Abidin ya zo daga Damashk tare da Gwaggwonsa Sayyid Zainabul Kubra da sauran abin da ya yi saura na Iyalan Imam Husaini, ran nan suka iso, ranar arba’in. Suka zo suka sami Jabir Bn Abdullah a wurin. Imam Zainul Abidin yana cewa a nan ne aka yanka mazajenmu, a nan ne aka ci zarafin yaranmu da matanmu, a nan ne aka kashe jaririnmu. Suka yi kuka, suka wanzu a wurin har kwana uku suna koke-koke.
A lokacin ne aka mai da kawuka na wadanda duk aka cire ma kai. Don kamar da riwaya wadda ta zo, da ma akwai riwayoyi daban-daban, amma ruwaya wadda ta fi karfi, ta fi inganci, ita ce Imam Zainul Abidin ya dawo da kan Babansa da kawukan iyalan gidansa da na Sahabbansa gaba daya, kuma kowanne sun tona sun hada kan da gangan jikin. Na’am a baya na kan kawo maganar cewa a yadda aka gaya mana, ranar arba’in ne aka hada kan Imam Husaini da gangan jikinsa. Kuma zai zama ‘su’ul adab’ ma ga wanda yake da Imani ya ce ya aka yi haka? To imma shi bai san wani abu ba ma’anawi ba, to akalla zai iya gane wanda yake ‘madi.’Kan ne Yazidu Alla’in ya mika ma Imam Zainul Abidin. Yayin da ya ce masa ‘ka roke ni ko me kake so.’ Ya ce ina da bukatu guda uku ko hudu. Ya ce na daya, a yi jajen zaman makoki a fadarka. Sai ya ce masa a fada na a yi zaman makoki, wannan ba zai yiwu ba. Sai su kuma Fadawa suka ce, to ai ka yi masa alkawari, Sarki yana alkawari ya saba ne? Kai ka ce masa duk abin da ya roka, to kuma ya roki wannan. Sai ya ce, to shikenan a yi jajen. Sai aka tsai da jajen farko a fadar Yazidu. Ya ce bukata ta biyu, a cikin kayan da aka karba namu, akwai abu daya da nake bukata, shi ne hijabin Sayyida Fatimatuz Zahra. Aka ce Yazidu ya ce, ba ma hijabin ba, duk kayansu a maida masu. Na uku, ya ce yana so a ba shi kan Babansa. Sai ya ce ba kan Babansa ba ma, duk kawukan a ba su. Wannan kuma Allah ne ya dora Imam Zainul Abidin a kansa, don a lokacin ma ya so ya kashe Imam zainul Abidin ne, yana neman sa da laifi don ya kashe shi, to amma Allah mai iko da zuciya, sai ya birkita zuciyarsa, ya zama yana masa komai da yake so. Don ya ce masa, idan za ka kashe ni ne, sai ya ce a’a ba kashe ka zan yi ba. In ka kashe ni ne, to wa zai mayar da haramin Manzon Allah zuwa Madina? Sai ya ce ba kasheka zan yi ba, kai ne za ka maishe su.
Sai ya tambayi Imam Zainul Abidin, ka san abin da ya sa na yi naka wannan? Ya ce na sani mana. Sai ya ce meye dalili? Ya ce a zuciyarka kana tunanin kar ya zama akwai wani wanda yake da wani ‘minna’, wani abin da zai iya cewa ni ne na yi ma wane wani abu kenan, in ba kai ba. Ya ce ashe ka gane zuciyata, kamar ka shiga zuciyata. Tunanin Yazidu a lokacin, shi ne bari ya yi masa wannan, a ce wa ya yi ma Imam Zainul Abidin wannan? A ce Yazidu ne. To, sai ya ga Imam Zainul Abidin ya ga abin da ke cikin zuciyarsa. Wato shi yana ganin Yazidu kamar ya yi abin kirki ne, ga shi ma bai kashe Imam Zainul Abidin ba. Ya ce ka san abin da ya sa ban kashe ka na? Na sani mana! Menene? A zuciyarka kana tunanin zai zama za ka yi tunkaho kai ne ka iya ka faranta raina. Ya ce ashe ka san zuciyata.
To, sannan kuma ya umurci Nu’uman Bn Bashir ya raka su. To shi ne suka bukaci a bi da su ta Karbala, duk da yake Karbala ba hanyar Madina ba ne. To dai ya zama sun zo daidai arba’in, daidai ranar arba’in. Sai ya dace da zuwa Jabir yana nan, sai kuma hango suna zuwa. Suka zauna nan suka kwana uku kafin su wuce zuwa Madina.
Za mu ci gaba insha Allah.
