Al’amarin Imam Husain ya ma zama mahadan ‘Insaniyya’ (111) Tare da Sayyid Zakzaky
Mai karatu yau muna mako na uku ke nan da soma kawo maku wannan jawabi, wanda Sayyid Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron Yaumu arba’in na shahadar Imam Husaini (SA) na wannan shekara ta 1433, wanda kuma aka gudanar a Husainiyya Bakiyyatullah Zariya. Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana, tare da fatan ana wa’aztuwa. Muna kuma rokon Allah (T) ya kara wa Sayyid Zakzaky lafiya da kariya ta musamman daga dukkan sharri. A sha karatu lafiya.
To, kamar yadda na ce, bisa al’ada akan karanta abin da ya faru ne. Wadanda suka zo da Maktal Imam Husani sukan raba biyu ne, daya a karanta ranar Ashura, a karanta wak’ar da ta faru. Dayan kuma a karanta ranar arba’in. To, ranar Ashura mu a nan ran nan lokaci ya kure mana don mun dauko bayani da dan tsawo, saboda haka a ranar Ashura mun fadi kadan ne, sai muka kawo wata riwaya sassauka wadda ta dan dunkula abubuwan da suka faru a dunkule, ba a fade shi da tafsili mai tsawo ba na mubarazar kowanne, sai aka fadi mubarazar ba’adin Sahabban Abi Abdillah (AS) da ba’adin iyalan gidansa, sannan kuma ta kammala da shi nasa mubaraza din. To, sai muka karanta wannan a ranar.
Amma bayan nan mun dauko bayani na abin da ya faru bayan waki’ar Ashura tirya-tiryan har muka dauki kamar kwana uku muna yi, har muka yi bayanin ga abin da ya faru a Kufa, jawaban da aka yi, da jawabin Sayyida Fatima Bint Ali ’yar shekara 11wadda ta yi a Kufa. Da kuma wanda Sayyida Zainab ta yi wa mutanen Kufa, da kuma wanda Imam Zainul Abidina ya yi ma mutanen Kufa, da kuma shigar da su gaba ga Fadar Yazid, da irin abin da ya gudana, wanda har ya yi niyyar ma kashe Imam Zainul Abidina, inda Gwaggwonsa ta ce sai ya kashe ta kafin ya kashe shi.
To, sannan kuma da abin da gudana na hawa mumbarin musulmi ya yi miyagun maganganu, wanda bawan Allah, Abdullahi Bn Akil ya mai da masa, har ma ya nemi a kama Abdullahi Bn Akil, wanda suka je kama shi, jama’a suka tare. Kuma ya tura dogarai da daddare aka yi artabu har aka shiga gidan Abdullahi Bn Akil aka kamo shi makaho, da kuma ya cika da burinsa. Abdullahi Bn Akil yana ce ma Ibn Murjana cewa, “tun kafin uwarka ta haife ka nake rokon shahada; aka yi Jamal na rasa ido daya ban sami shahada ba, aka yi Siffin na rasa daya idon, ban sami shahada ba, sai yanzu alhamdu lillah Allah ya azurta ni da wannan. Kuma da ma na kasance ina rokon Allah ya azurta ni da shahada din nan a hannun mafi sharrin bayi.” Sai shi kuma mafi sharrin bayin ya ji haushi, sai kuwa ya sa shi ya cimma burinsa. Sai kuma aka kai iyalan Annabi zuwa Dimashak. Duk wadannan mun yi, ba sai mun maimata wannan ba.
A daidai wannan lokaci akwai abin da na taba karanto mana, rubutu ne na jaje, wanda Imam Ja’afarus Sadik (AS) ya rubuta a matsayin ta’aziyya ga wani Ammi nasa da ’ya’yansa da aka kama, ’ya’yan Imam Hasan Al-mujtaba, wanda Sarkin Zamanin ya kama su, aka je aka kulle su. To, sai ya rubuta masu takarda yana masu ta’aziyya. Wata rana a Fudiyya, shekarun baya na taba karanto mana wannan a ranar arba’in a matsayin ta’aziyya. Kuma ina ganin yanzu babu laifi idan muka tunatar da kanmu dangane da wannan a matsayin jaje da ta’aziyya.
DAURIYA MUHIMMIN AL’AMARI NE
Wannan rubutu ne, ba magana ce aka ruwaito ba, tamkar wasika ce ya rubuta. An kawo da ruwaya mai tsawo, wanda babu bukatar mu karanta isnadi. Ya ce, Jafar Ibn Muhammad (AS) ya rubuta wa Abdullah Bn Hasan (RA) yayin da aka kama shi, shi da iyalan gidansa, yana masa ta’aziyya bisa abin da suka shiga ciki gaba dayansu. Ga abin da ya ce, “Bismillahir rahmanir rahim. Ya zuwa khalafissalih, warjin nagari da zuriyyarsa dayyiba na ’ya’yan dan uwansa da ’ya’yan Amminsa. Ya ce bayan haka nan, in kai ka kadaita, da kai da iyalan gidanka na kama kun da aka yi, da abin da ya same ku na musiba, to ba ka kadaita da bakin ciki da takaici da radadin zuciya fiye da ni ba. Wato kai aka kama da gangan jiki da iyalan gidanka, amma a bakin ciki, da ni da kai duk daya ne, ni ma ina ji a zuciyata.”
“Tabbas abin da ya same ka na radadi da damuwa da zafin musiba, ni ma shigen irin wannan ya same ni. Amma na koma ya zuwa abin da Allah, Jalla jalaluhu ya umurci masu takawa da yin dauriya da kyakkyawar ta’aziyya.” Ta’aziyya shi ne kamar lallashi. Ga shi kana cikin musiba, amma a gaya maka wata magana don a sanyaya maka rai, shi ne ta’aziyya. Za ka ga mutum idan aka yi rasuwa ya je ta’aziyya, za ka ga ya kan yi lallashi ne, yakan fadi wasu kalmomi masu dan dadada rai. Mutum ga shi da musiba din, amma kuma dai sai ya ji dadi, ba wai a yi ba’a, ko raha su yi dariya ba, a’a, ma’ana ya gaya masu wata magana wadda wannan musibar tasu, duk da tana nan a musiba, amma kuma yanzu sai su sami saukin musiba din da jin cewa ashe ma za su sami lada wajen Allah.
To, sai ya ce, “sai na koma ya zuwa ga abin da Allah Jalla jalalahu ya umurci masu takawa na dauriya da kyakkyawar ta’aziyya. Yayin da Allah (T) yake ce ma Annabinsa (S) ‘ka daure da hukuncin Ubangijinka, kana nan a idanuwanmu.’ Wato Allah (T) yana gaya ma Manzonsa wannan abin da ke samun ka daga mushirikan Larabawan Makka, da izgili da cutar da Annabi da fatar bakinsu da hannunwansu, to duk abin da ke faruwa din nan, Allah (T) yake ce ma Manzonsa ka daure bisa hukuncin Ubangijinka, wato wannan abin da ka fada ciki, kana nan a idonmu, ma’ana muna ganin ka da duk abin da ke faruwa da kai, kai dai naka dauriya.
Yayin da yake ce masa “ka daure da hukuncin Ubangijinka, kar ka zama kamar ma’abucin kifi,” shi ne Yunus Bn Mata (AS). A nan ana ce ma Manzon ya daure bisa abin da ke samun sa kada ya yi gaggawa irin na Yunus Bn Mata. Yunus Bn Mata Annabi ne, Annabin Allah ne, Annabi Yunus. To, amma da ya ga musiba za ta sauka ma mutane, ya yi masu da’awa, ya yi masu da’awa suka ki, ya ga musiba za ta sauka, sai ya fita ya bar su, bai zauna tare da su ba. A matsayinsa na Annabi, wannan laifi ne iri na Annabawa. Amma da wani Waliyyi ne ya yi irin wannan laifin, to da ya yi daidai. To, kuma in Waliyyi ya yi laifi, to mu kuma shi ne da’armu, mu Ayyuhannasu. Akwai fadin cewa, laifin Annabawa da’ar Waliyyai, laifin Waliyyai da’ar mu kuma Ayyuhannas. Wannan laifi ne irin na Annabi, ba irin na kowa da kowa ba.
Yanzu misali ka ga alamar, ba ma musiba irin girgizar kasa ba, ba Tsunami ba, ko ruwan sama ka ga zai zo ya lakada maka duka, me za ka yi? (Gudu!) Yawwa, za a ce ka yi daidai. To, in da abu zai daki wasu, shi ga Annabi ya kamata ya tsaya shi ma ya dake shi, ko kuma ya kwace su, amma ba ya gudu ba. Amma wannan Annabi fa kenan, ba ayyuhannasu irin su mu ba. In irin su mu ne, sai a ce an yi daidai.
Nan ka ga ana cewa kar ka zama irin Yunus (AS), shi ya yi gaggawa na inda ya fita kafin musiba ta sauka. Da abin da ya kamata ya yi shi ne, a matsayinsa na Annabi ya tsaya, sai bai yi haka ba. Duk da ma ana cewa in ka yi gaggawa ba laifi ka yi ba, to amma za ka rasa wani matsayi wanda da ka kai gare shi in da ba ka fita din ba.
Har inda Allah (T) yake ce ma Annabinsa, yayin da aka yi masalu ga Hamza, Amminsa. Aka tsaga leben Hamza, ka tsaga harshensa, aka tsaga kirjinsa, aka fito da hantarsa aka gatsa, aka bar shi, aka cire kunne da harshe aka yi tsakiya da shi, wata ta cire ta yi tsakiya. Amma lokacin sai Allah (T) ya ce ma Annabi, in za ku yi ukuba, wato ku yi ramuwa, to ku yi da shigen abin da aka yi maku. Amma in kuka daure, to shi ya fi. Wato kana iya ramawa, amma shigen abin da aka yi maka shi za ka yi, kar ka wuce. To, amma ka ga me Annabi (S) ya zaba? ‘fa sabara’, sai ya yi hakuri. Sai Manzon Allah (S) bai rama ba.
Da kuma inda Allah (T) yake ce ma Annabinsa, “ka umurci iyalanka a salla, kai ma ka daure a kan salla din. Mu ba mu tambaye ka batun arziki ba, mu ne masu azurta ka.” Da yawa masu fasara suna batun cewa, ba mu tambaye ka arziki ba, suna cewa ba mu ce ka ba mu wani abu ba, eh, ya za a ce a ba Allah wani abu? Ma’ana ba mu tambaye ka dangane da al’amarin arziki ba, mu ne masu daukan takalifinka. Wato ma’ana ka daure. Ka umurci iyalanka da salla, kai ma da daure.
Da inda Allah (T) yake cewa “wadannan wadanda idan musiba ta same su su kan ce inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah (T) ya ce wadannan akwai falala gare su daga wajen Ubangijinsu da rahama, kuma wadannan su ne shiryayyu. Wato idan wata musiba ta same su sai su yi istirja’i. Istirja’i shi ne komawa ga Allah, inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Da inda Allah (T) yake cewa yana cika wa masu dauriya ladansu ba tare da bincike ba, in dai mai dauriya ne ya zo, ba a binciken a ce yaya? In dai Sabiruna suka zo sai dai akwai a ce a wuce. Ba a binciken komai game da su. A ce abu kazan su fa? Abu kazan su fa? Sai dai kawai a ce su wuce.
Da kuma yayin da Allah (T) ya fadi, yana magana game da abin da Lukman ya ce ma dansa, ‘ka daure bisa duk abin da ya same ka, wannan yana daga cikin al’amura masu azama, wato muhimmai. Mihimmin al’amari ne dauriya.
A biyomu mako na gaba don ci gaba in sha Allahu
